Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w09 12/15 pp. 4-7
  • Za Ka Iya Ƙetaro Zuwa Makidoniya?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Za Ka Iya Ƙetaro Zuwa Makidoniya?
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Ka Bincika Kanka
  • Inda Za Ka Yi Hidima
  • Fuskantar Sababbin Ƙalubale
  • Albarkar Jehobah Tana “Kawo Wadata”
  • Za Ka Iya “Ƙetaro Zuwa Makidoniya”?
    Hidimarmu Ta Mulki—2011
  • Ku Karfafa Abotarku da Jehobah Sa’ad da Kuke Hidima a Inda Ake Wani Yare
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2016
  • Za Ka Iya Taimaka wa ‘Yan’uwa a Ikilisiyarku?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2016
  • Sun Ba da Kansu da Yardar Rai
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2017
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
w09 12/15 pp. 4-7

Za Ka Iya Ƙetaro Zuwa Makidoniya?

A BIRNIN Taruwasa a Asiya Ƙarama inda jiragen ruwa suke sauka, manzo Bulus ya sami wahayi. Wani mutumin Makidoniya ya roƙe shi: “Ka ƙetaro zuwa Makidoniya, ka taimake mu.” Da Bulus ya ga wahayin, shi da abokan tafiyarsa suka kammala ‘cewa Allah ya kiraye su domin su yi bishara’ ga mutanen Makidoniya. Menene sakamakon? A babban birnin Makidoniya da ke Fillibi, Lidiya da iyalinta suka zama masu bi. Wasu a wannan lardin Romawa da ke Makidoniya sun bi su.—A. M. 16:9-15.

Ana ganin irin wannan himma tsakanin Shaidun Jehobah a yau. Da son ransu mutane da yawa sun yi amfani da dukiyarsu kuma sun ƙaura zuwa wurare da ake bukatar masu shelar Mulki sosai. Alal misali, Lisa tana son ta sa hidima farko a rayuwarta. Ta ƙaura daga Kanada zuwa Kenya. Trevor da Emily, ’yan Kanada, sun ƙaura zuwa Malawi da makasudin faɗaɗa hidimarsu. Paul da Maggie daga Ingila, sun ga cewa murabus da suka yi zarafi ne mai kyau na faɗaɗa hidimarsu ga Jehobah kuma suka ƙaura zuwa Afirka ta Gabas. Kana da halin sadaukar da kai? Za ka iya yin irin wannan ƙaurar? Idan haka ne, waɗanne ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki da kuma shawarwari ne za su taimaka maka ka yi nasara?

Ka Bincika Kanka

Wani abu da kake bukatar ka bincika shi ne muradinka. Yesu ya ce, babbar doka ita ce: “Ka yi ƙaunar Ubangiji Allahnka da dukan zuciyarka, da dukan ranka, da dukan azancinka.” Ya kamata dalilan yin hidima a wata ƙasa ya zama domin ƙaunar da ake yi wa Allah Jehobah da kuma muradin cika aikin almajirantarwa. Yesu ya ci gaba: “Wata kuma ta biyu mai-kamaninta ita ce, Ka yi ƙaunar maƙwabcinka kamar ranka.” Ana nuna ƙaunar maƙwabci a muradi na gaske na son mu taimaka. (Mat. 22:36-39; 28:19, 20) Yin hidima a ƙasar waje sau da yawa ya ƙunshi yin aiki tuƙuru da kuma halin sadaukar da kai. Ba zuwa yawon shaƙatawa ba ne. Dole ne ƙauna ce za ta motsa ka. Remco da Suzanne daga Netherland, da suke hidima yanzu a Namibia, sun taƙaita batun kamar haka, “Ƙauna ce ta sa muke nan.”

Willie, mai kula da da’ira a Namibia, ya lura cewa: “Waɗanda suke ƙasashen waje, ba sa zuwa da zaton cewa ’yan’uwa da ke yankin za su kula da su ba. Sun zo ne da ra’ayin yin hidima tare da ’yan’uwan da ke yankin, suna taimaka musu a aikin wa’azi.”

Bayan ka bincika muradinka, ka tambayi kanka: ‘Wane iyawa nake da shi da zai taimaka mini a ƙasar waje? Ni ƙwararren mai hidima ne? Waɗanne yare nake yi? Ina shirye na koyi sabon yare?’ Ka tattauna batun sosai da iyalinka. Ka tuntuɓi dattawan ikilisiyarku. Kuma ka yi addu’a ga Jehobah game da batun. Ya kamata irin wannan bincika kanka sosai ya taimaka maka ka ga ko kana da iyawa da ƙudurin yin hidima a ƙasar waje.—Duba akwatin nan “Ka San Kanka.”

Inda Za Ka Yi Hidima

An kira Bulus zuwa Makidoniya a cikin wahayi. A yau, Jehobah ba ya yi mana ja-gora ta mafificin iko. Duk da haka, ta wurin wannan jaridar da sauran littattafai, mutanen Allah suna sanin yankuna masu yawa da suke da bukata sosai. Saboda haka ka fara da rubuta sunayen waɗannan wuraren. Idan ba ka shirya koyan wani yare ba ko kuma ba za ka jima sosai ba a ƙasar waje, ka yi la’akari da yin hidima a ƙasar da ka iya yaren da yawancin mutanen da ke ƙasar suke yi. Sai ka bincika batutuwa kamar su bukatar biza, sufuri, tsaro, farashin abubuwan biya bukata, da kuma yanayi. Za ka iya samun taimako idan ka tattauna da waɗanda suka ƙaura zuwa hidima a ƙasar waje. Ka yi addu’a game da waɗannan batutuwa. Ka tuna cewa Bulus da abokan aikinsa “ruhu mai-tsarki ya hana su faɗin maganar cikin Asiya.” Ko da yake sun yi ƙoƙarin su shiga cikin Bitiniya, “ruhun Yesu ba ya yarda” su yi hakan ba. Hakazalika, zai iya ɗaukan lokaci kafin ka san inda za ka iya ba da taimako sosai.—A. M. 16:6-10.

A yanzu ya kamata ka fahimci wasu zaɓi da za ka yi. Idan kana tunanin yin hidima a ƙasar waje, ka rubuta zuwa ofishin reshe na Shaidun Jehobah a ƙasashen da kake da su a zuciya. Ka tsara irin hidimomin da ka yi a dā da wanda kake ciki yanzu a hidimar Jehobah, da kuma wasu tambayoyi da kake da su, kamar su farashin abubuwan biyan bukata, irin masauki da za ka iya samu, wuraren kiwon lafiya da ke wurin, da kuma zarafin samun aikin yi. Sai ka ba da wasiƙa ko wasiƙunka ga kwamitin hidima na ikilisiyarku. Za su haɗa da tasu wasiƙar yabo kuma su aika ta kai tsaye zuwa ofisoshin reshen da kake so. Amsarsu za ta taimaka maka ka san inda za ka fi kasance da amfani sosai.

Willie da aka yi maganarsa ɗazu ya lura cewa: “Waɗanda suka yi nasara sun ziyarci ƙasar da farko kuma suka nemi wuraren da za su fi yin farin ciki da gaske. Wasu ma’aurata sun ga cewa zama a cikin ƙauye zai yi musu wuya. Saboda haka, sun zauna a cikin ƙaramin gari inda ake bukatar masu hidima amma za su sami abubuwan zaman gari da zai sa su farin ciki.”

Fuskantar Sababbin Ƙalubale

Barin wurin da kake da zama zuwa wani sabon yanki gabaki ɗaya babu shakka zai iya kasance da ƙalubale a gare ka. “Jin cewa kai kaɗai ne matsala ce sosai,” in ji Lisa, da aka ambata ɗazu. Menene ya taimake ta? Kusantar waɗanda suke cikin ikilisiyar da ke sabon yankinta. Ta kafa makasudin koyan sunan kowa. Domin ta cim ma hakan, tana zuwa taro da wuri kuma bayan an tashi tana ɗan tsayawa domin ta yi magana da ’yan’uwa. Lisa ta yi aiki da wasu a hidima, ta gayyaci mutane da yawa zuwa gidanta, kuma ta samu sababbin abokai. Ta ce: “Ba na da na sanin sadaukarwar da na yi. Jehobah ya albarkace ni sosai.”

Bayan da suka yi renon ’ya’yansu, Paul da Maggie sun ƙaura daga cikin gidan da suka yi shekaru 30 a ciki. Ya ce: “Kawar da dukiyoyinmu yana da sauƙi. Barin iyalinmu shi ne ainihin ƙalubalen, abin ya wuce yadda muka yi zato. Mun yi kuka sosai a cikin jirgin sama. Yana da sauƙi mu yi tunani, ‘Ba za mu iya ba.’ Amma mun dogara ga Jehobah. Samun sababbin abokai yana ƙara ƙarfafa ka ka ci gaba.”

Greg da Crystal sun zaɓi su ƙaura daga Kanada zuwa Namibia domin suna yin Turanci, yaren da yawanci suke yi a ƙasar. Amma, daga baya sun ga cewa zai kasance da amfani idan suka koyi yaren yankin. “A wasu lokatai, muna yin sanyin gwiwa. Amma bayan mun koyi yaren yankin ne kawai muka fahimci al’adar. Yin tarayya kud da kud da ’yan’uwan ya taimaka mana mu saba da sabon gidanmu.”

Irin wannan hali na tawali’u da kuma yardan rai, zai iya kasancewa da tasiri mai kyau ga ’yan’uwan da ke yankin. Jenny da farin ciki ta tuna iyalin da suka ƙaura zuwa ƙasar Ireland, inda ta yi girma. “Masu karimci ne” in ji ta. “Sun zo yin hidima ne, ba don a yi musu hidima ba. Suna cike da farin ciki da kuma himma kuma hakan ne ya motsa ni na gwada hidimar.” A yanzu, Jenny tana hidima da mijinta a matsayin masu wa’azi a ƙasar waje a Gambiya.

Albarkar Jehobah Tana “Kawo Wadata”

Babu shakka Bulus ya ji daɗin hidimarsa a Makidoniya! Bayan shekara goma, ya rubuta wasiƙa zuwa ga ’yan’uwa da ke Fillibi: “Ina gode ma Allahna yayin da na ke tuna da ku duka.”—Filib. 1:3.

Trevor da Emily, waɗanda suka yi hidima a Malawi kafin aka gayyace su zuwa Makarantar Gileyad, su ma sun ji hakan. “A wasu lokatai mukan yi tunanin ko muna yin abin da ya dace, amma muna farin ciki. Mun kusaci juna kuma mun ga albarkar Jehobah.” Greg da Crystal, da aka ambata da farko, sun ba da rahoto cewa, “Babu wani abin da za mu riƙa yi da zai fi wannan.”

Hakika, ba kowa ba ne zai iya yin hidima a ƙasar waje ba. Wasu za su fi yin abin da ya fi kyau ta wajen ƙaura zuwa wani yanki da ke cikin ƙasarsu inda ake da bukata sosai. Wasu za su iya kafa makasudin yin hidima a wasu ikilisiyoyin da ke kusa da gidansu. Abin da yake da muhimmanci shi ne ka yi iyakar ƙoƙarinka ka bauta wa Jehobah. (Kol. 3:23) Da haka, hurarrun kalmomin za su kasance gaskiya a gare ka: “Albarkar Ubangiji ta kan kawo wadata, ba ya kan haɗa ta da baƙinciki ba.”—Mis. 10:22.

[Akwati/Hotunan da ke shafi na 5]

Ka San Kanka

Don ka bincika kanka ka ga ko za ka iya yin hidima a ƙasar waje, ka yi la’akari da tambayoyi na gaba kuma ka bincika kanka da gaske cikin addu’a ka ga ko za ka iya ƙaura zuwa wata ƙasa. Bayani da ke cikin fitowa na Hasumiyar Tsaro na dā zai iya taimaka maka ka yi hakan.

• Ni Mutumi ne mai ruhaniya?—“Steps Toward Happiness” (15 ga Oktoba, 1997, shafi na 6)

• Ni ƙwararren mai hidima ne?—“How to Succeed in the Pioneer Ministry” (15 ga Mayu, 1989, shafi na 21)

• Zan iya zama ba tare da iyalina da abokai na ba?—“Coping With Homesickness in God’s Service” (15 ga Mayu , 1994, shafi na 28)

• Zan iya koyan sabon yare?—“Serving With a Foreign-Language Congregation” (15 ga Maris, 2006, shafi na 17)

• Ina da kuɗin kula da kaina?—“Can You Serve in a Foreign Field?” (15 ga Oktoba, 1999, shafi na 23)

[Hotunan da ke shafi na 5]

Halin tawali’u da yardan rai za su iya kasance da tasiri mai kyau ga ’yan’uwa da ke yankin

[Hotunan da ke shafi na 7]

Waɗanda suka zo yin hidima da gaske sune ke yin nasara

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba