Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • lr babi na 9 pp. 52-56
  • Muna Bukatar Mu Tsayayya Wa Jarraba

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Muna Bukatar Mu Tsayayya Wa Jarraba
  • Ka Koya Daga Wurin Babban Malami
  • Makamantan Littattafai
  • Shaidan Ya Jarraba Yesu
    Darussa daga Littafi Mai Tsarki
  • “Ku Yi Tsayayya Da Shaiɗan” Yadda Yesu Ya Yi
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
  • Wane Irin Mutum Ne Ya Kamata Ka Zama
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
  • Ka Yi Hattara, Shaidan Yana So Ka Bijire!
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2015
Dubi Ƙari
Ka Koya Daga Wurin Babban Malami
lr babi na 9 pp. 52-56

BABI NA 9

Muna Bukatar Mu Tsayayya Wa Jaraba

AKWAI wanda ya taɓa gaya maka ka yi abin da ba shi da kyau?— Ya ce maka idan ka isa ka yi mana? Ko kuma dai ya ce ne yana da daɗi kuma ba laifi ba ne idan ka yi?— Idan wani ya yi mana haka, yana ƙoƙari ya jarabe mu ne.

Menene ya kamata mu yi idan aka jarabe mu? Ya kamata ne mu faɗa ciki mu yi abin da yake mugu?— Wannan ba zai faranta wa Jehovah Allah rai ba. Amma ka san wanda zai yi farin ciki?— Shaiɗan Iblis ne zai yi farin ciki.

Shaiɗan abokin gaban Allah ne, kuma Shaiɗan abokin gabanmu ne. Ba za mu iya ganinsa ba domin ruhu ne. Amma yana iya ganinmu. Wata rana Iblis ya yi magana da Yesu, Babban Malami, kuma ya yi ƙoƙari ya jarabe shi. Bari mu ga abin da Yesu ya yi. Da haka za mu san abin da ya dace mu yi sa’ad da aka jarabe mu.

Bayan an yi wa Yesu baftisma, ya kalli sama kuma ya yi addu’a

Menene Yesu wataƙila ya fara tunawa sa’ad da aka yi masa baftisma?

Yesu ko da yaushe yana so ya yi nufin Allah. Ya nuna haka a fili wajen yin baftisma a cikin Kogin Urdun. Bayan da Yesu ya yi baftisma ne Shaiɗan ya yi ƙoƙari ya jarabe shi. Littafi Mai Tsarki ya ce “sammai suka buɗe” wa Yesu. (Matta 3:16) Wannan zai iya nufin cewa Yesu ya fara tuna dukan rayuwarsa ta farko a sama tare da Allah.

Bayan baftismarsa Yesu ya je cikin daji ya yi tunani a kan abubuwa da ya tuna. Kwanaki arba’in da dare arba’in suka shige. A dukan wannan lokacin Yesu bai ci kome ba, saboda haka a lokacin yana jin yunwa sosai. A wannan lokacin ne, Shaiɗan ya yi ƙoƙarin ya jarabi Yesu.

Iblis ya yi amfani da duwatsu ya jarraba Yesu

Ta yaya Iblis ya yi amfani da duwatsu ya jarabi Yesu?

Iblis ya ce: “Idan kai Ɗan Allah ne, ka umurci waɗannan duwatsu su zama gurasa.” Wasu gurasa suna da daɗi ƙwarai! Amma da Yesu zai iya juya duwatsu su zama gurasa?— E, zai iya. Me ya sa? Domin Yesu, Ɗan Allah yana da iko na musamman.

Da za ka mai da dutse ya zama gurasa idan Iblis ya umurce ka ka yi haka?— Yesu yana jin yunwa. Da ba daidai ba ne ya yi shi sau ɗaya kawai?— Yesu ya sani ba daidai ba ne ya yi amfani da ikonsa a wannan hanyar. Jehovah ya ba shi wannan ikon ya jawo mutane ne ga Allah, ba don ya yi amfani da shi ba domin kansa.

To, maimakon haka, Yesu ya gaya wa Shaiɗan abin da yake rubuce a cikin Littafi Mai Tsarki: “Ba da abinci kaɗai ba mutum za ya rayu, amma da kowacce magana da ke fitowa daga bakin Allah.” Yesu ya sani cewa yin abin da zai faranta wa Jehovah rai ya fi samun abinci muhimmanci.

Amma Iblis ya sake ƙoƙari. Ya kai Yesu cikin Urushalima kuma ya sa ya tsaya a gefen haikali da yake da tsawo. Sai Shaiɗan ya ce: ‘Idan kai Ɗan Allah ne, faɗa da kanka: gama an rubuta, mala’ikun Allah za su sa ba za ka ji rauni ba.’

Me ya sa Shaiɗan ya faɗi haka?— Ya faɗa ne domin ya jarabi Yesu ya yi aikin wauta. Amma Yesu bai saurari Shaiɗan ba. Ya gaya wa Shaiɗan: “An kuma rubuta, Ba za ka gwada Ubangiji Allahnka ba.” Yesu ya sani cewa ba daidai ba ne ya gwada Jehovah ta wajen saka ransa cikin haɗari.

Duk da haka Shaiɗan bai gaji ba. Sai ya ɗauki Yesu zuwa wani dutse mai tsawo. A nan ya nuna masa dukan mulkoki, ko kuma gwamnatoci, na duniya da kuma darajarsu. Sai Shaiɗan ya ce wa Yesu: “Dukan waɗannan ni ba ka, idan ka fāɗi, ka yi mini sujjada.”

Ka yi tunanin abin da Iblis ya bayar. Shin dukan waɗannan mulkoki, ko kuma gwamnatocin mutane, da gaske na Shaiɗan ne?— Yesu bai yi jayayya cewa na Shaiɗan ne ba. Da ya yi jayayya da Shaiɗan zai zama ba shi ne mai su ba. Hakika, Shaiɗan da gaske shi ne mai mallakar dukan al’ummai na duniya. Littafi Mai Tsarki ya kira shi “mai-mulkin wannan duniya.”—Yohanna 12:31.

Yesu ya ki amincewa da abin da Shaidan ya ce zai ba shi, wato dukan duniyar nan

Me ya sa Shaiɗan ya iya miƙa wa Yesu dukan waɗannan mulkoki?

Menene za ka yi idan Iblis ya yi maka alkawarin wani abu don ka bauta masa?— Yesu ya sani cewa ba daidai ba ne a bauta wa Shaiɗan ko da menene zai ba Shi. Saboda haka Yesu ya ce: ‘Ka tafi daga nan, Shaiɗan! Domin Littafi Mai Tsarki ya ce Jehovah Allahnka ne kaɗai za ka bauta’ wa.—Matta 4:1-10; Luka 4:1-13.

Wata yarinya tana kallon abincin da aka ajiye kamar ta ci

Menene za ka yi idan aka jarabe ka?

Mu ma muna fuskantar jaraba. Ka san wasu daga cikinsu?— Ga wani misali a nan. Mamarka wataƙila ta yi alkaki ko nakiya. Wataƙila ta ce maka kada ka ci har sai lokacin ci ya yi. Amma kuma kana jin yunwa, ka jarabu ka ci. Ka yi wa mamarka biyayya ke nan?— Shaiɗan yana so ka yi mata rashin biyayya.

Ka tuna da Yesu. Shi ma yana jin yunwa sosai. Amma ya sani cewa faranta wa Allah rai ya fi cin abinci muhimmanci. Za ka nuna kana kama da Yesu sa’ad da ka bi abin da mamarka ta ce.

Wataƙila wasu yara za su ce ka sha ƙwaya. Za su ce maka za ta sa ka ji daɗi. Za ta iya kasancewa muguwar ƙwaya. Za su sa ka rashin lafiya ko ma su kashe ka. Ko kuma wasu su ba ka taba, wanda ya ƙunshi ƙwayoyi, kuma su ce, idan ka isa ka sha. Me za ka yi?—

Wani yaro ya ba wasu yara sigari; daya ya karba, dayan ya ki karba kuma ya bar wurin

Ka tuna da Yesu. Shaiɗan ya yi ƙoƙarin ya sa Yesu ya saka ransa cikin haɗari, ya gaya masa ya yi tsalle daga saman haikali. Amma Yesu bai yi haka ba. Me za ka yi idan wani ya ce ka yi mugun abu idan ka isa?— Yesu bai saurari Shaiɗan ba. Bai kamata ka saurari wanda yake so ya saka ka yin mugun abu ba.

Wata yarinya ta rike sifar giciye

Me ya sa bai dace a yi amfani da sifoffi wajen bauta ba?

Za a iya cewa ka yi sujjada ga gunki, abin da Littafi Mai Tsarki ya ce kada mu yi. (Fitowa 20:4, 5) Wataƙila a biki ne a makaranta. Za a iya ce maka idan ka ƙi ba za ka sake zuwa makaranta ba. Me za ka yi?—

Yana da sauƙi mu yi abin da yake da kyau idan wani yana yin haka. Amma zai yi wuya idan wasu suna so mu yi abin da yake mugu. Za su ce abin da suke yi ba shi da laifi sosai. Amma babbar tambaya ita ce, Menene Allah ya ce game da shi? Shi ya fi mu sani.

Saboda haka, ko menene wasu suka ce, kada mu yi abubuwa da Allah ya ce ba su da kyau. A wannan hanyar za mu riƙa faranta wa Allah rai kullum, kuma ba za mu taɓa faranta wa Iblis rai ba.

Za ka samu ƙarin bayani game da yadda za ka tsayayya wa jarabar yin abin da yake mugu a Zabura 1:1, 2; Misalai 1:10, 11; Matta 26:41 da kuma 2 Timothawus 2:22.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba