Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • lfb darasi na 75 p. 178-p. 179 par. 4
  • Shaidan Ya Jarraba Yesu

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Shaidan Ya Jarraba Yesu
  • Darussa daga Littafi Mai Tsarki
  • Makamantan Littattafai
  • Muna Bukatar Mu Tsayayya Wa Jarraba
    Ka Koya Daga Wurin Babban Malami
  • “Ku Yi Tsayayya Da Shaiɗan” Yadda Yesu Ya Yi
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
  • Ka Yi Tsayayya Da Shaiɗan, Kuma Zai Guje ka!
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2006
  • Amsoshin Tambayoyi Daga Littafi Mai Tsarki
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
Dubi Ƙari
Darussa daga Littafi Mai Tsarki
lfb darasi na 75 p. 178-p. 179 par. 4
Yesu ya ki ya jefa kansa daga saman haikali

DARASI NA 75

Shaiɗan Ya Jarraba Yesu

Yesu ya ki ya mai da dutse zuwa burodi

Bayan da Yesu ya yi baftisma, sai ruhu mai tsarki ya bishe shi zuwa cikin jeji. Yesu ya ji yunwa sosai domin ya yi azumi na kwana 40. Bayan haka, sai Shaiɗan ya zo ya jarraba Yesu kuma ya ce: ‘Idan da gaske kai Ɗan Allah ne, ka juya dutsen nan zuwa burodi.’ Amma Yesu ya faɗi abin da Nassosi suka ce: ‘An rubuta cewa ba abinci ne kaɗai zai sa mu rayu ba. Amma ya kamata mu yi biyayya ga umurnin Jehobah.’

Bayan haka, sai Shaiɗan ya ce wa Yesu: ‘Idan kai Ɗan Allah ne, ka faɗo daga saman haikalin. Domin an rubuta cewa Allah zai aiko da mala’ikunsa su riƙe ka.’ Amma Yesu ya sake faɗin abin da ke cikin Nassosi: ‘An rubuta cewa kada mu gwada Jehobah.’

Yesu ya ki ya karbi mulkokin duniya da Shaidan ya ce zai ba shi

Sai Shaiɗan ya sake nuna wa Yesu dukan mulkokin duniya da ɗaukakarsu da kuma wadatarsu. Ya ce: ‘Zan ba ka duka waɗannan mulkokin da kuma ɗaukakarsu idan ka bauta mini sau ɗaya kawai.’ Sai Yesu ya ce masa: ‘Ka rabu da ni Shaiɗan! Domin an rubuta cewa ya kamata mu bauta wa Jehobah kaɗai.’

Sai Shaiɗan ya rabu da shi kuma mala’iku suka zo suka ba Yesu abinci. Daga lokacin, sai Yesu ya soma yin wa’azin Mulkin Allah. Wannan shi ne aikin da aka aiko shi ya yi a duniya. Mutane sun so koyarwa Yesu kuma suna bin sa duk inda ya je.

“Sa’ad da [Shaiɗan] yake yin ƙarya, don kansa yake yi: gama maƙaryaci ne shi, da uban ƙarya kuma.”​—Yohanna 8:44

Tambayoyi: Waɗanne Jarrabawa uku ne Shaiɗan ya yi wa Yesu? Ta yaya Yesu ya amsa masa?

Matta 4:​1-11; Markus 1:​12, 13; Luka 4:​1-15; Kubawar Shari’a 6:​13, 16; 8:3; Yaƙub 4:7

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba