Sun Ci Gaba Da Tafiya Cikin Gaskiya
“Ba ni da wani farinciki wanda ya fi wannan, in ji labarin ’ya’yana suna tafiya cikin gaskiya.”—3 YOHANNA 4.
1. A kan menene “gaskiyar bishara” ta mai da hankali?
JEHOVAH yana amincewa da waɗanda suke yi masa sujjada “cikin ruhu da cikin gaskiya” ne kawai. (Yohanna 4:24) Suna biyayya da gaskiya, sun yarda da ilahirin koyarwar Kirista da ke bisa Kalmar Allah. Wannan “gaskiyar bishara” ta mai da hankali a kan Yesu Kristi da kuma kunita ikon mallakar Jehovah na Mulkin. (Galatiyawa 2:14) Allah ya ƙyale “aikawar saɓo” ga waɗanda suka fi son ƙarya, amma ceto ya dangana a kan samun bangaskiya cikin bisharar da yin tafiya cikin gaskiya.—2 Tassalunikawa 2:9-12; Afisawa 1:13, 14.
2. Don me manzo Yohanna ya yi godiya sosai, wace irin dangantaka yake da ita da Gayus?
2 Masu shelar Mulki “abokan aiki tare da gaskiya” ne. Kamar manzo Yohanna da abokinsa Gayus, sun riƙe gaskiya gam kuma sun yi tafiya cikinta. Yohanna ya rubuta wa Gayus: “Ba ni da wani farinciki wanda ya fi wannan, in ji labarin ’ya’yana suna tafiya cikin gaskiya.” (3 Yohanna 3-8) Ko idan ma Yohanna tsoho bai koya wa Gayus gaskiyar ba, tsufan manzon, manyanta ta Kirista, da ƙauna ta uba ya sa ya dace da a ɗauki wannan saurayin cikin ’ya’yan ruhaniya na Yohanna.
Gaskiya da Kuma Bauta ta Kirista
3. Menene manufa da amfanin taro da Kiristoci na farko suka yi?
3 Don su koyi gaskiya, Kiristoci na farko suna taro na ikilisiya, sau da yawa a gidaje. (Romawa 16:3-5) Da haka suna samun ƙarfafa kuma suna motsa juna zuwa ga ƙauna da nagargarun ayyuka. (Ibraniyawa 10:24, 25) Game da waɗanda suke da’awa su Kiristoci ne na baya bayan nan, Tertullian (a misalin shekara ta 155–bayan ta 220 A.Z.) ya rubuta: “Muna taruwa mu karanta littattafan Allah . . . Da waɗannan kalmomi masu tsarki muka ciyar da bangaskiyarmu, muka ƙarfafa begenmu, muka tabbatar da dogararmu.”—Apology, babi na 39.
4. Waƙa tana da wane matsayi a taron Kirista?
4 Wataƙila rera waƙa ɓangare ne na taron Kiristoci na farko. (Afisawa 5:19; Kolossiyawa 3:16) Farfesa Henry Chadwick ya rubuta cewa ɗan sūka Celsus na ƙarni na biyu ya ce waƙoƙi da Kiristoci suke amfani da su, “daɗinsu suka motsa zuciyarsa sosai.” Chadwick ya daɗa cewa: “Clement na Alexandria ne marubucin Kirista na farko da ya tattauna irin kiɗa da ta dace Kirista ya yi amfani da ita. Ya ce bai kamata ya zama kiɗa da ke ta da sha’awar jima’i ba.” (The Early Church, shafofi 274-275) Yadda Kiristoci na farko suka rera waƙa sa’ad da suka taru, haka Shaidun Jehovah sau da yawa suke rera waƙoƙi da ke bisa Littafi Mai Tsarki da sun ƙunshi zabura da ke yabon Allah da Mulkinsa.
5. (a) Yaya ake ba da ja-gora ta ruhaniya a ikilisiyoyin Kirista na farko? (b) Ta yaya Kiristoci na gaskiya suka yi amfani da kalmomin Yesu da ke rubuce a Matta 23:8, 9?
5 A ikilisiyoyin Kirista na farko, dattawa suna koyar da gaskiya, bayi masu hidima suna taimakon ’yan’uwa masu bi a hanyoyi dabam dabam. (Filibbiyawa 1:1) Hukumar mulki da take dogara da Kalmar Allah da ruhu mai tsarki suna tanadin ja-gora na ruhaniya. (Ayukan Manzanni 15:6, 23-31) Ba a amfani da laƙabi na addini domin Yesu ya ba da umurni ga almajiransa: “Kada a kira ku Malam: gama malaminku ɗaya ne, ku duka kuwa ’yan’uwa ne. Kuma kada ku ce da kowane mutum a duniya ubanku: gama ɗaya ne Ubanku, shi na sama.” (Matta 23:8, 9) A wannan hanyar da wasu da yawa akwai kamani tsakanin Kiristoci na farko da Shaidun Jehovah.
An Tsananta Musu don Wa’azin Gaskiya
6, 7. Ko da yake suna sanar da saƙo na salama, yaya aka bi da Kiristoci na gaskiya?
6 Ko da yake suna shelar saƙon salama na Mulkin, an tsananta wa Kiristoci na farko, yadda aka yi wa Yesu. (Yohanna 15:20; 17:14) Ɗan tarihi John L. von Mosheim ya kira Kiristoci na ƙarni na farko “rukunin mutane da suka fi halin salama, waɗanda ba su taɓa tunanin mugunta ba ga jama’a.” Dokta Mosheim ya faɗa cewa abin da “yake ba Romawa haushi game da Kiristoci shi ne yadda bautarsu ke da sauƙi, wadda ba ta yi kama da bukukuwan addini na wasu mutane ba.” Ya daɗa cewa: “Ba sa miƙa hadayu, ba su da haikalai, ba su da siffofi, ko tsarin firistoci; wannan ya isa ya jawo musu zargi daga mutane da ba su san wannan ba, waɗanda suke tunani babu addini idan ba waɗannan abubuwa. Da haka ana kallonsu kamar ba su yarda da akwai Allah ba; kuma ga dokar Roma, waɗanda aka tuhume su da rashin yarda da Allah suna da lahani ga jam’iyyar ’yan Adam.”
7 Firistoci, masu zane, da wasu da suke samun abincinsu ta bautar gumaka suka zuga jama’a a kan Kiristoci, da ba su saka hannu cikin ayyukan bautar gumaka ba. (Ayukan Manzanni 19:23-40; 1 Korinthiyawa 10:14) Tertullian ya rubuta: “Sun gaskata cewa Kiristoci ne suke haddasa kowanne bala’i na Jihar, kowane tsautsayi na mutanen. Idan rigyawar ta kai har ganuwa, idan kogin Nilu bai zube ba ya jiƙa gona, idan ba a yi ruwa ba ko an yi girgizar ƙasa, idan ana yunwa, idan an yi annoba, kirar da ake yi: ‘A jefa Kiristoci ga zaki!’ ” Kiristoci na gaskiya ‘suna tsare kansu daga gumaka, ko menene sakamakon haka.’—1 Yohanna 5:21.
Gaskiya da Kuma Bukukuwa na Addini
8. Me ya sa waɗanda suke tafiya cikin gaskiya ba sa bikin Kirsimati?
8 Waɗanda suke tafiya cikin gaskiya suna guje wa bukukuwa da ba na nassi ba domin ‘haske ba shi da tarayya da duhu.’ (2 Korinthiyawa 6:14-18) Alal misali, ba sa bikin Kirsimati, da ake yi a ranar 25 ga Disamba. The World Book Encyclopedia ya ce: “Babu wanda ya san daidai ranar haihuwar Kristi.” The Encyclopedia Americana (Bugun 1956) ya ce: “Saturnalia, wani bikin Roma da ake yi a tsakiyar watan Disamba, ya zama misali na al’adu da yawa na Kirsimati.” M’Clintock da Strong’s Cyclopædia ya lura cewa: “Bikin Kirsimati ba umurni ba ne daga Allah, kuma ba daga Sabon Alkawari ba ne.” Littafin nan Daily Life in the Time of Jesus ya ce: “Garke . . . ba sa fita fili lokacin sanyi; wannan ya nuna cewa watan Kirsimati lokacin sanyi ne, saboda haka ba zai zama daidai ba, tun da yake Linjila ta ce makiyaya suna fili.”—Luka 2:8-11.
9. Me ya sa bayin Jehovah na dā da yanzu ba sa bikin Ista?
9 Ista an ce wai bikin tashin Kristi daga matattu ne, amma tushe masu tabbaci sun haɗa ta da bautar ƙarya. The Westminster Dictionary of the Bible ya ce Ista “asalinta bikin rani ne da ke ɗaukaka allahiya Teutonici na haske da damina da aka sani a Anglo-Saxon da Eastre,” ko Eostre. Ko yaya dai, Encyclopædia Britannica (Bugu na 11) ya ce: “Babu wani nuni na bikin Ista cikin Sabon Alkawari.” Ista ba bikin Kiristoci na farko ba ne kuma yau mutanen Jehovah ba sa yin bikin.
10. Wane biki Yesu ya kafa, su waye suke yinsa daidai?
10 Yesu bai ce mabiyansa su yi bikin haihuwarsa ko tashinsa daga matattu ba, amma ya kafa Abin Tuni na mutuwarsa ta hadaya. (Romawa 5:8) Hakika, wannan ne kawai biki da ya umurce almajiransa su yi. (Luka 22:19, 20) Ana kiransa Jibin Maraice na Ubangiji kuma, wannan bikin na shekara shekara har ila Shaidun Jehovah suna yinsa.—1 Korinthiyawa 11:20-26.
An Yi Shelar Gaskiya a Dukan Duniya
11, 12. Ta yaya waɗanda suke tafiya cikin gaskiya suke tallafa wa aikinsu na wa’azi?
11 Waɗanda suka san gaskiya suna ɗauka ta gata ce su ba da lokacinsu, ƙarfinsu, da wasu abubuwa ga aikin wa’azin bishara. (Markus 13:10) Ana tallafa wa aikin wa’azi na Kiristoci na farko ta ba da kyauta. (2 Korinthiyawa 8:12; 9:7) Tertullian ya rubuta: “Ko idan ma akwai asusu, ba a karɓan kuɗi a ƙofa, sai ka ce addini batun kasuwanci ne. Kowanne mutum sau ɗaya a wata yana kawo ɗan kuɗi—ko kuma lokacin da yake so, sai dai in yana so, kuma in zai iya; domin ba a tilasa wa kowa; kyauta ce da son rai.”—Apology, babi na 39.
12 Aikin wa’azin Mulki na Shaidun Jehovah na dukan duniya ma ana tallafa masa ne da kyauta na son rai. Ban da Shaidun, mutane da suke son aikin suna ɗauka cewa gata ce su tallafa wa wannan aikin ta ba da kyautarsu. A nan ma akwai kamani tsakanin Kiristoci na farko da Shaidun Jehovah.
Gaskiya da Kuma Hali
13. Game da halinsu, wane gargaɗi na Bitrus Shaidun Jehovah suke bi?
13 Masu tafiya cikin gaskiya, Kiristoci na farko sun bi gargaɗin manzo Bitrus: “Kuna al’amura na dacewa wurin Al’ummai; domin, yayinda su ke kushenku kamar ma’aikatan mugunta, ta wurin nagargarun ayyukanku da su ke dubawa su ɗaukaka Allah cikin ranar ziyara.” (1 Bitrus 2:12) Shaidun Jehovah sun amince da wannan kalmomi.
14. Yaya Kirista yake ɗaukan nishaɗi na lalata?
14 Har ma bayan da ridda ta shigo, Kiristoci sun guje wa ayyukan lalata. W. D. Killen, farfesan tarihin addini, ya rubuta: “A ƙarni na biyu da na uku gidan wasa a kowane babban gari wajen jan hankali ne; ko da yake ’yan wasan malalata ne, wasansu na biyan bukatar sha’awar lalata na zamani ne. . . . Dukan Kiristoci na gaskiya suna ƙyamar wannan wajen. . . . Suna guje wa halin; ɗaukaka alloli da suke yi ya lalatar da tabbacinsu.” (The Ancient Church shafofi 318-319) Mabiyan Yesu na gaskiya a yau suna guje wa ayyukan ƙazanta da lalata na nishaɗi.—Afisawa 5:3-5.
Gaskiya da Kuma “Masu Mulki”
15, 16. Su wanene “masu-mulki,” kuma ta yaya waɗanda suke tafiya cikin gaskiya suke ɗaukan su?
15 Duk da nagarin halin Kiristoci na farko, yawancin daular Roma ba su fahimce su ba. Ɗan tarihi E. G. Hardy ya ce, dauloli na ɗaukan su “la’anannu masu ƙwazo.” Wasiƙu tsakanin Gwamna Pliny the Younger na Bithynia da Daula Trajan sun nuna cewa shugabanni ba su san ainihi yadda Kiristanci yake ba. Yaya Kiristoci suke ɗaukan masu mulki?
16 Kamar mabiyan Yesu na farko, Shaidun Jehovah suna biyayya mai iyaka ga gwamnatoci “masu-mulki.” (Romawa 13:1-7) Idan bukata ta mutane ta saɓa wa nufin Allah, suna tsayin daka: “Dole sai mu fi biyayya ga Allah da mutane.” (Ayukan Manzanni 5:29) Littafin nan After Jesus—The Triumph of Christianity ya ce: “Ko da Kiristoci ba sa saka hannu cikin bautar daula, ba mutane da suke ta da faɗa ba ne, amma addininsu, ko da dabam ne kuma a wani lokaci abin fushi ne ga arna, ba abin razana ba ne ga daular.”
17. (a) Kiristoci na farko sun gabatar da wace gwamnati ce? (b) Ta yaya mabiyan Kristi na gaskiya suka yi amfani da kalmomin Ishaya 2:4 a rayuwarsu?
17 Kiristoci na farko sun gabatar da Mulkin Allah, yadda ubanni Ibrahim, Ishaƙu, da Yakubu suka ba da gaskiya ga alkawarin ‘birni da Allah ya yi.’ (Ibraniyawa 11:8-10) Kamar Shugabansu, almajiran Yesu “ba na duniya ba ne.” (Yohanna 17:14-16) Game da yaƙe-yaƙe da jayayya na ’yan Adam, sun biɗi salama ta ‘bubbuga takubansu su zama garmuna.’ (Ishaya 2:4) Da ya lura da wannan kamani, mai koyar da tarihin coci Geoffrey F. Nuttall ya ce: “Halin Kiristoci na farko game da yaƙi kamar na mutane ne da ke kiran kansu Shaidun Jehovah kuma mun iske wannan gaskiya da wuya mu yarda.”
18. Me ya sa ba gwamnati da take da dalilin jin tsoron Shaidun Jehovah?
18 Mutane masu tsakatsaki masu biyayya ga “masu mulki,” Kiristoci na farko ba su kasance abin razana ba ga masu mulki, haka kuma Shaidun Jehovah. “Yana bukatar aminci a yarda cewa Shaidun Jehovah ba abin razana ba ne ga kowacce tsarin sarauta ta siyasa,” in ji edita na Amirka ta Arewa. “Ba masu zangon ƙasa ba ne kuma rukunin addini ne masu ƙaunar salama.” Masu mulki da suka fahimce su sun san ba abin da za su ji tsoronsa daga wurin Shaidun Jehovah.
19. Game da haraji, me za a ce game da Kiristoci na farko da kuma Shaidun Jehovah?
19 Hanya ɗaya da Kiristoci na farko suka daraja “masu mulki” ta biyan harajinsu ne. Da yake rubuta wa Daular Roma Antoninus Pius (138-161 A.Z.), Justin Martyr ya yarda cewa Kiristoci suna biyar harajinsu “da son rai fiye da dukan mutane.” (First Apology, babi na 17) Tertullian ya gaya wa sarakunan Roma cewa masu karɓan harajinsu ya kamata “su yi godiya ga Kiristoci” don biyar harajinsu. (Apology, babi na 42) Kiristoci sun amfana daga Salama ta Roma, dokarta da tsari, hanyoyi masu kyau, da tafiya babu haɗari a jirgin ruwa. Fahimtar hakkinsu ga jam’iyyar, sun yi biyayya ga kalmomin Yesu: “Ku ba Kaisar abin da ke na Kaisar, Allah kuma abin da ke na Allah.” (Markus 12:17) Mutanen Jehovah a yau sun bi wannan gargaɗin kuma an yaba musu don yin gaskiyarsu, game da biyar haraji.—Ibraniyawa 13:18.
Gaskiya—Gami na Haɗin Kai
20, 21. Game da ’yan’uwanci na salama, menene ya kasance gaskiya ga Kiristoci na farko da bayin Jehovah na zamani?
20 Domin suna tafiya cikin gaskiya, an haɗa Kiristoci na farko a ’yan’uwanci na salama, yadda Shaidun Jehovah suke a yau. (Ayukan Manzanni 10:34, 35) Wata wasiƙa da aka buga a jaridar The Moscow Times ta ce: “[Shaidun Jehovah] an san su da abokantaka, masu alheri, mutane masu tawali’u da suke da sauƙi a bi da su, ba sa saka wani matsi a kan mutane kuma koyaushe suna biɗan salama a dangantakarsu da wasu . . . Ba masu karɓan toshiya, mashaya ko masu shan miyagun ƙwayoyi a tsakaninsu ba, dalilin na da sauƙi: Suna ƙoƙari ra’ayi da ke bisa Littafi Mai Tsarki ya yi musu ja-gora a dukan abin da suke yi ko kuma faɗa. Idan dukan mutane a duniya aƙalla suna ƙoƙari su yi rayuwa daidai da Littafi Mai Tsarki yadda Shaidun Jehovah suke yi, muguwar duniyarmu za ta bambanta.”
21 Encyclopedia of Early Christianity ya ce: “Coci na farko ya ga kansa sabon iyali da dā mugun rukuni, Yahudawa, da na Al’umma, za su iya zama tare cikin salama.” Shaidun Jehovah ’yan’uwanci ne na salama a dukan duniya—da gaske sabuwar jam’iyya ta duniya. (Afisawa 2:11-18; 1 Bitrus 5:9; 2 Bitrus 3:13) Sa’ad da wani shugaban ’yan gadi na Filin Wasan Pretoria Show a Afirka ta Kudu ya ga yadda Shaidu daga dukan ƙabilai na masu hallara taron gunduma suka taru suna zaman lumana, ya ce: “Kowa yana da hali mai kyau, mutane da suke magana da kyau ga juna, halin da aka nuna ’yan kwanaki—ya nuna irin mutane waɗanda suke cikin jam’iyyarku, kuma duka suna zaman iyali mai farin ciki.”
Albarka don Koyar da Gaskiya
22. Me ke faruwa domin Kiristoci suna bayyanawar gaskiya?
22 Ta halinsu da aikin wa’azi, Bulus da wasu Kiristoci suna “bayyanawar gaskiya.” (2 Korinthiyawa 4:2) Ba ka yarda ba cewa Shaidun Jehovah suna yin haka kuma suna koya wa dukan al’ummai gaskiya? Mutane a dukan duniya suna karɓan bautar gaskiya kuma suna rugowa zuwa ‘dutsen gidan Jehovah’ cikin adadin da ke ci gaba da ƙaruwa. (Ishaya 2:2, 3) Kowacce shekara, dubbai suna baftisma alamar keɓe kansu ga Allah, da ke sa ana kafa sababbin ikilisiyoyi da yawa.
23. Yaya kake ɗaukan waɗanda suke koya wa dukan al’ummai gaskiya?
23 Ko da yake sun zo daga wurare dabam dabam, mutanen Jehovah suna da haɗin kai cikin bauta ta gaskiya. Ƙauna da suke nunawa ta sakankance su almajiran Yesu ne. (Yohanna 13:35) Ka gani cewa “Allah yana wurinsu”? (1 Korinthiyawa 14:25) Kana tallafa wa waɗanda suke koya wa dukan al’ummai gaskiya? Idan haka ne, ka nuna godiya na dindindin don gaskiya kuma ka samu gatar yin tafiya a cikinta har abada.
Yaya Za Ka Amsa?
• Game da bauta, wane kamani ne ke tsakanin Kiristoci na farko da kuma Shaidun Jehovah?
• Wane biki na addini ne kaɗai waɗanda suke tafiya cikin gaskiya suke yi?
• Su waye “masu-mulki,” yaya Kiristoci suke ɗaukan su?
• Ta yaya gaskiya ta zama gami na haɗin kai?
[Hoto a shafi na 15]
Taron Kirista ya kasance albarka ga waɗanda suke tafiya cikin gaskiya
[Hotuna a shafi na 17]
Yesu ya ba mabiyansa umurni su kiyaye bikin Tuna mutuwarsa ta hadaya
[Hoto a shafi na 18]
Kamar Kiristoci na farko, Shaidun Jehovah suna daraja “masu-mulki”