Laraba, 15 ga Oktoba
Ni ne Alpha da Omega.—R. Yar. 1:8, Tsohuwar Hausa a Sauƙaƙe.
Alpha shi ne harafi na farko a rubutun Helenanci kuma omega shi ne na ƙarshe. Jehobah ya ce Shi ne “Alpha da Omega” don ya nuna cewa idan har ya soma yin abu, tabbas zai yi nasara wajen ƙarasa shi. Da Jehobah ya halicci Adamu da Hauwaꞌu, Ya gaya musu cewa: “Ku yi ta haifuwa sosai ku yalwata, ku ciccika duniya ku kuma sha ƙarfinta.” (Far. 1:28) A wannan lokacin ne Jehobah ya bayyana nufinsa, “Alpha” ke nan, wato ‘farkon.’ Idan Jehobah ya cika nufin nan kuma ꞌyan Adam masu aminci sun cika duniya sun kuma mai da ita aljanna, wannan lokacin ne zai zama “Omega,” wato ‘ƙarshen.’ Da Jehobah ya gama halittar “sama da duniya, da dukan tulin abubuwan da suke cikinsu,” ya faɗi wani abin da ya nuna cewa tabbas nufinsa zai cika. Ya keɓe rana ta bakwai musamman don ya cika nufinsa ga ꞌyan Adam da kuma duniya. Ta haka, Jehobah yana ba da tabbaci ne cewa zai cika dukan nufinsa a ƙarshen rana ta bakwai.—Far. 2:1-3. w23.11 5 sakin layi na 13-14
Alhamis, 16 ga Oktoba
Ku shirya wa Yahweh hanya a daji, ku gyara hanya a hamada domin Allahnmu!—Isha. 40:3.
Wannan tafiyar za ta iya ɗauki Israꞌilawan watanni huɗu. Amma Jehobah ya yi alkawari cewa zai kawar da duk wani abin da zai iya hana su komawa. A ganin Yahudawa masu aminci, komawa ƙasar Israꞌila zai kawo musu albarka sosai fiye da sadaukarwa da za su yi. Albarka mafi muhimmanci da za su samu ita ce bautar da za su yi wa Jehobah. A Babila, babu haikali inda Yahudawan za su riƙa miƙa hadayu ga Jehobah kamar yadda Dokar Musa ta ce, kuma babu firistoci. Ƙari ga haka, mutanen da suke bauta ma allolin ƙarya sun fi waɗanda suke bauta wa Jehobah yawa sosai. Don haka, dubban Yahudawa da suke ƙaunar Jehobah suna marmarin lokacin da za su koma ƙasarsu domin su maido da bauta ta gaskiya. w23.05 14-15 sakin layi na 3-4
Jumma’a, 17 ga Oktoba
Ku yi zaman mutanen haske.—Afis. 5:8.
Ruhu mai tsarki ne zai taimaka mana mu ci-gaba da ‘zama mutanen haske.’ Me ya sa? Domin yin rayuwa mai tsarki a wannan duniyar da ke cike da halin lalata, bai da sauƙi ko kaɗan. (1 Tas. 4:3-5, 7, 8) Ruhu mai tsarki zai iya taimaka mana mu kauce ma irin tunanin mutanen da ke duniyar nan, waɗanda raꞌayinsu dabam yake da na Allah. Ruhu mai tsarki zai kuma taimaka mana mu dinga yin “ayyuka masu kyau, da zaman adalci.” (Afis. 5:9) Wani abin da za mu iya yi don mu sami ruhu mai tsarki shi ne, mu roƙi Allah cewa ya ba mu ruhunsa. Yesu ya ce Jehobah ‘zai ba da ruhu mai tsarki ga masu roƙonsa.’ (Luk. 11:13) Ƙari ga haka, idan muna yabon Jehobah tare da ꞌyanꞌuwanmu a taro, Jehobah zai ba mu ruhunsa. (Afis. 5:19, 20) Idan muna da ruhu mai tsarki, zai taimaka mana mu riƙa yin abin da Allah yake so. w24.03 23-24 sakin layi na 13-15