Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w11 4/1 p. 21
  • “Ka Tuna da Ni, Ya Allahna, Tare da Alheri”

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • “Ka Tuna da Ni, Ya Allahna, Tare da Alheri”
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
  • Makamantan Littattafai
  • “Ku Rinjayi Mugunta Da Nagarta”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2007
  • Darussa Daga Littafin Nehemiah
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2006
  • Ganuwar Urushalima
    Littafina na Labarun Littafi Mai Tsarki
  • Ganuwar Urushalima
    Darussa daga Littafi Mai Tsarki
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
w11 4/1 p. 21

Ka Kusaci Allah

“Ka Tuna da Ni, Ya Allahna, Tare da Alheri”

“INA tunanin cewa Jehobah, wanda ya san ni sosai, ba zai taɓa nuna mini ƙauna ko ya amince da ni ba.” Haka wata mata Kirista mai aminci ta rubuta, wadda ta yi fama da tunanin cewa ba ta da daraja. Irin wannan tunanin ya taɓa addabarka kuwa, kana tunanin cewa ba ka cancanci samun kulawar Allah ba, balle ka samu amincewarsa? Idan haka ne, kalmomin da aka rubuta a Nehemiya 13:31 za su iya ƙarfafa ka.

Nehemiya, gwamnan Yahudawa a ƙarni na biyar K.Z., ya yi iyakar ƙoƙarinsa ya faranta wa Allah rai. Shi ne ya yi ja-gora wajen sake gina bangon Urushalima duk da hamayyar abokan gaba suka yi. Ya zartar da Dokar Allah, ya kula da faƙirai, kuma ya yi ƙoƙarin ya gina bangaskiyar ’yan’uwansa Israilawa. Allah ya lura da ayyuka nagari da wannan mutumi mai aminci ya yi kuwa? Nehemiya ya sami amincewar Jehobah kuwa? Za mu iya samun amsoshin a cikin kalmomin ƙarshe na littafin da ke ɗauke da sunansa.

Nehemiya ya yi addu’a: “Ka tuna da ni, ya Allahna, tare da alheri.”a Nehemiya yana tsoron cewa Allah bai lura da nagargarun ayyukansa ba ne ko kuwa Allah zai mance da shi gabaki ɗaya? A’a. Babu shakka, Nehemiya ya san abin da marubuta na farko na Littafi Mai Tsarki suka rubuta game da irin ƙaunar da Jehobah yake yi wa masu bauta masa da aminci da kuma ayyukansu nagari. (Fitowa 32:32, 33; Zabura 56:8) To, mene ne yake roƙon Allah ya yi masa? Wani littafin bincike ya ce kalmar Ibrananci da aka fassara “tuna” tana nufin “ƙauna daga zuci da kuma ayyukan da suke biyo bayan tunawa.” Da cikkaken bangaskiya a ikon addu’a, Nehemiya yana roƙon Allah ya tuna da shi cikin ƙauna kuma ya albarkace shi.—Nehemiya 2:4.

Jehobah zai amsa addu’ar da Nehemiya ya yi cewa ya tuna da shi kuwa? A wata hanya, ya riga ya yi hakan. Domin Jehobah ya amince a rubuta addu’ar Nehemiya a cikin hurarrun Nasossi, hakan ya tabbatar da mu cewa yana tunawa da Nehemiya cikin ƙauna. Amma abin da “Mai-jin addu’a” zai yi, zai wuce amsa roƙon da Nehemiya ya yi.—Zabura 65:2.

A nan gaba Allah zai albarkaci Nehemiya domin dukan abubuwa masu kyau da ya yi domin bauta ta gaskiya. (Ibraniyawa 11:6) A sabuwar duniya ta adalci mai zuwa wadda Jehobah ya yi alkawarinta, zai albarkaci Nehemiya ta wurin ta da shi daga matattu.b (2 Bitrus 3:13; Ru’ya ta Yohanna 21:3, 4) A cikin aljannar, inda zai samu damar yin rayuwa har abada, Nehemiya zai ga cewa babu shakka, Jehobah ya tuna da shi da alheri.

Addu’ar Nehemiya ta tabbatar da gaskiyar kalmomin Sarki Dauda: “Za ka albarkaci mai-adilci; Ya Ubangiji, da tagomashi za ka kewaye shi kamar da garkuwa.” (Zabura 5:12) Hakika, Allah yana gani kuma yana daraja ƙoƙarce-ƙoƙarcen da muke yi da gaske don mu faranta masa rai. Muddin kana iya ƙoƙarinka don ka bauta masa, babu shakka zai tuna da kai da alheri kuma zai albarkace ka sosai.

[Hasiya]

a Wannan shi ne na ƙarshe a cikin wurare huɗu a wannan littafin da ke cikin Littafi Mai Tsarki inda Nehemiya ya yi addu’a ga Allah don samun sakamako mai kyau domin ayyukansa na aminci.—Nehemiya 5:19; 13:14, 22, 31.

b Domin ƙarin bayani game da nufin Allah ga mutane masu aminci a duniya, ka duba shafi na 3 da na 7 na littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?, Shaidun Jehobah ne suka wallafa.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba