WAƘA TA 151
Zai Kira Su
(Ayuba 14:13-15)
1. Yau muna nan, gobe sai labari,
Rayuwa babu tabbas.
Kwanakinmu duk ba su da yawa,
Hakan abin ƙunci ne.
To, me zai faru in muka rasu?
Ga alkawarin Allah:
(AMSHI)
Zai kira duk za su amsa,
Za su ji kiransa fa.
Ya ƙosa ya ta da su,
Abin da ya ce ke nan.
Don haka, kar mu yi shakka,
Mu yi imani da Shi.
Allah yana da iko
Mu rayu har abada.
2. Aminan Allah ko da sun rasu
Ba zai manta da su ba.
Allah Jehobah zai tayar da su
Domin duk amincinsu.
Zai cika dukan alkawuransa,
Rayuwa a Aljanna.
(AMSHI)
Zai kira duk za su amsa,
Za su ji kiransa fa.
Ya ƙosa ya ta da su,
Abin da ya ce ke nan.
Don haka, kar mu yi shakka,
Mu yi imani da Shi.
Allah yana da iko
Mu rayu har abada.
(Ka kuma duba Yoh. 6:40; 11:11, 43; Yaƙ. 4:14.)