WAƘA TA 65
Mu Riƙa Samun Ci Gaba!
(Ibraniyawa 6:1)
1. Mu duƙufa samun ci gaba kullum!
Mu bar kowa ya ga halayenmu masu kyau.
Mu yi himma a yaɗa bisharar nan,
Allah za ya kāre mu.
Dukanmu muna da aikin yi,
Aikin Yesu Ubangijinmu.
Mu roƙi Jehobah ya taimake mu,
Don mu riƙa nagarta.
2. Duk mu ƙoƙarta mu riƙa wa’azi!
Mu sanar da saƙon da zai sa a sami rai,
Kuma zai sa a riƙa yabon Allah,
Su yabe shi da ƙwazo.
Maƙiya za su tsorata mu,
Amma kada mu ji tsoron su.
Mu riƙa shelar Mulkin nan da ƙwazo,
Mu yi hakan koyaushe.
3. Duk mu ƙoƙarta mu riƙa biyayya,
Mu riƙa inganta
wa’azinmu koyaushe.
Za mu bi ja-gorancin ruhun Allah
Da duk zuciyarmu fa.
Mu ƙaunaci dukan ɗalibai,
Don su so Kalmar Allah sosai.
Su riƙa samun ci gaba koyaushe,
Haskensu ya haskaka.
(Ka kuma duba Filib. 1:27; 3:16; Ibran. 10:39.)