Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w12 10/1 pp. 18-19
  • A Yaushe Ne Yesu Ya Zama Sarki?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • A Yaushe Ne Yesu Ya Zama Sarki?
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
  • Makamantan Littattafai
  • 1914—Shekara Mai Muhimmanci a Annabcin Littafi Mai Tsarki
    Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?
  • Mene ne Ƙirgen Littafi Mai Tsarki ya Bayyana Game da Shekara ta 1914
    Amsoshin Tambayoyi Daga Littafi Mai Tsarki
  • Mulkin Allah Yana Sarauta!
    Ka Ji Dadin Rayuwa Har Abada!​—Don Nazarin Littafi Mai Tsarki
  • Mene Ne Mulkin Allah?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
w12 10/1 pp. 18-19

Ka Koya Daga Kalmar Allah

A Yaushe Ne Yesu Ya Zama Sarki?

Wannan talifin ya tattauna tambayoyin da wataƙila ka taɓa yin tunani a kansu kuma ya nuna inda za ka iya samun amsoshinsu a cikin naka Littafi Mai Tsarki. Shaidun Jehobah za su yi farin cikin tattauna waɗannan amsoshin da kai.

1. Wane mulki ne aka yi wa Yesu alkawarinsa?

Allah ya yi alkawari cewa wani daga zuriyar Sarki Dauda zai zauna bisa kursiyin Allah har abada. Wanda aka yi alkawarinsa shi ne Yesu, kuma yanzu yana sarauta a sama a matsayin Sarkin Mulkin Allah.—Ka karanta Zabura 89:4; Luka 1:32, 33.

Jehobah ya zaɓi Dauda ya zama sarkin mutanensa Isra’ilawa tun yana yaro. Sa’ad da Dauda ya mutu, Allah ya zaɓi Sulemanu ya zauna bisa “kursiyin Ubangiji.” (1 Labarbaru 28:4, 5; 29:23) Bayan Sulemanu ya mutu, sarakuna da yawa sun yi sarauta a Urushalima amma yawancinsu ba su da aminci. Daga baya, Jehobah ya ƙyale rundunan Babila su halaka Urushalima kuma su cire sarkin da yake sarauta a lokacin. Hakan ya faru ne a shekara ta 607 kafin zamanin Kristi. Kuma tun daga lokacin, babu wani sarki daga zuriyar Dauda da ya yi sarauta a Urushalima.—Ka karanta Ezekiyel 21:27.

2. Daga wane lokaci zuwa wane lokaci ne Mulkin Allah ya kasance babu sarki?

Bayan an halaka Urushalima, Jehobah ya faɗa wa annabinsa Daniyel cewa Allah zai zaɓi sarkin da zai yi sarauta daga sama. Wane lokaci ne sarkin nan zai fara sarauta?—Ka karanta Daniyel 7:13, 14.

Daniyel ya bayyana wani wahayi wanda ya nuna cewa Allah ya umurta a sare wani itace mai girma, daidai da umurnin da Allah ya ba da cewa a daina sarauta a Urushalima. Amma za a bar jijiyar itacen a ƙasa don ya sake girma bayan “lokatai guda bakwai.” Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa “lokatai” uku da rabi daidai ne da kwanaki 1,260, saboda haka, adadin “lokatai bakwai” zai zama kwanaki 2,520. (Ru’ya ta Yohanna 12:6, 14) A wani lokaci, kwanaki suna nufin shekaru a cikin annabcin da aka rubuta a Littafi Mai Tsarki. (Littafin Lissafi 14:34) Saboda haka, Mulkin Allah ba zai kasance da sarki ba sai bayan shekara 2,520.—Ka karanta Daniyel 4:10-17.

3. A yaushe ne Yesu ya zama Sarki?

A shekara ta 1914, wato, shekaru 2,520 cir bayan an halaka Urushalima, Allah ya naɗa Yesu ya zama Sarki a sama. Mataki na farko da Yesu ya ɗauka sa’ad da ya zama sarki shi ne ya koro Shaiɗan da aljanunsa daga sama. (Ru’ya ta Yohanna 12:7-10) Wannan abin ya faru ne a sama, amma sakamakon haka shi ne taɓarɓarewar abubuwa a duniya. (Ru’ya ta Yohanna 12:12) Abubuwan da suke faruwa tun shekara ta 1914 sun nuna cewa Yesu ya zama sarki a wannan shekarar.—Ka karanta Matta 24:14; Luka 21:10, 11, 31.

4. Ta yaya za ka amfana daga sarautar Yesu?

Annabcin da ke cika tun daga lokacin da aka naɗa Yesu suna nuna cewa za ka iya dogara ga abin da ke cikin Littafi Mai Tsarki. Ba da daɗewa ba, Sarki Yesu zai yi amfani da ikonsa don ya kawo salama.—Ka karanta Zabura 72:8, 12, 13; Daniyel 2:44.

Don ƙarin bayani, ka duba shafuffuka na 215-218 na wannan littafin Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa? Shaidun Jehobah suka wallafa.

[Taswira a shafi na 18, 19]

(Don ganin cikakken rubutun, ka duba littafin)

Oktoba ta shekara ta Oktoba ta shekara ta

607 kafin zamanin Kristi 1914 a zamanin Kristi

← Shekaru 2,520 →

1000 kafin 1 kafin 1 a 1000 a 2000 a

zamanin zamanin zamanin zamanin zamanin

Kristi Kristi Kristi Kristi Kristi

← 606 da wata 3 →← 1,913 da wata 9 →

An kawo Ka yi amfani da kalkuleta: Allah ya naɗa Yesu

ƙarshen sarauta Shekaru 606 da wata 3 Sarki mai iko

a Urushalima Shekaru 1,913 da wata 9 bisa al’ummai

= 2,520

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba