Oktoba
Laraba, 1 ga Oktoba
Hikimar da ta fito daga wurin Allah . . . mai son yin biyayya ce.—Yak. 3:17, New World Translation.
Shin yana maka wuya ka yi biyayya a wasu lokuta? Ya yi wa Dauda wuya, shi ya sa ya yi adduꞌa ga Allah cewa: “Ka ba ni ruhun biyayya da zai riƙe ni.” (Zab. 51:12) Dauda yana ƙaunar Jehobah sosai. Amma a wasu lokuta, ya yi masa wuya ya yi biyayya. Haka ma yake da mu. Me ya sa? Na ɗaya, mu ajizai ne kuma hakan yana sa mu yi rashin biyayya. Na biyu, a kowane lokaci Shaiɗan yana ƙoƙarin sa mu yi wa Jehobah rashin biyayya kamar yadda ya yi da Hauwaꞌu. (2 Kor. 11:3) Na uku, muna rayuwa ne tare da mutanen da suke son yin rashin biyayya. Shi ya sa Littafi Mai Tsarki ya ce suna da “ruhun nan da yake zuga zuciyar mutanen da suka ƙi biyayya ga Allah.” (Afis. 2:2) Don haka, dole ne mu yi iya ƙoƙarinmu mu guji jarabar yin zunubi, da kuma matsin da Shaiɗan da mutane a duniyar nan suke mana don su sa mu yi rashin biyayya. Dole ne mu yi iya ƙoƙarinmu mu riƙa yi wa Jehobah biyayya da waɗanda ya naɗa su yi ja-goranci. w23.10 6 sakin layi na 1
Alhamis, 2 ga Oktoba
Ka ɓoye kyakkyawan ruwan inabin sai yanzu!—Yoh. 2:10.
Mene ne za mu iya koya daga yadda Yesu ya mai da ruwa ya zama ruwan inabi? Ya koya mana darasi game da sauƙin kai. Yesu bai yi takama game da wannan muꞌujizar ba. Ban da haka ma, bai taɓa yin takama game da abubuwan da ya cim ma ba. A maimakon haka, ya kasance da sauƙin kai kuma ya miƙa yabo da ɗaukaka ga Ubansa a kowane lokaci. (Yoh. 5:19, 30; 8:28) Idan muka yi koyi da Yesu kuma muka kasance da sauƙin kai, ba za mu riƙa yin takama game da abubuwan da muka cim ma ba. Kada mu yi takama da kanmu. Amma mu yi takama da Allahnmu mai alheri, wanda muke bauta wa. (Irm. 9:23, 24) Mu miƙa masa dukan yabo da ɗaukaka. Balle ma, babu wani abu mai kyau da za mu iya yi in ba da taimakonsa ba. (1 Kor. 1:26-31) Idan muna da sauƙin kai, ba za mu riƙa son karɓan yabo don abubuwa masu kyau da muka yi wa mutane ba. Za mu gamsu da sanin cewa Jehobah yana gani kuma yana daraja abubuwan da muke yi. (Ka kuma duba Matiyu 6:2-4; Ibran. 13:16) Hakika, za mu faranta wa Jehobah rai idan muka yi koyi da sauƙin kan da Yesu yake da shi.—1 Bit. 5:6. w23.04 4 sakin layi na 9; 5 sakin layi na 11-12
Jumma’a, 3 ga Oktoba
Kada ku kula da kanku kaɗai, amma ku kula da waɗansu kuma.—Filib. 2:4.
Allah ya hure manzo Bulus ya ƙarfafa Kiristoci su dinga tunanin abin da zai amfane waɗansu mutane. Ta yaya za mu yi hakan idan muna a taro? Mu tuna cewa ba mu ne kaɗai muke so mu yi kalami ba. Ga wani misali. Idan kana hira da abokanka, za ka ta yin magana ne, ba za ka ba su dama su ma su yi magana ba? Ba za ka yi hakan ba, domin kana so su ma su sa baƙi a tattaunawar. Haka ma idan ana taro, zai dace mu bar mutane su ma su yi kalami. Ka tuna cewa ɗaya daga cikin hanyoyi mafi kyau da za mu iya ƙarfafa ꞌyanꞌuwanmu ita ce, ta wurin ba su dama su furta bangaskiyarsu. (1 Kor. 10:24) Don haka, mu dinga yin gajerun kalamai, hakan zai ba wa ꞌyanꞌuwanmu damar yin kalamai. Ko da gajeren kalami za ka yi, kar ka yi magana a kan batutuwa da yawa. Domin idan ka faɗi kome-da-kome da ke sakin layin, sauran ꞌyanꞌuwa ba za su samu abin da za su faɗa ba. w23.04 22-23 sakin layi na 11-13
Asabar, 4 ga Oktoba
Duk ina yin haka ne saboda labari mai daɗi, domin in sami rabona a cikin albarkarsa.—1 Kor. 9:23.
Idan yanayinmu ya canja, zai dace mu tuna da muhimmancin taimaka ma mutane, musamman ma ta wurin yin waꞌazi. Muna yin waꞌazi ga mutane da suke da imani dabam-dabam, kuma inda suka fito ya bambanta. Manzo Bulus ya kasance da raꞌayin da ya dace don ya iya yin waꞌazi ga kowa, kuma za mu iya yin koyi da shi. Yesu ya naɗa Bulus manzo ga “waɗanda ba Yahudawa ba.” (Rom. 11:13) Don haka, Bulus ya yi waꞌazi ga Yahudawa da Helenawa da masu ilimi da ƙauyawa da hukumomin gwamnati da kuma sarakuna. Don ya iya yin waꞌazi ga mutanen nan, Bulus ya “zama kowane irin abu ga ko waɗanne irin mutane.” (1 Kor. 9:19-22) Da yake yin waꞌazi ga mutane, ya yi tunani a kan inda suka fito da kuma imaninsu, hakan ya taimaka masa ya san yadda zai tattauna da kowannensu don ya taimaka musu su yi kusa da Allah. Mu ma za mu iya kyautata yadda muke yin waꞌazi idan muna tattaunawa da kowanne mutum bisa ga bukatunsa. w23.07 23 sakin layi na 11-12
Lahadi, 5 ga Oktoba
Kada mai hidimar Ubangiji ya zama mai yawan gardama, amma dai ya zama mai kirki ga kowa.—2 Tim. 2:24.
Mai sauƙin kai jarumi ne, ba rago ba. Don idan mutum ya shiga yanayi mai wuya, yana bukatar ƙarfin zuciya kafin ya iya kame kansa. Sauƙin kai ko kuma tawaliꞌu hali ne da “ruhun Allah yake haifar.” (Gal. 5:22, 23) A Helenanci, ana amfani da kalmar nan sauƙin kai don a kwatanta yadda akan sa doki mai ƙarfi sosai ya natsu. Ka yi tunanin wannan, duk da cewa an sa dokin ya natsu, hakan ba ya nufin cewa ya rasa ƙarfinsa. Mu ma ta yaya za mu koyi zama masu ƙarfi da kuma sauƙin kai? Ba za mu iya yin hakan da kanmu ba, muna bukatar mu roƙi Allah ya ba mu ruhunsa don ya taimaka mana mu zama da wannan halin. Mutane da yawa sun iya yin hakan. Misali, akwai ꞌyanꞌuwanmu da yawa da mutane suka so su yi gardama da su ko su ɓata musu rai, amma sun nuna sauƙin kai kuma sun amsa da alheri. Abin da ꞌyanꞌuwan suka yi ya burge wasu mutane.—2 Tim. 2:24, 25. w23.09 15 sakin layi na 3
Litinin, 6 ga Oktoba
Na roƙa daga wurin Yahweh, ya kuwa ba ni abin da na roƙa daga gare shi.—1 Sam. 1:27.
Jehobah ya nuna wa manzo Yohanna wani wahayi mai ban mamaki. A wahayin, Yohanna ya ga dattawa 24 a sama suna masa sujada. Sun yabi Allah suna cewa ya cancanci ya karɓi “ɗaukaka, da girma, da iko.” (R. Yar. 4:10, 11) Malaꞌiku masu aminci su ma suna da dalilai da dama na yabon Jehobah da kuma ɗaukaka shi. Don suna tare da shi a sama kuma sun san shi sosai. Suna ganin halayensa ta abubuwa da yake yi, kuma hakan yana motsa su su yabe shi. (Ayu. 38:4-7) Mu ma zai dace mu dinga yabon Jehobah idan muna yin adduꞌa, ta wajen faɗin abubuwa da suka sa muke ƙaunar sa kuma muke girmama shi. Yayin da kake karanta Littafi Mai Tsarki kuma kake nazarin sa, ka yi ƙoƙari ka gano halayen Jehobah da suke burge ka. (Ayu. 37:23; Rom. 11:33) Saꞌan nan a cikin adduꞌarka, ka gaya masa yadda kake ji game da halayen. Za mu kuma iya yabon Jehobah don yadda yake taimaka mana da ꞌyanꞌuwanmu Kiristoci.—1 Sam. 2:1, 2. w23.05 3-4 sakin layi na 6-7
Talata, 7 ga Oktoba
Ku yi tafiyar da ta cancanta da masu bin Ubangiji.—Kol. 1:10.
A shekara ta 1919, bayin Jehobah sun sami ꞌyanci daga Babila Babba. A shekarar nan, “bawan nan mai aminci, mai hikima” ya soma aiki sosai domin mutane su soma yin tafiya a “Hanyar Tsarki.” (Mat. 24:45-47; Isha. 35:8) Saboda aikin da bayin Allah a dā suka yi don su shirya hanyar, waɗanda suka soma tafiya a hanyar sun koyi abubuwa da yawa game da Jehobah da kuma nufinsa. (K. Mag. 4:18) Kuma za su iya soma yin rayuwa da ta jitu da nufinsa. Jehobah bai bukaci mutanensa su yi canje-canjen da suke bukata farat ɗaya ba. A maimakon haka, ya ci-gaba da kyautata halayen mutanensa a-hankali-a-hankali. Hakika, idan lokacin da za mu iya faranta wa Allah rai a dukan abubuwan da muke yi ya zo, za mu yi farin ciki sosai! Kowace hanya tana bukatar gyara a-kai-a-kai. Tun daga 1919, an ci-gaba da yin aiki a “Hanyar Tsarki” domin a taimaka wa mutane da yawa su iya barin Babila Babba. w23.05 17 sakin layi na 15; 19 sakin layi na 16
Laraba, 8 ga Oktoba
Har abada ba zan bar ka ba.—Ibran. 13:5.
Hukumar da Ke Kula da Ayyukanmu tana horar da waɗanda suke taimaka wa kwamitoci dabam-dabam na Hukumar. Yanzu waɗannan mataimakan suna kula da ayyuka da yawa a ƙungiyar Jehobah. An koyar da su sosai don su ci-gaba da kula da tumakin Kristi. Dab da ƙarshen ƙunci mai girma, za a ɗauki sauran shafaffu da suka rage zuwa sama, amma ba za a daina bauta ta gaskiya a nan duniya ba. Shugabanmu Yesu Kristi zai tabbatar da cewa bayin Allah sun ci-gaba da bauta wa Jehobah. A lokacin, ƙasashen da suka haɗa kai, wato Gog na Magog, za su kawo mana hari. (Ezek. 38:18-20) Amma ba za su yi nasara ba, ba za su iya hana bayin Allah bauta masa ba. Hakika, Jehobah zai cece mu. A wahayin da aka nuna wa Yohanna, ya ga wani “babban taro,” wato waɗansu tumaki. An gaya wa Yohanna cewa wannan “babban taro” ko kuma taro mai girma, sun fito ne daga “azabar nan mai zafi.” (R. Yar. 7:9, 14) Don haka, muna da tabbaci cewa Jehobah zai cece su. w24.02 5-6 sakin layi na 13-14
Alhamis, 9 ga Oktoba
Kada ku kashe wutar ruhu mai tsarki.—1 Tas. 5:19, New World Translation.
Mene ne za mu yi don mu samu ruhu mai tsarki? Za mu iya roƙon Allah ya ba mu ruhu mai tsarki, mu yi nazarin Kalmarsa, kuma mu bauta wa Allah tare da mutanensa. Yin hakan zai taimaka mana mu kasance da “halin da ruhun Allah yake haifar.” (Gal. 5:22, 23) Waɗanda suke yin abubuwa masu kyau da tunanin abubuwa masu kyau ne kawai Allah yake ba wa ruhunsa. Idan muka ci-gaba da yin tunanin abubuwa marasa kyau kuma muna aikata su, zai daina ba mu ruhu mai tsarki. (1 Tas. 4:7, 8) Ƙari ga haka, idan muna so mu ci-gaba da samun ruhu mai tsarki, to, ‘kada mu rena annabci.’ (1 Tas. 5:20) A ayar nan, “annabci” yana nufin saƙon da Allah ya ba mu ta ruhu mai tsarki. Kamar abin da ya ce game da ranar Jehobah da kwanakin ƙarshe da muke ciki. Ba zai dace mu riƙa tunani cewa ranar Jehobah ko Armageddon ba za ta zo a zamaninmu ba. A maimakon haka, mu riƙa ɗaukan cewa za ta zo nan ba da daɗewa ba, ta wajen ci-gaba da yin ayyukan ibada da kuma kasancewa da “hali iri na Allah.”—2 Bit. 3:11, 12. w23.06 12 sakin layi na 13-14
Jumma’a, 10 ga Oktoba
Tsoron Yahweh shi ne mafarin hikima.—K. Mag. 9:10.
Me ya kamata mu Kiristoci mu yi idan muka ga batsa babu zato, ko a waya ko talabijin ko kuma a kwamfutarmu? Mu kau da idanunmu nan da nan. Wani abin da zai taimaka mana mu yi hakan shi ne idan muka tuna cewa abokantakarmu da Jehobah ita ce abu mafi daraja da muke da ita. Ko hotunan da mutane suke gani ba batsa ba ne za su iya sa mu tunanin yin lalata. Me ya sa ya dace mu guji kallon su? Domin bai kamata mu yi duk wani abin da zai sa mu tunanin yin lalata ba, komen ƙaƙantarsa. (Mat. 5:28, 29) Wani dattijo a ƙasar Thailand mai suna David ya ce: “Nakan tambayi kaina cewa: ‘Ko da ma wannan abin ba batsa ba ne, Jehobah zai ji daɗi idan na ci gaba da kallon sa?’ Irin wannan tunanin yakan taimake ni in yi abin da ya dace.” Idan muka zama masu tsoron yin abin da zai ɓata wa Jehobah rai, hakan zai taimaka mana mu yi abin da ya dace. Tsoron Allah “shi ne mafarin hikima.” w23.06 23 sakin layi na 12-13
Asabar, 11 ga Oktoba
Jamaꞌata, ku tafi ku shiga ɗakunanku.—Isha. 26:20.
‘Ɗakunan’ suna iya nufin ikilisiyoyinmu. Jehobah ya yi mana alkawari cewa a lokacin ƙunci mai girma, zai kāre mu idan muka ci-gaba da bauta masa tare da ꞌyanꞌuwanmu. Don haka, dole mu yi iya ƙoƙarinmu yanzu mu ƙaunaci ꞌyanꞌuwanmu da dukan zuciyarmu. Mai yiwuwa abin da zai ceci ranmu ke nan! Idan “Babbar Ranar Yahweh” ta zo, abubuwa za su yi ma kowa wuya sosai. (Zaf. 1:14, 15) Mutanen Jehobah ma za su sha wuya. Amma idan muka yi shiri tun yanzu, za mu iya kasancewa da kwanciyar hankali kuma mu taimaki ꞌyanꞌuwanmu. Za mu iya jimre duk wani abin da zai same mu. Idan ꞌyanꞌuwanmu suka shiga cikin wahala, za mu yi iya ƙoƙarinmu mu taimaka musu. Za mu tausaya musu, kuma mu ba su abin da suke bukata. Ƙari ga haka, za mu manne wa ꞌyanꞌuwanmu domin muna ƙaunar su sosai. Bayan ƙuncin, Jehobah zai ba mu rai na har abada a duniya, lokacin kuwa, balaꞌi da matsaloli duk za su zama labari.—Isha. 65:17. w23.07 7 sakin layi na 16-17
Lahadi, 12 ga Oktoba
[Jehobah] zai mai da ku cikakku, zai kafa ku, zai kuma ƙarfafa ku.—1 Bit. 5:10.
Kalmar Allah tana yawan cewa masu bangaskiya suna da ƙarfi. Amma ba a ko yaushe ne sukan ji cewa suna da ƙarfi ba. Misali, akwai lokacin da Sarki Dauda ya ce yana da “ƙarfi kamar babban dutse,” amma a wani lokacin kuma, ya ji “tsoro” sosai. (Zab. 30:7) Da Jehobah ya ba wa Samson ruhunsa, shi ma ya samu ƙarfi sosai. Amma ya san cewa idan babu ruhun nan, ‘zai rasa ƙarfinsa, ya zama kamar kowa.’ (Alƙa. 14:5, 6; 16:17) Hakika, Jehobah ne ya ba ma waɗannan bayinsa ƙarfi. Manzo Bulus shi ma ya dogara ga Jehobah don ya ba shi ƙarfi. (2 Kor. 12:9, 10) Ya yi fama da rashin lafiya. (Gal. 4:13, 14) Akwai kuma lokuta da yin abin da ya dace bai yi masa sauƙi ba. (Rom. 7:18, 19) Wasu lokuta kuma, ya yi fama da damuwa da tsoro. (2 Kor. 1:8, 9) Duk da haka, Bulus ya kasance da ƙarfi a lokutan nan. Me ya taimaka masa? Jehobah ne ya ba shi ƙarfin da yake bukata don ya jimre matsalolin nan. w23.10 12 sakin layi na 1-2
Litinin, 13 ga Oktoba
Yahweh yakan dubi zuciya ne.—1 Sam. 16:7.
Idan a wasu lokuta mun ji kamar ba mu da muhimmanci, zai dace mu tuna cewa Jehobah da kansa ne ya jawo mu wurinsa. (Yoh. 6:44) Ya ma fi mu sanin halaye masu kyau da muke da su, kuma ya san tunanin zuciyarmu. (2 Tar. 6:30) Don haka, idan ya ce muna da daraja, ya kamata mu yarda da shi. (1 Yoh. 3:19, 20) Kafin mu koyi gaskiya, mai yiwuwa wasunmu mun yi abubuwa marasa kyau, kuma hakan ya sa zuciyarmu tana damin mu. (1 Bit. 4:3) Wasu Kiristoci kuma sun daɗe suna bauta ma Jehobah da aminci, amma har yanzu suna fama da wata kasawa kuma hakan na sa zuciyarsu ta dame su. Kai kuma fa, shin haka kake ji? Idan haka ne, kada ka yi sanyin gwiwa domin akwai bayin Allah masu aminci da su ma suka yi fama da tunani kamar haka. Alal misali, saꞌad da manzo Bulus ya yi tunani a kan kurakuren da ya yi, sai ya ce shi abin tausayi ne. (Rom. 7:24) Bulus ya riga ya tuba daga zunubansa kuma ya yi baftisma. Amma ya kira kansa “mafi ƙanƙanta a cikin manzannin Yesu,” kuma ya ce shi ne “mafi zunubi.”—1 Kor. 15:9; 1 Tim. 1:15. w24.03 27 sakin layi na 5-6
Talata, 14 ga Oktoba
Sai suka bar . . . Gidan Yahweh.—2 Tar. 24:18.
Wani darasi da za mu iya koya daga shawara marar kyau da Sarki Yowash ya yanke shi ne, muna bukatar mu yi abokan kirki, wato waɗanda suke ƙaunar Jehobah kuma suke so su faranta masa rai. Bai kamata mu ce sai tsaranmu ne kawai za mu yi abokantaka da su ba. Ka tuna cewa Yehoyida ya girmi Yowash sosai, duk da haka sun zama abokai. Ka yi wa kanka tambayoyin nan: ‘Shin abokaina suna taimaka min in kasance da bangaskiya sosai? Suna ƙarfafa ni in yi irin rayuwar da Jehobah yake so? Sukan yi magana game da Jehobah da kuma gaskiyar da yake koya mana? Suna son ƙaꞌidodin Jehobah? Idan na yi abin da bai dace ba, sukan gaya min kuskurena?’ (K. Mag. 27:5, 6, 17) Gaskiyar ita ce, idan abokanka ba sa ƙaunar Jehobah, to ba ka bukatar su. Amma idan abokanka suna ƙaunar Jehobah, kar ka bar su domin za su taimaka maka!—K. Mag. 13:20. w23.09 9-10 sakin layi na 6-7
Laraba, 15 ga Oktoba
Ni ne Alpha da Omega.—R. Yar. 1:8, Tsohuwar Hausa a Sauƙaƙe.
Alpha shi ne harafi na farko a rubutun Helenanci kuma omega shi ne na ƙarshe. Jehobah ya ce Shi ne “Alpha da Omega” don ya nuna cewa idan har ya soma yin abu, tabbas zai yi nasara wajen ƙarasa shi. Da Jehobah ya halicci Adamu da Hauwaꞌu, Ya gaya musu cewa: “Ku yi ta haifuwa sosai ku yalwata, ku ciccika duniya ku kuma sha ƙarfinta.” (Far. 1:28) A wannan lokacin ne Jehobah ya bayyana nufinsa, “Alpha” ke nan, wato ‘farkon.’ Idan Jehobah ya cika nufin nan kuma ꞌyan Adam masu aminci sun cika duniya sun kuma mai da ita aljanna, wannan lokacin ne zai zama “Omega,” wato ‘ƙarshen.’ Da Jehobah ya gama halittar “sama da duniya, da dukan tulin abubuwan da suke cikinsu,” ya faɗi wani abin da ya nuna cewa tabbas nufinsa zai cika. Ya keɓe rana ta bakwai musamman don ya cika nufinsa ga ꞌyan Adam da kuma duniya. Ta haka, Jehobah yana ba da tabbaci ne cewa zai cika dukan nufinsa a ƙarshen rana ta bakwai.—Far. 2:1-3. w23.11 5 sakin layi na 13-14
Alhamis, 16 ga Oktoba
Ku shirya wa Yahweh hanya a daji, ku gyara hanya a hamada domin Allahnmu!—Isha. 40:3.
Wannan tafiyar za ta iya ɗauki Israꞌilawan watanni huɗu. Amma Jehobah ya yi alkawari cewa zai kawar da duk wani abin da zai iya hana su komawa. A ganin Yahudawa masu aminci, komawa ƙasar Israꞌila zai kawo musu albarka sosai fiye da sadaukarwa da za su yi. Albarka mafi muhimmanci da za su samu ita ce bautar da za su yi wa Jehobah. A Babila, babu haikali inda Yahudawan za su riƙa miƙa hadayu ga Jehobah kamar yadda Dokar Musa ta ce, kuma babu firistoci. Ƙari ga haka, mutanen da suke bauta ma allolin ƙarya sun fi waɗanda suke bauta wa Jehobah yawa sosai. Don haka, dubban Yahudawa da suke ƙaunar Jehobah suna marmarin lokacin da za su koma ƙasarsu domin su maido da bauta ta gaskiya. w23.05 14-15 sakin layi na 3-4
Jumma’a, 17 ga Oktoba
Ku yi zaman mutanen haske.—Afis. 5:8.
Ruhu mai tsarki ne zai taimaka mana mu ci-gaba da ‘zama mutanen haske.’ Me ya sa? Domin yin rayuwa mai tsarki a wannan duniyar da ke cike da halin lalata, bai da sauƙi ko kaɗan. (1 Tas. 4:3-5, 7, 8) Ruhu mai tsarki zai iya taimaka mana mu kauce ma irin tunanin mutanen da ke duniyar nan, waɗanda raꞌayinsu dabam yake da na Allah. Ruhu mai tsarki zai kuma taimaka mana mu dinga yin “ayyuka masu kyau, da zaman adalci.” (Afis. 5:9) Wani abin da za mu iya yi don mu sami ruhu mai tsarki shi ne, mu roƙi Allah cewa ya ba mu ruhunsa. Yesu ya ce Jehobah ‘zai ba da ruhu mai tsarki ga masu roƙonsa.’ (Luk. 11:13) Ƙari ga haka, idan muna yabon Jehobah tare da ꞌyanꞌuwanmu a taro, Jehobah zai ba mu ruhunsa. (Afis. 5:19, 20) Idan muna da ruhu mai tsarki, zai taimaka mana mu riƙa yin abin da Allah yake so. w24.03 23-24 sakin layi na 13-15
Asabar, 18 ga Oktoba
Ku yi ta roƙo za a ba ku. Ku yi ta nema za ku samu. Ku yi ta ƙwanƙwasawa, za a buɗe muku.—Luk. 11:9.
Kana bukatar ka ƙara zama mai haƙuri? Idan haka ne ka roƙi allah ya ba ka wannan halin. Haƙuri yana ɗaya daga cikin halayen da ruhu mai tsarki yake ba mu. (Gal. 5:22, 23) Don haka, za mu iya roƙan Allah ya ba mu ruhu mai tsarki, kuma ya sa mu kasance da halayen da ruhun yake haifarwa. Idan mun shiga yanayi da ke bukatar mu yi haƙuri, mu “yi ta roƙo” Allah ya ba mu ruhu mai tsarki don mu iya yin haƙuri. (Luk. 11:13) Za mu kuma iya roƙan Jehobah ya taimaka mana mu kasance da irin raꞌayinsa game da abubuwa. Bayan mun yi adduꞌa, muna bukatar mu yi iya ƙoƙarinmu don mu ci-gaba da yin haƙuri a kullum. Idan mun ci-gaba da roƙan Jehobah ya sa mu ƙara zama masu haƙuri, kuma muka ci-gaba da yin iya ƙoƙarinmu don mu nuna haƙuri, Jehobah zai taimaka mana mu kasance da halin nan ko da ba mu da shi a dā. Zai kuma taimaka mana mu yi tunani mai zurfi a kan labarai da ke Littafi Mai Tsarki. A Littafi Mai Tsarki, akwai labaran mutane da yawa da suka nuna haƙuri. Yin tunani a kan labaransu zai taimaka mana mu zama masu haƙuri. w23.08 22 sakin layi na 10-11
Lahadi, 19 ga Oktoba
Ku saki ragar kamun kifinku, ku jawo kifi.—Luk. 5:4.
Yesu ya tabbatar wa manzo Bitrus cewa Jehobah zai kula da shi. Yesu ya sake taimaka wa manzo Bitrus da kuma sauran manzannin su iya kama kifi a hanya mai ban mamaki. (Yoh. 21:4-6) Ba shakka, wannan alꞌajibi ya sa Bitrus ya gaskata cewa Jehobah zai tanada masa abubuwan da yake bukata. Mai yiwuwa manzannin sun tuna abin da Yesu ya faɗa cewa Jehobah zai iya tanada musu abubuwan da suke bukata muddin sun sa Mulkin Allah farko a rayuwarsu. (Mat. 6:33) Abubuwan nan sun taimaka wa Bitrus ya sa Mulkin Allah farko a rayuwarsa maimakon kamun kifi. Ya yi waꞌazi da ƙarfin zuciya a ranar Fentakos na shekara ta 33, kuma hakan ya sa dubban mutane sun zama almajiran Yesu. (A. M. 2:14, 37-41) Bayan haka, ya taimaka wa Samariyawa da waɗanda ba Yahudawa ba su koya game da Yesu kuma su zama almajiransa. (A. M. 8:14-17; 10:44-48) Hakika, Jehobah ya yi amfani da Bitrus sosai domin ya jawo mutane iri-iri zuwa ƙungiyarsa. w23.09 20 sakin layi na 1; 23 sakin layi na 11
Litinin, 20 ga Oktoba
Idan ba ku iya faɗa mini mafarkin duk da maꞌanarsa ba, to, za a yayyanka ku gaɓa-gaɓa.—Dan. 2:5.
Wajen shekaru biyu bayan da Babiloniyawa suka hallaka Urushalima. Sarkin Babila, wato, Nebukadnezzar ya yi mafarki mai ban tsoro game da wani babban gunki. Ya ce zai kashe dukan masu hikima na Babila, har da Daniyel idan har ba su gaya masa mafarkin da ya yi, da maꞌanarsa ba. (Dan. 2:3-5) Daniyel yana bukatar ya yi wani abu nan da nan, in ba haka ba, mutane da yawa za su mutu. Sai “ya shiga wurin sarki, ya roƙe shi ya ba shi lokaci domin ya bayyana masa maꞌanar mafarkin.” (Dan. 2:16) Daniyel ya yi hakan ne domin yana da ƙarfin zuciya da kuma bangaskiya. Babu inda aka nuna a Littafi Mai Tsarki cewa Daniyel ya taɓa faɗan maꞌanar mafarki kafin wannan lokacin. Ya gaya wa abokansa “su nemi jinƙai daga wurin Allah na sama game da wannan asirin.” (Dan. 2:18) Jehobah ya amsa adduꞌoꞌinsu. Da taimakonsa, Daniyel ya bayyana maꞌanar mafarkin Nebukadnezzar kuma hakan ya sa ba a kashe Daniyel da abokanansa ba. w23.08 3 sakin layi na 4
Talata, 21 ga Oktoba
Amma wanda ya jimre har zuwa ƙarshe, zai tsira.—Mat. 24:13.
Ka yi tunani a kan amfanin yin haƙuri. Idan muna da haƙuri, za mu zama masu farin ciki da kuma kamun kai. Don haka, haƙuri zai sa mu kasance da lafiyar jiki da kuma lafiyar ƙwaƙwalwa. Idan muna haƙuri da mutane, za mu kasance da dangantaka mai kyau da su. Ikilisiyarmu za ta kasance da haɗin kai. Idan ba ma saurin fushi, ko da wani ya ɓata mana rai, ba za mu yi abin da zai sa yanayin ya ƙara muni ba. (Zab. 37:8; K. Mag. 14:29) Abu mafi muhimmanci ma shi ne, muna yin koyi da Ubanmu na sama ke nan, kuma hakan zai sa mu ƙara yin kusa da shi. Babu shakka, haƙuri hali ne mai kyau da ke amfanar mu! Duk da cewa yin haƙuri bai da sauƙi, da taimakon Jehobah, za mu iya ci-gaba da zama masu haƙuri. Kuma yayin da muke haƙuri muna jiran sabuwar duniya, za mu iya kasance da tabbaci cewa ‘idanun Yahweh suna a kan masu tsoronsa, a kan masu sa zuciya ga ƙaunarsa marar canjawa.’ (Zab. 33:18) Bari dukanmu mu ƙudiri niyyar ci-gaba da saka haƙuri kamar riga. w23.08 22 sakin layi na 7; 25 sakin layi na 16-17
Laraba, 22 ga Oktoba
Bangaskiya wadda ba ta da ayyukan da suke tabbatar da ita banza ce.—Yak. 2:17.
Yakub ya bayyana cewa mutum zai iya ce shi mai bangaskiya ne, amma ayyukansa ba sa nuna hakan. (Yak. 2:1-5, 9) Yakub ya kuma yi misali da wani mutum da ya ga “wani ɗanꞌuwa ko wata ꞌyarꞌuwa” ba ta da ‘rigar sawa, da kuma abinci,’ amma ya ƙi ya taimaka mata. Ko da wannan ɗanꞌuwan yana ganin yana da bangaskiya, ayyukansa ba su nuna hakan ba. Don haka, bangaskiyarsa ba ta da amfani. (Yak. 2:14-16) Yakub ya ce Rahab ta nuna bangaskiya ta ayyukanta. (Yak. 2:25, 26) Ta ji labarin Jehobah kuma ta ga cewa yana taimaka wa Israꞌilawa. (Yosh. 2:9-11) Sai ta nuna bangaskiyarta ta ayyukanta. Ta ɓoye ꞌyan leƙen asiri guda biyu da ake nema a kashe. Abin da ta yi ya sa Jehobah ya ɗauke ta a matsayin mai adalci kamar yadda ya yi da Ibrahim. Kuma ya nuna mana cewa yana da muhimmanci mu nuna bangaskiyarmu ta ayyukanmu. w23.12 5-6 sakin layi na 12-13
Alhamis, 23 ga Oktoba
Ina adduꞌa cewa ku kafu sosai. Bari ƙauna ta zama tushenku.—Afis. 3:17.
A matsayinmu na Kiristoci, ba koyarwa masu sauƙi ne kawai muke so mu fahimta ba. Da taimakon ruhu mai tsarki, muna marmarin koyan “abubuwan Allah masu wuyar ganewa.” (1 Kor. 2:9, 10) Za ka iya yin nazari mai zurfi da zai sa ka ƙara kusantar Jehobah. Alal misali, za ka iya bincika yadda ya nuna ƙauna ga bayinsa a dā, da kuma yadda hakan ya nuna cewa yana ƙaunar ka. Za ka kuma iya bincika yadda Israꞌilawa suka bauta ma Jehobah a dā, kuma ka kwatanta shi da yadda muke bauta ma Jehobah a yau. Ko kuma za ka iya yin nazari mai zurfi game da annabce-annabce da Yesu ya cika saꞌad da yake duniya. Za ka yi farin ciki sosai idan ka bincika batutuwan nan ta yin amfani da Littafin Bincike Don Shaidun Jehobah. Yin nazari mai zurfi zai ƙarfafa bangaskiyarka kuma zai taimaka maka ka “sami sanin Allah.”—K. Mag. 2:4, 5. w23.10 18-19 sakin layi na 3-5
Jumma’a, 24 ga Oktoba
Fiye da kome kuma sai ku ƙaunaci juna da ƙauna ta ainihi, gama ƙauna takan yafe laifofi masu ɗumbun yawa.—1 Bit. 4:8.
Kalmar da manzo Bitrus ya yi amfani da ita a nan tana nufin “ƙaunar da aka ja ta don ta ƙara tsayi ko fāɗi.” Saurar ayar ta gaya mana abin da za mu yi idan muna da irin wannan ƙaunar, wato za ta sa mu yafe ko kuma mu rufe laifofin ꞌyanꞌuwanmu. Za mu iya kwatanta shi haka: A ce muna da teburi da wani abu ya ɗiga a kai, ya bushe kuma ba za a iya goge shi ba, za mu iya ɗaukan yadi mu buɗe shi kuma mu ja shi har sai ya rufe dukan teburin. Haka ma, idan muna ƙaunar ꞌyanꞌuwanmu sosai, za mu iya rufe laifofinsu, wato za mu iya yafe musu, ko da “laifofi masu ɗumbun yawa” suka yi mana. Ya kamata mu zama masu ƙaunar ꞌyanꞌuwanmu sosai, har mu iya yafe laifin da suka yi mana ko saꞌad da yin hakan ya yi mana wuya. (Kol. 3:13) Idan muka yafe ma ꞌyanꞌuwanmu, hakan zai nuna cewa muna ƙaunar su sosai, kuma muna so mu faranta wa Jehobah rai. w23.11 11-12 sakin layi na 13-15
Asabar, 25 ga Oktoba
Saꞌan nan Shafan . . . ya karanta wa sarki.—2 Tar. 34:18.
Saꞌad da Sarki Josiya ya kai shekaru 26, ya soma gyara haikalin Jehobah. Saꞌad da ake aikin, an “sami Littafin Koyarwar Yahweh, wanda aka bayar ta bakin Musa.” Da aka karanta wa sarkin littafin, nan da nan ya bi abin da aka rubuta a ciki. (2 Tar. 34:14, 19-21) Za ka so ka riƙa karanta Littafi Mai Tsarki a kullum? Idan kana ƙoƙarin yin hakan, shin kana jin daɗin sa? Shin kana mai da hankali ga ayoyin da za su taimaka maka? Saꞌad da Josiya yake wajen shekara 39, ya yi wani kuskuren da ya yi ajalinsa. Maimako ya nemi nufin Jehobah, ya dogara ga kansa. (2 Tar. 35:20-25) Wannan ya koya mana cewa komen tsufanmu ko kuma yawan shekaru da muka yi muna nazarin Littafi Mai Tsarki, dole ne mu ci-gaba da neman nufin Jehobah. Hakan yana nufin cewa za mu riƙa roƙan sa ya yi mana ja-goranci, da yin nazarin Kalmarsa, da kuma bin shawarar Kiristoci da suka manyanta. Hakan zai taimaka mana mu guji yin kuskure mai tsanani, kuma ya taimaka mana mu yi farin ciki a rayuwa.—Yak. 1:25. w23.09 12 sakin layi na 15-16
Lahadi, 26 ga Oktoba
Allah yana ƙin mai girman kai, amma yana yin alheri ga mai sauƙin kai.—Yak. 4:6.
Littafi Mai Tsarki ya yi magana game da mata da yawa da suka ƙaunaci Jehobah sosai kuma suka bauta masa. Matan sun nuna “natsuwa” da “aminci cikin kome.” (1 Tim. 3:11) Ƙari ga haka, ꞌyan mata Kiristoci za su iya bin misalin mata a ikilisiyarsu da suke ƙaunar Jehobah. ꞌYan mata, ku yi tunanin mata da kuka sani da ke da halaye masu kyau da za ku iya yin koyi da su. Ku lura da halayensu, saꞌan nan ku yi tunanin yadda ku ma za ku bi halinsu. Idan muna so mu zama Kiristoci da suka manyanta, muna bukatar sauƙin kai. Idan mace tana da sauƙin kai, za ta kasance da dangantaka mai kyau da Jehobah da kuma mutane. Alal misali, macen da take ƙaunar Jehobah za ta bi abin da ke 1 Korintiyawa 11:3. A wurin, Jehobah ya nuna waɗanda yake so su yi ja-goranci a ikilisiya da kuma wanda zai yi hakan a iyali. Akwai hanyoyi da Jehobah yake so dukanmu mu bi abin da ya faɗa a ayar nan a ikilisiya da kuma a iyali. w23.12 18-19 sakin layi na 3-5
Litinin, 27 ga Oktoba
Maza su ƙaunaci matansu kamar yadda suke ƙaunar jikinsu.—Afis. 5:28.
Jehobah yana so maigida ya ƙaunaci matarsa, ya biya bukatunta, ya zama abokinta kuma ya taimaka mata ta bauta masa da kyau. Zama mai hankali, da daraja mata, da zama wanda za a iya yarda da shi, za su taimaka maka ka zama miji nagari. Bayan ka yi aure, za ku iya haifan yara. Wane darasi ne za ka iya koya daga wurin Jehobah game da zama uba nagari? (Afis. 6:4) Jehobah ya gaya wa ɗansa Yesu a gaban jamaꞌa cewa yana ƙaunar sa kuma ya amince da shi. (Mat. 3:17) Idan kana da yara, ka riƙa tabbatar musu da cewa kana ƙaunar su. Ka riƙa yaba musu don abubuwa masu kyau da suke yi. Ubanni da suke yin koyi da Jehobah suna taimaka wa yaransu su zama Kiristocin da suka manyanta. Za ka iya yin shirin zama uba nagari ta wajen kula da ꞌyan iyalinku da ꞌyanꞌuwa a ikilisiya. Ka riƙa gaya musu cewa kana ƙaunar su kuma suna da muhimmanci a gare ka.—Yoh. 15:9. w23.12 28-29 sakin layi na 17-18
Talata, 28 ga Oktoba
[Jehobah] ne tushe a zamaninmu.—Isha. 33:6.
Ko da yake mu bayin Jehobah ne, mu ma muna fuskantar matsaloli kuma muna rashin lafiya kamar yadda sauran mutane suke yi. Ƙari ga haka, muna iya fuskantar hamayya ko kuma tsanantawa daga mutanen da ba sa son ganin mu. Jehobah ba ya hana abubuwan nan faruwa da mu, amma ya yi alkawarin cewa zai taimaka mana. (Isha. 41:10) Da taimakon Jehobah, ko da mun shiga yanayi mai wuya sosai, za mu iya yin farin ciki, mu yanke shawarwari masu kyau kuma mu riƙe amincinmu. Jehobah ya yi alkawari cewa zai ba mu “salama.” (Filib. 4:6, 7) Wannan salamar tana nufin kwanciyar hankali da kuma natsuwa da muke samu don muna da dangantaka mai kyau da Allah. Wannan salamar ta “wuce dukan ganewar ɗan Adam,” wato tana taimaka mana a hanya mai ban mamaki. Ka taɓa yin adduꞌa ga Jehobah kuma ka ji hankalinka ya kwanta? Mai yiwuwa abin ya ba ka mamaki. ‘Salamar’ da Jehobah ya ba ka ne ya sa ka ji hakan. w24.01 20 sakin layi na 2; 21 sakin layi na 4
Laraba, 29 ga Oktoba
Yabi Yahweh, ya raina! Dukan abin da ke a cikina, yabi Sunansa mai tsarki!—Zab. 103:1.
Waɗanda suke ƙaunar Jehobah suna so su yabi sunansa da dukan zuciyarsu. Sarki Dauda ya fahimci cewa yabon sunan Jehobah ɗaya yake da yabon Jehobah. Idan muka ji sunan Jehobah, mukan yi tunanin halayensa masu kyau da kuma abubuwan ban mamaki da ya yi. Dauda ya ɗauki sunan Ubansa na sama da tsarki kuma ya yabi sunan. Ya ce zai yi hakan da ‘dukan abin da ke a cikinsa,’ wato da dukan zuciyarsa. Lawiyawa ma sun ja-goranci mutane wajen yabon sunan Jehobah. Sun ce kalmomin bakinsu ba su isa su yabi Jehobah yadda ya dace ba. (Neh. 9:5) Babu shakka, yadda suka yabi Jehobah da dukan zuciyarsu kuma suka yi hakan da sauƙin kai, ya sa Jehobah farin ciki. w24.02 9 sakin layi na 6
Alhamis, 30 ga Oktoba
Babban abin shi ne duk inda muka kai, mu ci gaba daga nan.—Filib. 3:16.
Jehobah ba zai yi baƙin ciki domin ka kasa cim ma maƙasudin da ya fi ƙarfinka ba. (2 Kor. 8:12) Ka koyi darasi daga abubuwan da suka sa ka samu koma baya. Ka riƙa tunanin abubuwan da ka cim ma. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Allah ba marar adalci ba ne. Ba zai ƙyale ayyukanku da kuka yi ba.” (Ibran. 6:10) Don haka, bai kamata kai ma ka manta ba. Ka yi tunani a kan abubuwan da ka riga ka cim ma kamar ƙarfafa dangantakarka da Jehobah, da yin waꞌazi da kuma yin baftisma. Kamar yadda ka cim ma maƙasudanka a dā, haka ma za ka iya ci-gaba da yin ƙoƙari har sai ka cim ma waɗanda kake da su a yanzu. Za ka iya cim ma maƙasudinka da taimakon Jehobah. Yayin da kake ƙoƙari don ka cim ma maƙasudinka, ka riƙa tuna da yadda Jehobah yake taimaka maka da kuma albarka da yake maka, domin yin hakan zai sa ka farin ciki. (2 Kor. 4:7) Idan ba ka gaji ba, za ka samu ƙarin albarka.—Gal. 6:9. w23.05 31 sakin layi na 16-18
Jumma’a, 31 ga Oktoba
Shi Uban yana ƙaunarku da kansa, saboda kun ƙaunace ni, kun kuma ba da gaskiya cewa daga wurin Allah na fito.—Yoh. 16:27.
Jehobah yana neman hanyar da zai nuna wa mutanensa cewa ya amince da su. A cikin Littafi Mai Tsarki, sau biyu Jehobah ya gaya wa Yesu cewa shi Ɗansa ne da yake ƙauna kuma Ya amince da shi. (Mat. 3:17; 17:5) Za ka so ka ji cewa Jehobah yana ƙaunar ka kuma ya amince da kai? Jehobah ba ya magana da mu daga sama, amma yana magana da mu ta wurin Kalmarsa. Idan muka karanta abubuwa masu ban ƙarfafa da Yesu ya gaya wa mabiyansa, kamar Jehobah ne yake magana da mu. Yesu yana da halaye daidai irin na Ubansa. Don haka, a duk lokacin da muka karanta yadda Yesu ya gaya wa almajiransa cewa ya amince da su, mu ɗauka cewa Jehobah ne yake magana da mu. (Yoh. 15:9, 15) Idan muna fuskantar matsaloli, hakan ba ya nufin cewa Jehobah ya daina amincewa da mu. A maimakon haka, matsaloli suna ba mu damar nuna wa Jehobah yadda muke ƙaunar sa da kuma yadda muka dogara gare shi.—Yak. 1:12. w24.03 28 sakin layi na 10-11