An Tsarkake ka
“Aka wanke ku . . . aka tsarkake ku.” —1 KOR. 6:11.
1. Mene ne Nehemiya ya gani sa’ad da ya koma Urushalima? (Ka duba hoton da ke wannan shafin.)
MUTANEN Urushalima sun yi mamaki sosai. Me ya sa? Domin an ƙyale wani sanannen maƙiyin Jehobah ya zauna a cikin wani ɗaki a haikalin. Lawiyawa sun bar aikin da aka ba su. Dattawa kuma suna kasuwanci a ranar Assabaci maimakon su fi mai da hankali ga bautar Jehobah. Isra’ilawa da yawa suna auren waɗanda ba Yahudawa ba. Waɗannan ne wasu cikin matsalolin da Nehemiya ya gani sa’ad da ya koma Urushalima.—Neh. 13:6.
2. Ta yaya Isra’ila ta zama al’umma da aka tsarkake?
2 A cikin shekaru dubu da suka shige, Isra’ilawa suna shirye su yi wa Jehobah biyayya. Sun ce: “Dukan zantattukan da Ubangiji ya faɗi mu a aikata su.” (Fit. 24:3) Saboda haka, Allah ya tsarkake ko kuma ware su a matsayin mutanen da ya zaɓa. Wannan gata ne mai girma sosai. Bayan shekara arba’in, sai Musa ya tuna musu cewa: “Kai al’umma mai-tsarki ne ga Ubangiji Allahnka: Ubangiji Allahnka ya zaɓe ka ka zama al’umma keɓaɓiya a gare shi, gaba da dukan al’ummai da ke bisa fuskar duniya.”—K. Sha 7:6.
3. Mene ne ya faru da bauta ta gaskiya sa’ad da Nehemiya ya koma Urushalima a lokaci na biyu?
3 Abin baƙin ciki, al’ummar Isra’ila ba ta cika alkawarinta ba. Ko da yake akwai wasu Yahudawa da suke bauta wa Allah, amma yawancinsu ba sa shirye su yi wa Jehobah biyayya kuma sun yi kamar su masu tsarki ne. Nehemiya ya sake koma Urushalima bayan shekara ɗari da Yahudawan da suka rage suka koma don su sake gina birnin. Suna son su gina ta don su soma bauta wa Jehobah kuma. Amma a lokacin da Nehemiya ya isa, sai ya ga cewa Yahudawa ba su saka bautar Jehobah farko a rayuwarsu ba.
4. Waɗanne fannoni huɗu ne za su taimaka mana mu ci gaba da zama tsarkakku?
4 Kamar Isra’ilawa, Allah ya tsarkake Shaidun Jehobah. Kiristoci shafaffu da kuma “taro mai-girma” masu tsarki ne, kuma suna bauta wa Jehobah kaɗai. (R. Yoh. 7:9, 14, 15; 1 Kor. 6:11) Ba ma son mu rasa dangantakarmu da Jehobah a matsayin tsarkakku kamar yadda Isra’ilawa suka yi. Mene ne zai taimaka mana mu ci gaba da zama tsarkakku kuma mu samu tagomashin Jehobah? A wannan talifin, za mu tattauna fannoni huɗu da aka taƙaita a littafin Nehemiya sura ta 13: (1) Ka guji mugun tarayya da (2) ka goyi bayan ƙungiyar Jehobah da (3) Ka sa hidimar Jehobah a gaba da kuma na (4) ka kasance da halin Kirista. Bari yanzu mu tattauna kowane cikin waɗannan fannonin.
KA GUJI MUGUN TARAYYA
5, 6. Su wane ne Eliashib da Tobiah, me ya sa Eliashib yake tarayya da Tobiah?
5 Karanta Nehemiya 13:4-9. Kullum muna fuskantar mugun tarayya da zai iya sa mu zama marasa tsarki. Littafi Mai Tsarki ya gaya mana game da Babban Firist Eliashib da kuma wani mutum mai suna Tobiah, wanda wataƙila ɗan Ammon ne da ke yi wa sarkin Fasiya aiki. Tobiah da abokansa sun ƙoƙarta su sa Nehemiya ya daina gina ganuwar Urushalima. (Neh. 2:10) A cikin Dokar Allah, an hana Ammonawa su shiga cikin haikali. (K. Sha 23:3) Amma, me ya sa Eliashib ya ba Tobiah wurin zama a ɗakin cin abinci na haikali?
6 Da akwai dalilai uku: Na farko, Eliashib dangin Tobiah ne. Na biyu, Tobiah da ɗansa Jehohanan sun auri matan Yahudawa, kuma Yahudawa da yawa suna yaba wa Tobiah. (Neh. 6:17-19) Na uku, jikan Eliashib ya auri ’yar Sanballat, wanda gwamnar Samariya ne da kuma aminin Tobiah. (Neh. 13:28) Wannan dangantaka ce ta sa Eliashib ya ƙyale Tobiah wanda yake hamayya da aikin mutanen Allah ya riƙa ba shi shawara kuma Tobiah ba Ba’isra’ile ba ne. Amma Nehemiya ya kasance da aminci ga Jehobah ta wajen jefar da dukan kayayyakin Tobiah daga cikin haikali.
7. Ta yaya dattawa da sauran ’yan’uwa suke ƙoƙari su ga cewa sun kasance da tsarki?
7 A matsayin waɗanda suka keɓe kansu ga Jehobah, wajibi ne mu kasance da aminci a gare shi. Idan ba mu bi mizanansa ba, ba za mu ci gaba da zama tsarkakku a gabansa ba. Kada mu ƙyale dangantakar iyali ta shawo kan ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki. Dattawa Kiristoci suna yanke shawarwari bisa ra’ayin Allah ba na su ba ko kuma yadda suke ji game da wasu. (1 Tim. 5:21) Dattawa suna mai da hankali sosai don kada su yi abin da zai sa su yi rashin amincewar Allah.—1 Tim. 2:8.
8. Mene ne ya kamata mu tuna game da tarayyarmu?
8 Ya kamata mu tuna cewa “zama da miyagu ta kan ɓata halaye na kirki.” (1 Kor. 15:33) Wasu cikin danginmu suna iya zama mugun tarayya, wato su riƙa sa mu yin abubuwan da ba su dace ba. Eliashib ya kafa wa mutanen misali mai kyau ta wajen goyon bayan Nehemiya sa’ad da yake gina garun Urushalima. (Neh. 3:1) Amma da shigewar lokaci, abokantakar da Eliashib ya yi da Tobiah da wasu ta sa ya yi abubuwan da ba su dace ba kuma ya zama marar tsarki a gaban Jehobah. Muna bukatar mu yi abokantaka da mutane da za su ƙarfafa mu mu yi abubuwa masu kyau, kamar su karanta Littafi Mai Tsarki da halartar taro da kuma yin wa’azi. Muna farin ciki sa’ad da danginmu suka ƙarfafa mu mu yi abin da ya dace.
KA GOYI BAYAN ƘUNGIYAR JEHOBAH
9. Wane yanayi ne haikalin Jehobah yake ciki, kuma mene ne Nehemiya ya yi don ya daidaita yanayin?
9 Karanta Nehemiya 13:10-13. Lawiyawa ba sa yin aikin da aka ce su yi a haikali. Me ya sa? Domin mutanen ba sa ba da gudummawar kuɗi mai yawa a haikalin, shi ya sa Lawiyawa suke yin aiki a gonakinsu don su kula da iyalansu. Kamar dai waɗanda aka sanya su riƙa karɓan zakka ba sa yin haka ko kuma idan sun karɓa, sai su ƙi aika ta zuwa haikali kamar yadda aka ce su yi. (Neh. 12:44) Nehemiya ya sa aka karɓi wannan zakkar, kuma ya naɗa maza masu aminci da za su riƙa aika wa Lawiyawa zakkar.
10, 11. Ta yaya za mu goyi bayan bauta ta gaskiya?
10 Wane darasi ne za mu iya koya daga wannan labarin? An tuna mana cewa muna da gatar girmama Jehobah da wadatarmu. (Mis. 3:9) Sa’ad da muka ba da gudummawa don mu tallafa wa aikinsa, muna ba Jehobah abin da ya fito daga gare shi ne. (1 Laba. 29:14-16) Wataƙila muna ganin cewa gudummawarmu kaɗan ne, amma idan muka yi hakan da yardan rai, Jehobah zai yi farin cikin karɓa baiwarmu.—2 Kor. 8:12.
11 Wata iyali mai yara takwas tana gayyatar ma’aurata tsofaffi da suke hidimar majagaba na musamman su ci abinci tare da su, sau ɗaya kowane mako. Kuma sun yi hakan shekaru da yawa. Mamar takan ce: “Tun da yake ina dafa abincin mutane goma, ba zai yi wuya ba na haɗa da na mutane biyu.” Ana iya ganin wannan kamar ƙaramin abu ne, amma waɗannan majagaba sun yin godiya sosai don karimci da aka nuna musu! Majagaban sun kuma taimaka wa iyalin ta wajen gaya musu labarai da kuma ƙarfafa yaran su samu ci gaba a cikin ƙungiyar Jehobah. Daga baya, dukan yaran suka soma hidima ta cikakken lokaci.
12. Wane misali mai kyau ne dattawa da bayi masu hidima suke kafawa a cikin ikilisiya?
12 Labarin ya kuma koya mana cewa ya kamata dattawa da bayi masu hidima su zama masu kafa misali mai kyau a ƙungiyar Jehobah. Wasu a cikin ikilisiyar za su amfana daga misalinsu. Bulus ya goyi bayan bauta ta gaskiya kuma ya ba da shawarwari a kan yadda Kiristoci za su iya ba da gudummawa. Ya kamata dattawa su yi koyi da shi.—1 Kor. 16:1-3; 2 Kor. 9:5-7.
KA SA BAUTAR ALLAH A KAN GABA
13. Mene ne wasu Isra’ilawa suke yi a ranar Assabaci?
13 Karanta Nehemiya 13:15-21. Idan muna yawan tunani game da abubuwan mallaka kuma muna aiki tuƙuru don mu tara su, za mu iya rasa dangantakarmu da Jehobah. Fitowa 31:13 ta bayyana cewa Isra’ilawa suna yin Assabaci kowane mako don su tuna cewa su tsarkakku ne. An keɓe ranar Assabaci don a yi bauta ta iyali da addu’a da kuma yin bimbini a kan Dokar Allah. Amma, wasu Isra’ilawa a zamanin Nehemiya sun yi amfani da ranar don kasuwanci, kamar yadda suke yin amfani da sauran kwanaki na makon. Saboda haka, Nehemiya ya kori baƙi masu kasuwanci daga birnin kuma ya kulle ƙofofin kafin a soma Assabaci.
14, 15. (a) Mene ne zai faru idan muka fi mai da hankali ga neman kuɗi? (b) Ta yaya za mu iya shiga hutun Allah?
14 Mene ne za mu iya koya daga misalin Nehemiya? Darasi na farko shi ne mu rage yawan lokacin da muke yi wajen kasuwanci. Idan ba mu yi haka ba, aikinmu zai janye hankalinmu musamman idan muna jin daɗinsa. Ka tuna cewa Yesu ya ce ba za mu iya bauta wa ubangiji biyu ba. (Karanta Matta 6:24.) Da a ce Nehemiya ya so, da ya samu kuɗi sosai kuma da ya yi amfani da lokacinsa wajen yin kasuwanci da mutanen Tyre da wasu attajirai. Amma, mene ne ya yi? (Neh. 5:14-18) Ya yi aiki tuƙuru don ya taimaki ’yan’uwansa kuma ya ɗaukaka sunan Jehobah. Hakazalika, dattawa da bayi masu hidima a yau suna mai da hankali don yin abubuwa da za su amfani ikilisiyar kuma ’yan’uwa suna ƙaunarsu don hakan. Shi ya sa mutanen Allah suke ƙaunar juna da kasance da salama da kuma kwanciyar hankali.—Ezek. 34:25, 28.
15 Ba a bukatar Kiristoci su yi Assabaci kowane mako. Amma, Bulus ya gaya mana cewa “akwai fa hutun assabbat ajiyayye domin jama’ar Allah.”Sai ya daɗa cewa: “Wanda ya shiga cikin hutunsa shi da kansa ya huta daga ayyukansa, kamar yadda Allah ya yi daga nasa.” (Ibran. 4:9, 10) A matsayin Kiristoci, muna iya shiga cikin hutun Allah ta wajen yi masa biyayya da kuma yin abubuwa don mu tallafa wa nufinsa. Shin kai da iyalinka kuna saka Jehobah farko a rayuwarku ta wajen yin bauta ta iyali da halartar taro da kuma yin wa’azi? Wataƙila shugaban wajen aikinmu ko kuma mutanen da muke aiki tare da su ba za su ɗauki waɗannan abubuwa da muhimmanci ba. Ya kamata mu dage kuma mu bayyana musu cewa hidimar Jehobah ce ta fi muhimmanci a gare mu. Hakan ya yi daidai da abin da Nehemiya ya yi sa’ad da ya kori mutanen Tyre kuma ya rufe ƙofofin birnin. Ta hakan, ya nuna cewa Jehobah ne ya fi muhimmanci a gare shi. Domin an tsarkake mu, yana da kyau mu tambayi kanmu, ‘Shin salon rayuwata ta nuna cewa na keɓe kaina don yin hidimar Jehobah?’—Mat. 6:33.
KA KASANCE DA HALIN KIRISTA
16. Ta yaya Isra’ilawa a zamanin Nehemiya suka kusan rasa matsayinsu?
16 Karanta Nehemiya 13:23-27. A zamanin Nehemiya, mazan Isra’ila suna auren mata daga wasu al’ummai. A lokaci na farko da ya ziyarci Urushalima, dukan maza tsofaffi sun sa hannu a wata yarjejeniya kuma suka yi alkawari cewa mazan ba za su auri mata daga wasu al’ummai ba. (Neh. 9:38; 10:30) Amma bayan wasu shekaru, sai ya ga cewa mazan Yahudawa suna auren mata daga wasu al’ummai kuma sun kusan rasa matsayinsa na mutanen da Allah ya ware da kuma tsarkake. Yaran waɗannan mata ba sa iya karanta da kuma yin Ibrananci. Sa’ad da waɗannan yaran suka yi girma, shin za su ɗauka cewa su Isra’ilawa ne? Ko kuwa za su ɗauka cewa su baƙi ne, wato mutanen Ashdod da Ammonawa ko kuwa Mowabawa? Idan ba su iya Ibrananci ba, mai yiwuwa ba za su fahimci Dokar Allah ba. Zai yi musu wuya su san Jehobah kuma su bauta masa maimakon allolin ƙarya da mahaifiyarsu take bauta wa. Sa’ad da Nehemiya ya ga hakan, sai ya ɗauki mataki nan da nan don ya kāre sunan Isra’ilawa.—Neh. 13:28.
17. Ta yaya iyaye za su iya taimaka wa yaransu su ƙulla nasu dangantaka da Jehobah?
17 A yau muna bukatar mu ɗauki mataki don mu taimaka wa yaranmu su kasance da halin da ya dace da Kirista. Iyaye, ku tambayi kanku, ‘Shin yarana sun san “harshe mai-tsarki,” wato koyarwar Littafi Mai Tsarki? (Zaf. 3:9) Shin irin abubuwa da yarana suke tattaunawa yana nuna cewa ruhun Allah ne yake rinjayarsu ko kuma na duniya?’ Kada ka yi saurin sanyin gwiwa idan ka ga cewa yaranka suna bukatar yin gyara. Alal misali, yana ɗaukan lokaci kafin a koyi wani yare, musamman idan akwai wasu abubuwan da ke janye hankalin mutum. Hakazalika, duniya tana ƙoƙari ta matsa wa yaranka su yi wa Allah rashin biyayya. Saboda haka, cikin haƙuri ka yi amfani da bauta ta iyali da wasu zarafi don ka taimaka wa yaranka su ƙulla dangantaka ta kud da kud da Jehobah. (K. Sha 6:6-9) Ka tuna musu amfanin kasancewa dabam da mutanen duniyar Shaiɗan. (Yoh. 17:15-17) Kuma ka yi ƙoƙari ka motsa zuciyarsu.
18. Me ya sa iyaye ne suka fi dacewa su taimaki yaransu su keɓe kansu ga Jehobah?
18 Yaranku ne za su tsai da shawara da kansu ko za su bauta wa Allah ko a’a. Amma, a matsayin iyaye za ku iya taimaka musu a hanyoyi da yawa. Hakan ya haɗa da kafa misali mai kyau da bayyana musu halin da ya dace da kuma sa su san sakamakon bin mugun shawarwari. Iyaye, yaranku suna bukatar ku taimaka musu su kasance da halin da ya dace a matsayin Kirista. Ku ne ya dace ku taimaka musu su samu ci gaba don su keɓe kansu ga Jehobah. Hakika, dukanmu muna bukatar mu kāre halinmu na Kirista, wato mu yi rayuwar da ta jitu da ƙa’idojin Allah.—R. Yoh. 3:4, 5; 16:15.
ALLAH ZAI YI MANA ALHERI
19, 20. Mene ne za mu iya yi don Jehobah ya yi mana alheri?
19 Annabi Malakai ya bayyana cewa Jehobah yana tuna da ‘waɗanda suke jin tsoronsa, da masu-tunawa da sunansa’ kuma yana saka sunansu a “littafin tunawa.” (Mal. 3:16, 17) Allah ba zai taɓa mance da waɗanda suke jin tsoronsa da kuma masu ƙaunar sunansa ba.—Ibran. 6:10.
20 Nehemiya ya yi addu’a: “Ka tuna da ni, ya Allahna, tare da alheri.” (Neh. 13:31) Allah zai sanya sunanmu a cikin littafin tunawa kamar yadda ya yi da Nehemiya, idan muka ci gaba da guje wa mugun tarayya, muka goyi bayan ƙungiyarsa, muka saka bautarsa a kan gaba kuma muka kāre matsayinmu na Kirista. Bari mu ci gaba da ‘gwada kanmu ko muna cikin imani.’ (2 Kor. 13:5) Jehobah zai yi mana alheri, idan ba mu ƙyale dangantakarmu da shi a matsayin tsarkakku ta yi tsami ba.