Asabar, 18 ga Oktoba
Ku yi ta roƙo za a ba ku. Ku yi ta nema za ku samu. Ku yi ta ƙwanƙwasawa, za a buɗe muku.—Luk. 11:9.
Kana bukatar ka ƙara zama mai haƙuri? Idan haka ne ka roƙi allah ya ba ka wannan halin. Haƙuri yana ɗaya daga cikin halayen da ruhu mai tsarki yake ba mu. (Gal. 5:22, 23) Don haka, za mu iya roƙan Allah ya ba mu ruhu mai tsarki, kuma ya sa mu kasance da halayen da ruhun yake haifarwa. Idan mun shiga yanayi da ke bukatar mu yi haƙuri, mu “yi ta roƙo” Allah ya ba mu ruhu mai tsarki don mu iya yin haƙuri. (Luk. 11:13) Za mu kuma iya roƙan Jehobah ya taimaka mana mu kasance da irin raꞌayinsa game da abubuwa. Bayan mun yi adduꞌa, muna bukatar mu yi iya ƙoƙarinmu don mu ci-gaba da yin haƙuri a kullum. Idan mun ci-gaba da roƙan Jehobah ya sa mu ƙara zama masu haƙuri, kuma muka ci-gaba da yin iya ƙoƙarinmu don mu nuna haƙuri, Jehobah zai taimaka mana mu kasance da halin nan ko da ba mu da shi a dā. Zai kuma taimaka mana mu yi tunani mai zurfi a kan labarai da ke Littafi Mai Tsarki. A Littafi Mai Tsarki, akwai labaran mutane da yawa da suka nuna haƙuri. Yin tunani a kan labaransu zai taimaka mana mu zama masu haƙuri. w23.08 22 sakin layi na 10-11
Lahadi, 19 ga Oktoba
Ku saki ragar kamun kifinku, ku jawo kifi.—Luk. 5:4.
Yesu ya tabbatar wa manzo Bitrus cewa Jehobah zai kula da shi. Yesu ya sake taimaka wa manzo Bitrus da kuma sauran manzannin su iya kama kifi a hanya mai ban mamaki. (Yoh. 21:4-6) Ba shakka, wannan alꞌajibi ya sa Bitrus ya gaskata cewa Jehobah zai tanada masa abubuwan da yake bukata. Mai yiwuwa manzannin sun tuna abin da Yesu ya faɗa cewa Jehobah zai iya tanada musu abubuwan da suke bukata muddin sun sa Mulkin Allah farko a rayuwarsu. (Mat. 6:33) Abubuwan nan sun taimaka wa Bitrus ya sa Mulkin Allah farko a rayuwarsa maimakon kamun kifi. Ya yi waꞌazi da ƙarfin zuciya a ranar Fentakos na shekara ta 33, kuma hakan ya sa dubban mutane sun zama almajiran Yesu. (A. M. 2:14, 37-41) Bayan haka, ya taimaka wa Samariyawa da waɗanda ba Yahudawa ba su koya game da Yesu kuma su zama almajiransa. (A. M. 8:14-17; 10:44-48) Hakika, Jehobah ya yi amfani da Bitrus sosai domin ya jawo mutane iri-iri zuwa ƙungiyarsa. w23.09 20 sakin layi na 1; 23 sakin layi na 11
Litinin, 20 ga Oktoba
Idan ba ku iya faɗa mini mafarkin duk da maꞌanarsa ba, to, za a yayyanka ku gaɓa-gaɓa.—Dan. 2:5.
Wajen shekaru biyu bayan da Babiloniyawa suka hallaka Urushalima. Sarkin Babila, wato, Nebukadnezzar ya yi mafarki mai ban tsoro game da wani babban gunki. Ya ce zai kashe dukan masu hikima na Babila, har da Daniyel idan har ba su gaya masa mafarkin da ya yi, da maꞌanarsa ba. (Dan. 2:3-5) Daniyel yana bukatar ya yi wani abu nan da nan, in ba haka ba, mutane da yawa za su mutu. Sai “ya shiga wurin sarki, ya roƙe shi ya ba shi lokaci domin ya bayyana masa maꞌanar mafarkin.” (Dan. 2:16) Daniyel ya yi hakan ne domin yana da ƙarfin zuciya da kuma bangaskiya. Babu inda aka nuna a Littafi Mai Tsarki cewa Daniyel ya taɓa faɗan maꞌanar mafarki kafin wannan lokacin. Ya gaya wa abokansa “su nemi jinƙai daga wurin Allah na sama game da wannan asirin.” (Dan. 2:18) Jehobah ya amsa adduꞌoꞌinsu. Da taimakonsa, Daniyel ya bayyana maꞌanar mafarkin Nebukadnezzar kuma hakan ya sa ba a kashe Daniyel da abokanansa ba. w23.08 3 sakin layi na 4