WAƘA TA 49
Mu Riƙa Faranta Ran Jehobah
Hoto
	(Misalai 27:11)
- 1. Uba, mun yi alkawari, - Alkawarin bauta maka. - Muna so mu yi biyayya - Domin mu faranta ranka. 
- 2. Wakilinka a duniya - Yana yin shelar girmanka, - Yana ciyar da mu sosai - Don mu riƙa yin nufinka. 
- 3. Ka ba mu ruhunka, Allah, - Domin mu riƙe aminci. - Hakan zai sa mu yabe ka - Kuma mu faranta ranka. 
(Ka kuma duba Mat. 24:45-47; Luk. 11:13; 22:42.)