Ku Tsaya Shuru Ku Ga Ceton Jehovah!
“Ku yi shiri, ku tsaya shuru, ku ga ceton Ubangiji a wurinku.”—2 Labarbaru 20:17.
1, 2. Me ya sa farmakin “Gog na ƙasar Magog” yake da mummunar sakamako fiye da razanar ta’addanci na ƙasashe?
WASU sun kwatanta ta’addanci cewa farmaki ne bisa jama’a, har ma bisa wayewar kai. Abin da ya sa ke nan ya dace a mai da wa wannan razanar hankali. A wata sassa kuma, da akwai wani farmaki da ya fi wannan da jama’ar duniya ba su mai da wa hankali ba. Me ke nan?
2 Farmakin da “Gog na ƙasar Magog” zai yi ne da Littafi Mai Tsarki ya yi zancensa a Ezekiel sura ta 38. Zugugu ne a ce wannan farmakin yana da mummunar sakamako fiye da razanar ta’addanci na ƙasashe? Sam, domin farmakin Gog ba a kan gwamnatin mutane ba kawai. Ya yi wa gwamnatin Allah na samaniya farmaki! Amma, Mahalicci yana da ikon ya bi da mugun farmaki na Gog ɗin nan, ba kamar mutane ba da ba su da cikakken iya jure wa farmaki a zamaninsu ba.
Farmaki a Kan Gwamnatin Allah
3. Menene aka gayyaci masarautan duniya su yi tun shekara ta 1914, kuma yaya suka amsa?
3 Faɗace-faɗace tsakanin Sarkin Allah na yanzu da mugun zamanin Shaiɗan ya ci gaba tun lokacin da aka kafa Mulkin Allah a sammai a shekara ta 1914. A lokacin, aka sanar da masarauta na mutane su yi biyayya ga Masarauci da Allah ya zaɓa. Amma sun ƙi su yi haka, yadda aka annabta: “Sarakunan duniya sun tashi tsaye, mahukunta kuma suna ƙulla shawara gāba da Ubangiji da Masihansa, suna cewa, bari mu tsuntsunki maruruwansu, mu yarda ƙanginsu daga garemu.” (Zabura 2:1-3) Tsayayya wa Mulkin zai kai ƙarshensa a lokacin farmakin Gog na Magog.
4, 5. Ta yaya mutane za su iya yin yaƙi da gwamnatin Allah marar ganuwa a samaniya?
4 Za mu iya mamaki yadda mutane za su iya faɗa gāba da gwamnati ta samaniya marar ganuwa. Wannan gwamnatin, Littafi Mai Tsarki ya yi bayani cewa su “zambar ɗari da zambar arba’in da huɗu, watau waɗanda aka fanshe su daga cikin duniya,” tare da “Ɗan ragon,” Kristi Yesu. (Ru’ya ta Yohanna 14:1, 3; Yohanna 1:29) Domin a sama take, an kira sabuwar gwamnatin “sababbin sammai,” daidai kuma aka kira talakawanta a duniya “sabuwar duniya.” (Ishaya 65:17; 2 Bitrus 3:13) Yawancin abokan sarauta da Kristi 144,000 sun riga sun gama aikinsu a duniya da aminci. Saboda haka, sun tabbatar da cancantarsu su karɓi sabon aiki na hidima a sama.
5 Amma, har ila raguwar 144,000 suna duniya. Fiye da 15,000,000 da suka halarci bikin Jibin Maraice na Ubangiji a shekara ta 2002, waɗanda suka nuna an zaɓe su domin aiki a samaniya guda 8,760 ne kawai. Duk wanda ya yi wa waɗannan raguwar da suke na Mulkin farmaki, lallai yana gāba ne da Mulkin Allah.—Ru’ya ta Yohanna 12:17.
Sarkin Yana Yin Nasara
6. Yaya Jehovah da Kristi suke ɗaukan hamayya da ake yi wa mutanen Allah?
6 An faɗa yadda Jehovah ya ji game da hamayya a kan Mulkinsa da aka kafa: “Mai-zama a cikin sammai za shi yi dariya: Ubangiji za ya yi musu ganin raini. Sa’annan za shi yi musu magana cikin fushinsa, za shi wahalda su cikin zafin haushinsa. Duk da haka na kafa sarkina a bisa dutsena mai-tsarki Sihiyona.” (Zabura 2:4-6) Yanzu lokaci ya kai da Kristi ta wurin ja-gorar Jehovah ya fito garin “yin nasara.” (Ru’ya ta Yohanna 6:2) Yaya Jehovah yake ɗaukan hamayya da ake yi wa mutanensa a lokacin yaƙi na ƙarshe? Yana ɗauka ana yi masa ne da kuma Sarkinsa mai sarauta. ‘Shi wanda ya taɓa ku, ya taɓa ƙwayar idona,’ in ji Jehovah. (Zechariah 2:8) Yesu kuma ya nanata sosai cewa abin da mutane suka yi ko kuma suka ƙi yi wa ’yan’uwansa shafaffu an yi masa ne.—Matta 25:40, 45.
7. Domin waɗanne dalilai ne waɗanda suke na “taro mai-girma,” da aka kwatanta a Ru’ya ta Yohanna 7:9, suke fuskantar fushin Gog?
7 Hakika waɗanda suke goyon bayan raguwar shafaffu sosai haka su ma za su fuskanci fushin Gog. Waɗannan da za su kasance cikin “sabuwar duniya” na Allah “taro mai-girma” ne “daga cikin kowane iri, da dukan ƙabilai da al’ummai da harsuna.” (Ru’ya ta Yohanna 7:9) An ce suna “tsaye gaban kursiyin da gaban Ɗan ragon, suna yafe da fararen riguna.” Domin haka, suna da matsayi mai kyau a gaban Allah da kuma Kristi Yesu. Suna “da ganyayen dabino cikin hannuwansu,” suna yabon Jehovah Mamallakin sararin halitta da ya cancanta, wanda ya nuna sarautarsa ta wurin sarautar Sarkinsa da ya naɗa, Yesu Kristi, “Ɗan rago na Allah.”—Yohanna 1:29, 36.
8. Menene farmakin Gog zai sa Kristi ya yi, da wane sakamako?
8 Farmakin Gog zai sa Sarki da Allah ya naɗa ya tashi aiki ya yi yaƙi na Armageddon. (Ru’ya ta Yohanna 16:14, 16) Waɗanda suka ƙi su ba da kai ga ikon mallaka na Jehovah za su sha halaka. Waɗanda suka jimre da ƙunci domin amincinsu ga Mulkin Allah kuma, za su sami sauƙi na dindindin. Game da wannan, manzo Bulus ya rubuta: “Ainihin shaida ke nan ta shari’a mai-adalci ta Allah; da nufin a maishe ku kun cancanta ga mulkin Allah, wanda ku ke shan wahala dominsa: idan abu mai-adalci ne a gaban Allah a sāka ma waɗanda ke ƙuntata ku da ƙunci; ku kuma waɗanda a ke ƙuntata ku hutawa tare da mu, yayin bayyanuwar Ubangiji Yesu daga sama tare da mala’iku na ikonsa cikin wuta mai-huruwa, yana ɗaukan ramako bisa waɗanda ba su san Allah ba, da waɗanda sun ƙi yin biyayya da bisharar Ubangijinmu Yesu.”—2 Tassalunikawa 1:5-8.
9, 10. (a) Ta yaya Jehovah ya ba Yahuda nasara bisa magabta masu ƙarfi? (b) Menene Kiristoci a yau dole su ci gaba da yi?
9 A lokacin ƙunci mai girma mai zuwa, da zai ƙarasa a Armageddon, Kristi zai yi yaƙi da mugunta. Amma mabiyansa ba sa bukatar su yi faɗa, yadda ba a bukaci mazaunan Yahuda na mulkin ƙabila biyu dubban shekaru da suka shige ba. Yaƙin na Jehovah ne, kuma ya ba su nasara. Labarin ya ce: “Ubangiji ya sa ’yan kwanto su yi fakon ’ya’yan Ammon, da na Moab, da na dutsen Seir, waɗanda suka zo yaƙi da Yahuda; aka buga su kuwa. Gama ’ya’yan Ammon da na Moab suka tashi yaƙi da mazaunan dutsen Seir, domin su kashe su, su halaka su sarai: sa’anda suka ƙarasa mazaunan Seir, kowa ya yi ta ƙoƙari shi halaka wani. Sa’anda Yahuda suka zo hasumiya ta tsaro mai-fuskanta jeji, suka duba taron; ga su kuwa, gawaye ne, faɗaɗu a ƙasa, babu wanda ya tsira.”—2 Labarbaru 20:22-24.
10 Daidai da yadda Jehovah ya annabta ne: “Babu bukata ku yi wannan yaƙi.” (2 Labarbaru 20:17) Wannan tafarki ne da Kiristoci za su bi lokacin da Yesu Kristi zai fita “garin yin nasara.” Kafin lokacin, za su ci gaba da yaƙan mugunta, ba da makaman yaƙi ba, amma da makamai na ruhaniya. A ta haka, sun ci gaba da “rinjayi mugunta da nagarta.”—Romawa 6:13; 12:17-21; 13:12; 2 Korinthiyawa 10:3-5.
Wanene Zai Shugabanci Farmakin Gog?
11. (a) Waɗanne mutane ne Gog zai yi amfani da su a yin farmakinsa? (b) Menene kasance a faɗake a ruhaniya ya ƙunsa?
11 An nuna Gog na Magog cewa Shaiɗan Iblis ne cikin matsayinsa tun daga shekara ta 1914. Domin shi halitta na ruhu ne, ba zai iya yin farmakinsa kai tsaye ba, amma zai yi amfani da mutane su cika nufinsa. Su waɗanne mutane ne? Littafi Mai Tsarki bai ba mu daki-dakin ba, amma ya gaya mana alamar da ta taimake mu mu san su waɗanne ne. Yayin da aukuwa na duniya suke cika annabce-annabcen Littafi Mai Tsarki, a hankali za mu fahimta batun sarai. Mutanen Jehovah suna guje wa kame-kame amma sun kasance a faɗake a ruhaniya, suna sane da yanayin siyasa da na addini da suke cika annabcin Littafi Mai Tsarki.
12, 13. Ta yaya annabi Daniel ya annabta farmaki na ƙarshe a kan mutanen Allah?
12 Annabi Daniel ya ba da ƙarin bayani game da farmaki na ƙarshe a kan mutanen Allah, ya rubuta haka: “[Sarkin arewa] za ya fita kuwa da babbar hasala domin shi halaka mutane dayawa, ya washe su sarai. Za ya kafa [tanti] na fādassa tsakanin teku da dutse mai-tsarki mai-daraja.”—Daniel 11:44, 45.
13 Bisa yaren Littafi Mai Tsarki, “teku” ita ce Babbar Teku, ko kuma Bahar Mahaliya, “dutse mai-tsarki” kuma Sihiyona ce, da Jehovah ya ce game da ita: “Na kafa sarkina a bisa dutsena mai-tsarki Sihiyona.” (Zabura 2:6; Joshua 1:4) Saboda haka, a azanci na ruhaniya, ƙasar da ke “tsakanin teku da dutse mai-tsarki” suna wakilta yanayin ni’ima na ruhaniya na shafaffun Kiristoci. Ba a san su kuma ba cikin tekun mutane da suke bare daga Allah, amma suna zuba ido ga sarautar Kristi Yesu cikin Mulkinsa na samaniya. A bayyane, shafaffun bayin Allah, tare da abokansu taro mai girma masu aminci, su ne za su zama abin nema na sarkin arewa yayin da ya fara mugun farmakinsa a cikar annabcin Daniel.—Ishaya 57:20; Ibraniyawa 12:22; Ru’ya ta Yohanna 14:1.
Menene Bayin Allah Za Su Yi?
14. Waɗanne abubuwa uku mutanen Allah za su yi lokacin da aka yi musu farmaki?
14 Me za a yi tsammanin bayin Allah su yi lokacin da suke ƙarƙashin farmaki? Har ila, abin da al’ummar Allah a zamanin Jehoshaphat suka yi ne tafarki. Ka lura cewa an umurce mutanen su yi abubuwa uku: (1) su yi shiri, (2) su tsaya shuru, (3) su ga ceton Jehovah. Ta yaya mutanen Allah a yau za su yi daidai da waɗannan kalmomi?—2 Labarbaru 20:17.
15. Menene yake nufi ga mutanen Jehovah su yi shiri?
15 Su yi shiri: Ba tare da shakka ba, mutanen Allah za su ci gaba da riƙe matsayinsu na masu goyon bayan Mulkin Allah. Za su ci gaba da riƙe matsayinsu na Kiristoci masu tsaka-tsaki. Za su ‘kahu yadda ba sa kawuwa’ a hidimarsu na aminci ga Jehovah kuma su ci gaba da yabon Jehovah domin alherinsa a fili. (1 Korinthiyawa 15:58; Zabura 118:28, 29) Ba wani matsi na yanzu ko kuma na nan gaba da zai sa su bar wannan matsayi da Allah ya amince da shi.
16. A wace hanya ce bayin Jehovah za su tsaya shuru?
16 Su yi shuru: Bayin Jehovah ba za su yi ƙoƙarin su ceci kansu ba amma za su dogara sarai ga Jehovah. Shi kaɗai zai iya ceton bayinsa daga tarzomar duniya, kuma ya yi alkawarin hakan. (Ishaya 43:10, 11; 54:15; Makoki 3:26) Dogara ga Jehovah zai haɗa da dogara ga hanyar sadarwarsa da ake gani na zamani wadda yake amfani da ita na shekaru yanzu don cika ƙudurinsa. Fiye da dā, Kiristoci na gaskiya suna bukatar su sa dogararsu wajen abokan bauta da Jehovah da Sarkinsa suka naɗa su yi ja-gora. Waɗannan maza masu aminci za su jagabanci mutanen Allah. Yin banza da ja-gorarsu zai jawo bala’i.—Matta 24:45-47; Ibraniyawa 13:7, 17.
17. Me ya sa bayin Allah masu aminci za su ga ceton Jehovah?
17 Su ga ceton Jehovah: Ceto ne ladar waɗanda suka riƙe matsayinsu na tsaka-tsaki na Kirista kuma da suke dogara ga Jehovah don ceton. Har sai lokaci na ƙarshe—gwargwadon iyawarsu—za su sanar da zuwan ranar hukuncin Jehovah. Dole dukan halittu su sani cewa Jehovah shi ne Allah na gaskiya kuma yana da bayi masu aminci a duniya. Ba za a sake samun bukatar doguwar jayayya a kan damar ikon mallaka na Jehovah ba.—Ezekiel 33:33; 36:23.
18, 19. (a) Yaya waƙar da ke a Fitowa sura ta 15 ta nuna yadda waɗanda suka tsira wa farmakin Gog suke ji? (b) Menene ya kamata mutanen Allah su yi a yau?
18 Da sabon kuzari, mutanen Allah za su shiga sabuwar duniya, suna ɗokin rera waƙar nasara, yadda Isra’ilawa na dā suka yi bayan cetonsu daga Jar Teku. Za su yi godiya ta har abada ga Jehovah domin kāriyarsa, ɗaɗɗaya da kuma rukuni, za su furta kalmomi na dā cewa: “Zan rera waƙa ga Ubangiji, gama ya ɗaukaka ƙwarai. . . . Ubangiji mayaƙi ne: Ubangiji ne sunansa. . . . Hannun damanka, ya Ubangiji, yana kwantsame magabci. Cikin girman fifikonka kana kilme masu-tayar maka, ka kan aike da fushinka, yana cinye su kamar tattaka. . . . Kai cikin jinƙanka ka biyar da mutane waɗanda ka fanshe su: Ka yi musu ja gaba da ƙarfinka har mazauninka mai-tsarki. . . . Za ka shigadda su, ka dasa su cikin dutse na gādonka. Wurin ke nan, ya Ubangiji, wanda ka yi domin ka zauna a ciki. Tsatsarkan wuri, ya Ubangiji, wanda hannuwanka sun kafa. Ubangiji za ya yi mulki har abada abadin.”—Fitowa 15:1-19.
19 Yanzu da begen rai na har abada ya daɗa haske fiye da dā, zarafi mai kyau ne ga bayin Allah su nuna ibadarsu ga Jehovah kuma su sabonta ƙudurinsu su bauta masa shi Sarkinsu madawwami!—1 Labarbaru 29:11-13.
Za Ka Iya Bayyanawa?
• Me ya sa Gog zai yi farmakinsa gāba da shafaffu da kuma waɗansu tumaki?
• Yaya mutanen Allah za su yi shiri?
• Menene yake nufi a tsaya shuru?
• Ta yaya mutanen Allah za su ga ceton Jehovah?
[Hoto a shafi na 26]
Jehovah ya sa Jehoshaphat da mutanensa suka ci nasara, ba su bukaci su yi faɗa ba
[Hoto a shafi na 28]
Shafaffu da waɗansu tumaki suna sa hannu a ɗaukaka ikon mallaka na Jehovah
[Hoto a shafi na 30]
Kamar Isra’ila ta dā, mutanen Allah ba da daɗewa ba za su fara rera waƙar nasara