DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH | AYUBA 11-15
Ayuba Ya Yi Imani da Tashin Matattu
Ayuba ya yi imani cewa Allah zai ta da shi daga matattu
14:7-9, 13-15
Ayuba ya yi amfani da bishiya, wataƙila bishiyar zaitun wajen nuna tabbaci da yake da shi cewa Allah zai ta da shi daga matattu
Bishiyar zaitun tana da jijiyoyi masu shiga ƙasa sosai kuma hakan yakan sa ta sake tsiro bayan an datse bishiyar. Muddin jijiyoyin ba su mutu ba, za su sake tsirowa
Idan aka yi ruwan sama bayan fāri mai tsawo, kututturen bishiyar zaitun zai iya sake tsirowa kuma “ya yi rassa”