WAƘA TA 50
Alkawarin Bauta wa Jehobah
Hoto
	- 1. Na ba Allah zucina - Don ta so dokokinsa. - Na ba Allah muryata - Don ta rera mai yabo. 
- 2. Ya Jehobah Allahna, - Na ba ka rayuwata - Da kuma wadatata, - Don in bi umurninka. 
- 3. Allah ka taimaka min - Domin in yi nufinka. - Bari duk ayyukana - Su faranta maka rai. 
(Ka kuma duba Zab. 40:8; Yoh. 8:29; 2 Kor. 10:5.)