Maganar Jehobah Rayayyiya Ce
Darussa Daga Littafin Tarihi na Ɗaya
SHEKARU 77 sun wuce tun sa’ad da Yahudawa suka dawo ƙasarsu daga zaman bauta a Babila. Haikalin da Gwamna Zarubabel ya gina ya kai shekara 55. Ainihin dalilin dawowar Yahudawa shi ne domin su maido da bauta ta gaskiya a Urushalima. Amma, mutanen sun ƙi su nuna himma a bautar Jehobah. Suna bukatar ƙarfafa da gaggawa, kuma wannan shi ne abin da littafin Tarihi na Ɗaya na Littafi Mai Tsarki ya yi tanadinsa.
Ban da labaran tsararraki, Littafin Tarihi na Ɗaya ya ɗauki shekaru 40, daga mutuwar Sarki Saul zuwa mutuwar Dauda. Firist Ezra ne ya rubuta wannan littafin a shekara ta 460 K.Z. Littafin Tarihi na Ɗaya na da muhimmanci a gare mu domin ya ba da haske game da bauta a cikin haikali kuma ya ba da bayani dalla-dalla game da zuriyar Almasihu. Domin yana cikin hurarriyar Kalmar Allah, saƙonsa na ƙarfafa bangaskiyarmu kuma zai faɗaɗa fahimtarmu ta Littafi Mai Tsarki.—Ibraniyawa 4:12.
JERIN SUNAYE MAI MUHIMMANCI
(1 Tarihi 1:1–9:44)
Jerin tsararraki da Ezra ya rubuta yana da muhimmanci aƙalla domin dalilai uku: domin a tabbata cewa waɗanda suka cancanta ne kawai za su yi hidimar firist, don a gane gadōn kowane harshe, da kuma kāre sunan zuriyar da Almasihu zai fito. Tarihin ya ambata asalin Yahudawan har zuwa lokacin mutum na farko. Zuriya goma daga Adamu zuwa Nuhu, kuma wata zuriya goma daga Nuhu zuwa Ibrahim. Bayan ya gama lissafa ’ya’yan Isma’ilu, ’ya’yan ƙwarƙwarar Ibrahim, Ketura, da kuma ’ya’yan Isuwa, labarin ya mai da hankali ne a kan ’ya’ya 12 na Isra’ila.—1 Tarihi 2:1.
An tattauna sosai a kan zuriyar Yahuda domin ta wurin ta aka sami zuriyar Sarki Dauda. Zuriya 14 ne daga Ibrahim zuwa Dauda, kuma zuriya 14 ne daga Dauda zuwa lokacin da aka kai su bauta a Babila. (1 Tarihi 1:27, 34; 2:1-15; 3:1-17; Matiyu 1:17) Bayan haka, Ezra ya jera sunayen zuriyar ƙabilun da ke gabashin Urdun, daga nan kuma sai zuriyar Lawi. (1 Tarihi 5:1-24; 6:1) Bayan haka, ya ambata wasu ƙabilu da suke yammacin Kogin Urdun da kuma zuriyar Biliyaminu. (1 Tarihi 8:1) Ya kuma ambata sunayen waɗanda suka fara zama a Urushalima bayan sun dawo daga bauta a Babila.—1 Tarihi 9:1-16.
Tambayoyin Nassi da aka Amsa:
1:18—Wanene uban Shela, Kenan ne ko Arfakshad? (Luka 3:35, 36) Arfakshad shi ne uban Shela. (Farawa 10:24; 11:12) Kalmar nan “Kenan” da ke Luka 3:36 wataƙila kure ne, maimakon kalmar nan “Kaldiya.” Idan haka ne, to, furci na asali zai kasance, “ɗan Kaldiya Arfakshad.” Ko kuma wataƙila sunayen nan Kenan da Arfakshad sunan mutum ɗaya ne. Kuma gaskiyar da ba za a manta da ita ba ita ce, kalmar nan “ɗan Kenan” ba ta cikin wasu rubutun hannu.—Luka 3:36.
2:15—Dauda ne ɗan Yesse na bakwai? A’a. Yesse yana da ’ya’ya takwas, kuma Dauda ne ɗan auta. (1 Sama’ila 16:10, 11; 17:12) Ɗaya a cikin ’ya’yan Yesse ya mutu ba shi da ’ya’ya. Tun da yake ba zai yi wani tasiri ba a wajen rubuta sunayen zuriya, Ezra bai rubuta sunansa ba.
3:17—Me ya sa Luka 3:27 ta kira ɗan Yekoniya, Sheyaltiyel ɗan Niri? Yekoniya shi ne uban Sheyaltiyel. Amma, Niri ya aura wa Sheyaltiyel ’yarsa. Luka ya kira surukin Niri, ɗan Niri kamar yadda ya kira Yusufu ɗan Heli, wanda shi ne mahaifin Maryamu.—Luka 3:23.
3:17-19—Ta yaya ne Zarubabel, Fedaiya, da kuma Sheyaltiyel suka zama dangin juna? Zarubabel ɗan Fedaiya ne, ɗan’uwan Sheyaltiyel. Duk da haka, a wasu lokatai Littafi Mai Tsarki na kiran Zarubabel ɗan Sheyaltiyel. (Matiyu 1:12; Luka 3:27) Wataƙila wannan ya kasance haka ne domin Fedaiya ya mutu, kuma Sheyaltiyel ne ya rāine Zarubabel. Ko kuwa wataƙila da yake Sheyaltiyel ya mutu bai haihu ba, Fedaiya ya auri matar Sheyaltiyel, kuma suka haifi Zarubabel.—Maimaitawar Shari’a 25:5-10.
5:1, 2—Menene karɓan gadōn ɗan fari ke nufi ga Yusufu? Hakan na nufin cewa Yusufu ya sami kashi biyu na gadōn. (Maimaitawar Shari’a 21:17) Da haka, ya zama uban ƙabilai biyu, wato, Ifraimu, da Manassa. Sauran ’ya’yan Isra’ila sun haifi ƙabila ɗaiɗai.
Darussa Dominmu:
1:1-9:44. Sunayen zuriyoyin nan sun nuna cewa tsarin bauta ta gaskiya ya dangana ne a kan gaskiya ba ƙage ba.
4:9, 10. Jehobah ya amsa addu’ar da Yabez ya yi ta faɗaɗa iyakar yankinsa cikin salama domin ta ɗauki ƙarin mutane masu tsoron Allah. Muna bukatar mu yi addu’a sosai domin mu sami ƙaruwa yayin da muke saka hannu da himma a aikin almajirantarwa.
5:10, 18-22. A kwanakin Sarki Saul, ƙabilun da suke gabashin Urdun sun ci Hagarawa a yaƙi duk da yake cewa Hagarawan sun ninka su sau biyu a yawa. Hakan ya faru ne domin jaruman waɗannan ƙabilun sun dogara ga Jehobah kuma sun nemi taimakonsa. Bari mu dogara ga Jehobah yayin da muke ci gaba da yaƙi na ruhaniya da maƙiyanmu da suka fi mu yawa.—Afisawa 6:10-17.
9:26, 27. Lawiyawa masu tsare kofa suna da matsayi na riƙon amana. An ba su maƙullin buɗe hanyar wuri mai tsarki na haikalin. Sune suke buɗe ta kowace rana. An ba mu hakkin nemo mutane a yankinmu kuma mu taimake su su zo su bauta wa Jehobah. Bai kamata a dogara kuma a amince da mu kamar yadda aka amince da Lawiyawa masu tsare kofa ba?
DAUDA YANA SARAUTA
(1 Tarihi 10:1–29:30)
Labarin ya soma ne da Sarki Saul da ’ya’yansa uku da suka mutu a yaƙin da suka yi da Filistiyawa a Dutsen Gilbowa. An naɗa Dauda, ɗan Yesse, sarki bisa ƙabilar Yahuza. Jim kaɗan bayan haka, ya ci Urushalima a yaƙi. Mayaƙa daga dukan ƙabilun suka zo Hebron suka naɗa shi sarki bisa dukan Isra’ila. (1 Tarihi 12:38) Bayan haka, Isra’ilawa suka ɗauki akwatin alkawari zuwa Urushalima “suna ta sowa, suna ta busa ƙaho, suna kaɗa kuge da molaye, da garayu.”—1 Tarihi 15:28.
Dauda ya furta muradin gina wa Allah na gaskiya gida. Jehobah ya ba Sulemanu gatar yin haka, amma ya yi wa Dauda alkawarin Mulki. Yayin da Dauda ke ci gaba da yin yaƙi da maƙiyan Isra’ila, Jehobah ya ci gaba da ba shi nasara bisa nasara. Ƙidayar da aka yi ta kai ga mutuwar mutane 70,000. Bayan mala’ika ya umurce shi ya gina wa Jehobah bagade, Dauda ya sayi masussuka daga Arauna Bayebushe. Dauda ya soma “tara kayayyakin gini masu ɗumbun yawa” domin gina wa Jehobah gida “mai ƙayatarwa” a wannan filin. (1 Tarihi 22:5) Dauda ya tsara hidimar Lawiyawa, da aka kwatanta a cikin wannan littafin fiye da ko’ina a cikin Nassosi. Sarki da mutanen sun ba da gudummawa mai yawa don gina haikalin. Bayan ya yi sarauta na shekara 40, Dauda “ya rasu da kyakkyawan tsufa, cike da shekaru, da arziki, da daraja. Ɗansa Sulemanu kuma ya gāji sarautarsa.”—1 Tarihi 29:28.
Tambayoyin Nassi da aka Amsa:
11:11—Me ya sa adadin mutane 300 da aka kashe bai yi daidai da 800 na wannan labarin da ke cikin Sama’ila na biyu 23:8 ba? Yashobeyam ko Yosheb-basshebet shi ne Shugaba tsakanin manyan jaruman Dauda uku. Sauran jaruman su ne, Ele’azara da Shamma. (2 Sama’ila 23:8-11) Dalilin da ya sa aka sami bambanci shi ne, wataƙila labaran suna magana ne a kan abubuwa dabam dabam da mutumin ya yi.
11:20, 21—Menene matsayin Abishai a tsakanin jaruman nan uku na Dauda? Abishai ba ya cikin jaruman nan uku da suka yi wa Dauda hidima. Amma, kamar yadda aka ambata a 2 Sama’ila 23:18, 19, ya shugabanci mayaƙa 30 kuma ya fi dukansu shahara. Sunan da Abishai ya yi, ya kusan yin daidai da na manyan jaruman nan uku domin manyan ayyukan da ya yi sun kusa yin daidai da na Yashobeyam.
12:8—A wace hanya ce fuskokin jaruman ƙabilar Gad “kamar na zakoki”? Waɗannan gwarzayen mutanen sun ba wa Dauda goyon baya a cikin jeji. Gashinsu ya yi tsawo sosai. Da yake suna da gashi mai yawa a kai, kamaninsu ya kasance da ban tsoro kamar na zaki.
13:5—Menene “rafin Masar”? (L.M.T) Wasu sun yi tunanin cewa wannan furcin na nufin wani ɓangare na Kogin Nilu. Amma, an fahimci cewa “rafin Masar,” na nuni ne ga wani ƙwari mai kwazazzabo wanda shi ke kan iyakan kudu maso yamma da Ƙasar Alkawari.—Littafin Ƙidaya 34:2, 5; Farawa 15:18.
16:30—Menene ma’anar “rawar jiki” domin Jehobah? An yi amfani da furcin nan “rawar jiki” a alamance yana nufin jin tsoro da kuma ɗaukaka Jehobah.
16:1, 37-40; 21:29, 30; 22:19—Wane tsari na bauta ne ya ci gaba a Isra’ila daga lokacin da aka kawo Akwatin alkawari zuwa Urushalima har zuwa lokacin da aka gina haikali? Sa’ad da Dauda ya kawo Akwatin zuwa Urushalima kuma ya saka shi a alfarwar da ya kafa, an yi shekaru da yawa ba a saka Akwatin cikin mazauni ba. Bayan an kawo Akwatin, an ajiye shi a cikin alfarwa a Urushalima. Mazaunin yana Gibeyon, inda Babban Firist, Zadok da ’yan’uwansa suke yin hadayu yadda aka kwatanta a cikin Doka. An ci gaba da wannan tsarin har sa’ad da aka kammala ginin haikalin da ke Urushalima. Sa’ad da aka kammala haikalin, an ɗauko mazaunin daga Gibeyon zuwa Urushalima, kuma an ajiye Akwatin a cikin Wuri Mafi Tsarki na haikali.—1 Sarakuna 8:4, 6.
Darussa Dominmu:
13:11. Maimakon mu yi fushi kuma mu ɗora wa Jehobah laifi sa’ad da ƙoƙarce-ƙoƙarcenmu suka kasa, dole ne mu bincika yanayi kuma mu yi ƙoƙarin gano abin da ya jawo kasawar. Babu shakka, Dauda ya yi haka. Ya koya daga kuskuren da ya yi, kuma bayan haka, ya kawo Akwatin zuwa Urushalima ta yin amfani da hanyar da ta dace.a
14:10, 13-16; 22:17-19. Ya kamata a kowane lokaci mu yi addu’a ga Jehobah kuma mu nemi ja-gorarsa kafin mu yi abin da zai shafe mu a ruhaniya.
16:23-29. Dole ne bautar Jehobah ta zama aba ta farko a rayuwarmu.
18:3. Jehobah Mai Cika alkawari ne. Ta wurin Dauda, ya cika alkawarinsa na bai wa zuriyar Ibrahim duka ƙasar Ka’ana, “daga Kogin Masar zuwa babban kogi, wato Kogin Yufiretis ke nan.”—Farawa 15:18; 1 Tarihi 13:5.
21:13-15. Jehobah ya umurci mala’ikan ya dakatar da annobar domin ba ya son ya ga mutanensa suna wahala. Hakika, “shi mai yawan jinƙai ne.”b
22:5, 9; 29:3-5, 14-16. Ko da yake ba a umurce shi ya gina wa Jehobah haikali ba, Dauda ya nuna shi mai karimci ne. Me ya sa? Domin ya fahimci cewa dukan abin da ya tara, domin albarkar Jehobah ce. Irin wannan halin ya kamata ya motsa mu mu kasance da karimci.
24:7-18. Shirin ƙungiyoyin firistoci 24 da Dauda ya kafa ya soma aiki sa’ad da mala’ikan Jehobah ya bayyana ga Zakariya, baban Yahaya mai Baftisma, kuma ya sanar da shi haihuwar Yahaya. Tun da yana cikin “ƙungiyar Abaija,” Zakariya a lokacin yana hidima tasa a haikali. (Luka 1:5, 8, 9) Bauta ta gaskiya tana da dangantaka da mutane na tarihi, ba na ƙage ba. Za mu sami albarka idan muka ba da haɗin kai cikin aminci ga “amintaccen bawan nan mai hikima” game da tsari mai kyau na bautar Jehobah a yau.—Matiyu 24:45.
Ka Bauta wa Jehobah da “Yardar Rai”
Littafin Tarihi na Ɗaya ba labari ba ne kawai na zuriya. Amma, labari ne kuma na akwatin alkwarin da Dauda ya kawo Urushalima, da manyan nasarorin da ya yi, game da shirin gina haikali, da kuma kafa tsarin hidima na firistoci Lawiyawa. Duka abin da Ezra ya faɗa a Littafin Tarihi na Ɗaya ya amfane Isra’ilawa, wanda hakan ya taimaka musu suka sabonta himmarsu ga bautar Jehobah a haikali.
Dauda ya kafa misali mai kyau ta wajen saka bautar Jehobah aba ta farko a rayuwarsa! Maimakon neman wa kansa matsayi, Dauda ya biɗi yin nufin Allah. An ƙarfafa mu mu yi amfani da shawararsa mu bauta wa Jehobah da “zuciya ɗaya, da kuma yardar rai.”—1 Tarihi 28:9.
[Hasiya]
a Don ƙarin darussa daga ƙoƙarin da Dauda ya yi na kawo Akwatin zuwa Urushalima, ka dubi Hasumiyar Tsaro, 1 ga Yuni, 2005, shafuffuka na 28-31.
b Domin ƙarin bayani game da ƙidayar da bai dace ba da Dauda ya yi, ka dubi Hasumiyar Tsaro, 1 ga Yuni, 2005, shafuffuka na 28-31.
[Chart/Hotuna a shafuffuka na 28-31]
4026 K.Z. Adamu Daga Adamu zuwa
Nuhu (shekaru 1,056)
Shekaru 130 ⇩
Shitu
105 ⇩
Enosh
90 ⇩
Kenan
70 ⇩
Mahalalel
65 ⇩
Yared
162 ⇩
Anuhu
65 ⇩
Metusela
187 ⇩
Lamek
182 ⇩
2970 K.Z. Nuhu 2970 K.Z. An haifi NUHU
Daga Nuhu zuwa Ibrahim
Shekaru 502 ⇩ (shekara 952)
Shitu
RIGYAWA shekara ta 2370 K.Z.
100 ⇩
Arfakshad
Arpakeshadi
35 ⇩
Shela
30 ⇩
Eber
34 ⇩
Feleg
30 ⇩
Reyu
32 ⇩
Serug
30 ⇩
Nahor
29 ⇩
Tera
130 ⇩
2018 K.Z. Ibrahim An haifi IBRAHIM
Daga Ibrahim zuwa Dauda:
⇩ tsararraki 14 (shekara 911)
Ishaku
60 ⇩
Yakubu
c.88 ⇩
Yahuda
⇩
Feresa
⇩
Hesruna
⇩
Arama
⇩
Amminadab
⇩
Nashon
⇩
Salmon
⇩
Bo’aza
⇩
Obida
⇩
Yesse
1107 K.Z. An haifi DAUDA