Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w05 11/1 pp. 25-29
  • Za Ka Bi Allah Kuwa?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Za Ka Bi Allah Kuwa?
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2005
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Menene Bin Allah Yake Nufi?
  • Me Ya Sa Muke Bukatar Mu Bi Allah?
  • Ta Yaya Za Mu Bi Allah?
  • Ka Yi Tafiya Kamar Kana “Ganin Wannan Da Ba Ya Ganuwa”
  • Wace Albarka Ce Za a Samu?
  • Mu Riƙa Yin Tafiya Cikin Bangaskiya
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2025
  • Ka Bi Allah!
    “Ku Rera Waka da Farin Ciki” ga Jehobah
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2005
w05 11/1 pp. 25-29

Za Ka Bi Allah Kuwa?

“Ka bi Allah da tawali’u.”—Mika 6:8.

1, 2. Ta yaya za ka kwatanta yadda Jehobah yake ji game da mu da yadda uba yake koya wa ɗansa tafiya?

ƊAN yaro, yana tsaye a kan ƙafafunsa da ba su yi ƙwari ba, ya yi takunsa na farko ɗaya biyu zuwa hannun iyayensa. Ba zai kasance wani abu mai muhimmanci ba, amma ga uwarsa da ubansa, babban abu ne, lokaci ne da ke cike da bege domin abin da zai faru a nan gaba. Iyayen suna da begen cewa a watanni da shekaru masu zuwa yaron zai bi su suna tafiya tare. Suna da begen cewa za su yi wa yaron ja-gora a hanyoyi masu yawa kuma su tallafa masa a nan gaba.

2 Haka Jehobah Allah yake ji game da ’ya’yansa da ke duniya. Ya taɓa cewa game da mutanensa Isra’ilawa, ko kuma Ifraimu: “Ni ne na koya wa Ifraimu tafiya. Na ɗauke su a hannuna, . . . Na bishe su da linzamin alheri da ragamar ƙauna.” (Yusha’u 11:3, 4) A nan Jehobah ya kwatanta kansa da uba mai ƙauna wanda yake koya wa ɗansa tafiya cikin haƙuri, wataƙila yana ɗaukansa sa’ad da ya faɗi. Jehobah Ubanmu Mafi Girma, yana ɗokin ya koya mana tafiya. Yana kuma farin ciki ya ci gaba da koya mana sa’ad da muka ci gaba da yin ƙoƙari. Kamar yadda ayar jigonmu ta nuna, muna iya bin Allah! (Mika 6:8) Amma menene bin Allah yake nufi? Me ya sa muke bukatar mu yi haka? Ta yaya hakan zai yiwu? Kuma waɗanne albarkatai ake samu daga bin Allah? Bari mu bincika waɗannan tambayoyi huɗu ɗaiɗai da ɗaiɗai.

Menene Bin Allah Yake Nufi?

3, 4. (a) Menene yake da ban sha’awa game da kwatanci na tafiya tare da Allah? (b) Menene bin Allah yake nufi?

3 Hakika, mutum mai tsoka da jini ba zai iya tafiya da Jehobah a zahiri ba tun da shi ruhu ne. (Fitowa 33:20; Yahaya 4:24) Saboda haka sa’ad da Littafi Mai Tsarki ya yi maganar bin Allah, yana magana ne a alamance. Yana ba da kwatanci ne, da ya shafi dukan al’adu da kuma lokaci. Hakika, a wane wuri ne ko kuma zamani mutane ba za su iya fahimtar abin da ake nufi da mutum yana tafiya tare da wani ba? Wannan kwatancin ya nuna an shaƙu da kuma kusanci, ko ba haka ba? Wannan ya sa mun fahimci abin da ake nufi da bin Allah. Bari yanzu mu yi magana a kan abin da ake nufi.

4 Ka tuna da mutane masu aminci Anuhu da Nuhu. Me ya sa aka kwatanta su da cewa sun yi tafiya tare da Allah? (Farawa 5:24; 6:9) A cikin Littafi Mai Tsarki, kalmar nan “tafiya” sau da yawa tana nufin bin wani tafarki. Anuhu da Nuhu sun zaɓi tafarkin rayuwa da ta jitu da nufin Jehobah Allah. Ba kamar mutane da suke tare da su ba, sun dogara ga Jehobah domin ja-gora kuma sun yi biyayya ga umurninsa. Sun dogara a gare shi. Wannan yana nufi ne cewa Jehobah ne yake yanke masu shawarwarinsu? A’a. Jehobah ya ba wa mutane ’yancin zaɓan abin da suke so, kuma yana so mu yi amfani da wannan kyauta tare da ‘tunani.’ (Romawa 12:1) Amma kuma sa’ad da muke yanke shawara, cikin tawali’u muna ƙyale Jehobah ya yi wa tunaninmu ja-gora. (Karin Magana 3:5, 6; Ishaya 55:8, 9) Wato, sa’ad da muke tafiya a rayuwarmu, muna tare da Jehobah ne muna binsa.

5. Me ya sa Yesu ya yi maganar ƙara taƙi ga rayuwar mutum?

5 Sau da yawa Littafi Mai Tsarki yana kwatanta rai da tafiya. A wasu lokatai kwatancin kai tsaye ne, amma wasu kuma wajen ma’ana ne. Alal misali, Yesu ya ce: “Wanene a cikinku, don damuwa tasa, zai iya ƙara ko da taƙi ga tsawon rayuwa tasa?” (Matiyu 6:27) Wani abu game da waɗannan kalmomi zai ba ka mamaki. Me ya sa Yesu ya yi maganar “taƙi” tun da gwaji ne na tafiya, ga “rayuwa” ta mutum?a Hakika, Yesu yana kwatanta rayuwa ce da tafiya. Wato, ya koyar ne cewa damuwa ba za ta taimake ka ka ƙara ko taƙi guda ga tafiyar rayuwarka ba. Ya kamata ne, to, mu kammala cewa babu abin da za mu iya yi mu ƙara tsawon wannan tafiyar? Hakika ba haka yake ba! Wannan ya kawo mu ga tambayarmu ta biyu, Me ya sa muke bukatar mu bi Allah?

Me Ya Sa Muke Bukatar Mu Bi Allah?

6, 7. Mutane ajizai suna bukatar menene da gaggawa, kuma me ya sa za mu juya ga Jehobah domin ya biya mana wannan bukatar?

6 An ba da bayanin dalili ɗaya da ya sa muke bukatar mu bi Jehobah Allah a Irmiya 10:23: “Ya Ubangiji, na sani al’amuran mutum ba a hannunsa suke ba, ba mutum ne ke kiyaye takawarsa ba.” Mu ’yan adam ba mu da iyawa da kuma damar ja-gorar tafarkin rayuwarmu. Muna bukatar ja-gora da gaggawa. Waɗanda suka dage suka bi nasu hanyar kuma suka ’yanta kansu daga Allah, sun yi irin kuskure da Adamu da Hauwa’u suka yi. Ma’aurata na farko sun zaɓi su zaɓa wa kansu abin da ke mai kyau da marar kyau. (Farawa 3:1-6) Wannan zaɓi ba na mu ba ne.

7 Kana ganin kana bukatar ja-gora a tafiya ta rayuwa? Kowace rana muna fuskantar yanke shawara manya ko ƙanana. Wasu suna da wuya suna iya shafar rayuwarmu ta nan gaba. Amma ka yi tunani, wani wanda ya fi mu tsufa da kuma hikima yana farin ciki ya yi mana ja-gora wajen tsai da waɗannan shawarwari! Abin baƙin ciki, yawancin mutane sun gwammace su dogara da nasu sani su yi wa kansu ja-gora. Sun yi banza da gaskiyar da take rubuce cikin Karin Magana 28:26: “Wanda yake dogara ga son zuciyarsa, wawa ne, amma wanda yake tafiya cikin hikima zai kuɓuta.” Jehobah yana so mu kuɓuta daga bala’i da yake zuwa domin dogara da zuciya mai rikici ta ’yan adam. (Irmiya 17:9) Yana so mu yi tafiya cikin hikima, mu dogara a gare shi, shi Mai mana ja-gora mai hikima. Idan muka yi haka, tafiyarmu ta rayuwa za ta kasance da kwanciyar rai, da gamsuwa.

8. Zunubi da ajizanci suna kai mutane ga wane masauki, duk da haka menene Jehobah yake so mu mora?

8 Wani dalili kuma da ya sa muke bukatar mu bi Allah ya ƙunshi tsawon tafiya da za mu yi. Littafi Mai Tsarki ya faɗi wata gaskiya mai ƙuna. Hakika, dukan mutane ajizai masaukinsu ɗaya. Da yake kwatanta matsaloli da suke zuwa a lokacin tsufa, Mai Hadishi 12:5 ta ce: “Daganan sai kabari, masu makoki kuwa su yi ta kai da kawowa a kan tituna.” Kabari, shi ne inda zunubi da ajizanci suke kai mu. (Romawa 6:23) Amma, Jehobah yana so mu more fiye da gajeriyar tafiya daga haihuwa zuwa kabari. (Ayuba 14:1) Sai dai idan mun yi tafiya da Allah za mu sami begen tafiya mai tsawo kamar yadda aka nufe mu da ita, har abada. Ba abin da kake bukata ba ke nan? A bayyane yake cewa kana bukatar ka yi tafiya da Ubangijinka.

Ta Yaya Za Mu Bi Allah?

9. Me ya sa wasu lokaci Jehobah yake ɓoye ga mutanensa, duk da haka, wane tabbaci ya bayar in ji Ishaya 30:20?

9 Tambaya ta uku da za mu tattauna tana bukatar mu mai da mata hankali da kyau. Tambayar ita ce, Ta yaya za mu bi Allah? Mun sami amsa a Ishaya 30:20, 21: “Ubangiji . . . kansa zai kasance tare da ku, ya koya muku, ba za ku ƙara wahalar nemansa ba. Idan kuka kauce daga hanya zuwa dama ko hagu, za ku ji muryarsa a bayanku yana cewa, ‘Ga hanyan nan, ku bi ta.’ ” A wannan ayoyin masu ban ƙarfafa, kalmar Jehobah da ke rubuce a aya ta 20 wataƙila ta tunasar da mutanensa cewa sa’ad da suka yi masa tawaye, kamar yana ɓoye ne a gare su. (Ishaya 1:15; 59:2) A nan, an kwatanta cewa Jehobah ba ya ɓoye, amma yana tsaye ne a fili a gaban mutanensa masu aminci. Muna iya tunanin malami yana tsaye a gaban ɗalibai, yana kwatanta musu abin da yake so su yi.

10. A wace hanya ce kake jin ‘murya a bayanka’ ta Ubangiji?

10 A aya ta 21, wani kwatanci dabam aka yi. An kwatanta cewa Jehobah yana tafiya a bayan mutanensa, yana gaya musu hanyar da za su bi. Wani masanin Littafi Mai Tsarki ya lura cewa wannan furcin wataƙila daga yadda makiyayi yake bin tumakinsa ne, yana kira yana yi musu ja-gora yana hana su bin hanyar da ba daidai ba. Ta yaya wannan kwatancin ya shafe mu? Hakika, sa’ad da muka juya ga Kalmar Allah domin ja-gora, muna karanta kalmomi ne da aka rubuta shekaru dubbai da suka shige. Kamar suna zuwa ne daga bayanmu, a lokatai da suka shige. Duk da haka, suna da muhimmanci a yau kamar a ranar da aka rubuta su. Gargaɗin Littafi Mai Tsarki yana iya mana ja-gora a shawarwarinmu na yau da kullum, kuma zai iya taimakonmu mu tsara tafarkin rayuwa ta nan gaba. (Zabura 119:105) Sa’ad da muka nemi irin wannan gargaɗi kuma muka yi amfani da su, Jehobah ne yake mana ja-gora. Muna bin Allah.

11. In ji Irmiya 6:16, Jehobah ya ba da kwatancin wace gayyata ce ga mutanensa, amma yaya suka amsa?

11 Shin da gaske muna ƙyale Kalmar Allah ta yi mana irin wannan ja-gora ta kurkusa? Yana da muhimmanci wani lokaci mu dakata mu bincika kanmu da gaske. Ka yi la’akari da ayar da za ta taimake mu mu yi haka: “Haka Ubangiji ya ce, ‘Ku tsaya kan hanyoyi, ku duba, ku nemi hanyoyin dā, inda hanya mai kyau take, ku bi ta, don ku hutar da rayukanku.’ ” (Irmiya 6:16) Waɗannan kalmomin wataƙila sun tuna mana matafiyi da ya dakata a mararrabar hanya domin ya yi tambaya. A hanya ta ruhaniya, mutanen Jehobah masu tawaye a Isra’ila suna bukatar su yi haka. Suna bukatar su “nemi hanyoyin dā.” Wannan “hanya mai kyau” hanya ce da kakaninsu masu aminci suka bi, hanyar da al’ummar cikin wauta suke kauce wa. Abin baƙin ciki, Isra’ila ba ta ji wannan gargaɗi daga Jehobah ba. Wannan ayar ta ci gaba: “Amma suka ce, ‘Ai, ba za mu bi ta ba.’ ” A zamanin yau mutanen Allah sun bi wannan gargaɗin.

12, 13. (a) Ta yaya mabiyan Kristi shafaffu suka bi gargaɗi da ke Irmiya 6:16? (b) Ta yaya za mu bincika kanmu game da hanya da muke bi a yau?

12 Tun a ƙarshen ƙarni na 19, mabiyan Kristi da aka shafa sun bi gargaɗin Irmiya 6:16. Sun yi ja-gora wajen komawa ga “hanyoyin dā.” Ba kamar Kiristendam ba mai ridda, sun bi cikin aminci “sahihiyar maganar” da Yesu Kristi ya kafa kuma ya ɗaukaka ta wajen mabiyansa masu aminci a ƙarni na farko A.Z. (2 Timoti 1:13) Har wa yau, shafaffun suna taimakon juna da kuma abokanansu “waɗansu tumaki” su bi hanyar rayuwa mai kyau na farin ciki da Kiristendam suka yi watsi da ita.—Yahaya 10:16.

13 Ta wajen ba da abinci na ruhaniya a kan kari amintaccen bawan nan ya taimaki miliyoyi su sami “hanyoyin dā” kuma su bi Allah. (Matiyu 24:45-47) Kana tsakanin waɗannan miliyoyin kuwa? Idan haka ne, menene za ka yi domin kada ka kauce a hanyar kuma ka bi na ka tafarkin? Hikima ce ka dakata ka bincika hanyar da kake bi a rayuwa. Idan kana karatun Littafi Mai Tsarki da aminci da kuma littattafan Littafi Mai Tsarki kuma kana halartar tsarin koyarwa da shafaffu suka yi tanadi a yau, to ana koyar da kai ka yi tafiya tare da Allah. Kuma sa’ad da cikin tawali’u ka bi gargaɗi da aka bayar, hakika kana bin Allah, kana bin “hanyoyin dā.”

Ka Yi Tafiya Kamar Kana “Ganin Wannan Da Ba Ya Ganuwa”

14. Idan Jehobah ya kasance gaskiya a gare mu, ta yaya wannan zai bayyana a shawarwari da muke yankewa?

14 Domin mu yi tafiya da Jehobah, dole ne ya kasance da gaske a gare mu. Ka tuna, Jehobah ya tabbatar wa masu aminci na Isra’ila ta dā cewa shi ba a ɓoye yake a gare su ba. A yau, haka ma ya bayyana kansa ga mutanensa cewa shi ne Mai Koyar da su. Haka Jehobah yake da gaske a gare ka, kamar yana tsaye ne a gabanka yana koyar da kai? Irin wannan bangaskiya muke bukata idan za mu bi Allah. Musa yana da irin wannan bangaskiyar, “ya kuwa jure saboda yana ganin wannan da ba ya ganuwa.” (Ibraniyawa 11:27) Idan Jehobah ya kasance gaskiya a gare mu, to za mu tuna yadda yake ji sa’ad da muke yanke shawara. Alal misali, ba za mu ma yi tunanin yin mugun abu ba kuma mu ɓoye zunubanmu daga dattawa Kiristoci ko kuma daga ’yan’uwanmu. Maimakon haka, za mu yi ƙoƙari mu bi Allah ko babu ɗan adam da yake ganinmu. Kamar Dauda na dā, mun ƙuduri aniya: “Da zuciya mai tsabta zan zauna a gidana.”—Zabura 101:2.

15. Ta yaya hulɗa da ’yan’uwanmu maza da mata za ta taimake mu mu ga cewa Jehobah ya kasance da gaske?

15 Jehobah ya fahimci cewa mu ajizai ne, halittu na tsoka kuma ya fahimci cewa wani lokaci zai yi mana wuya mu gaskata abin da ba ma gani. (Zabura 103:14) Ya yi abubuwa da yawa domin ya taimake mu mu magance irin wannan kasawa. Alal misali, ya “keɓe wata jama’a” ta zama tasa daga dukan al’umman duniya. (Ayyukan Manzanni 15:14) Sa’ad da dukanmu muka yi hidima tare, muna samun ƙarfi daga juna. Jin yadda Jehobah ya taimaki ɗan’uwa ko ’yar’uwa ta ruhaniya ta ko ya magance wasu matsaloli ko kuma wasu gwaji yana sa Allahnmu ya kasance gaskiya a gare mu.—1 Bitrus 5:9.

16. Ta yaya koyo game da Yesu zai taimake mu mu yi tafiya da Allah?

16 Mafi duka, Jehobah ya ba mu misalin Ɗansa. Yesu ya ce: “Ni ne hanya, ni ne gaskiya, ni ne kuma rai. Ba mai zuwa wurin Uba sai ta wurina.” (Yahaya 14:6) Nazarin tafarkin rayuwar Yesu a duniya shi ne hanya ɗaya mafi kyau na sa Jehobah ya kasance gaskiya a gare mu. Dukan abin da Yesu ya ce ko ya yi, kwatanci ne na mutuntakar Ubansa na samaniya da kuma hanyoyinsa. (Yahaya 14:9) Sa’ad da muka yanke shawara, muna bukatar mu yi tunani da kyau game da yadda Yesu zai bi da abubuwa. Sa’ad da shawarar mu ta nuna mun yi tunani da kuma addu’a bisa wannan, to muna bin sawun Kristi. (1 Bitrus 2:21) Sanadin haka, muna bin Allah.

Wace Albarka Ce Za a Samu?

17. Idan muka yi tafiya a hanyar Jehobah, wace “hutu” za mu samu ga ranmu?

17 Bin Jehobah Allah rayuwa ce mai albarka. Ka tuna abin da Jehobah ya yi alkawari ga mutanensa game da bin “hanya mai kyau.” Ya ce: “Ku bi ta, don ku hutar da rayukanku.” (Irmiya 6:16) Menene wannan “hutu” take nufi? Rayuwa ce da ta cika da jin daɗi da alamu? A’a. Jehobah yana yin tanadin abu mafi kyau, abin da mafiya dukiya a tsakanin mutane ba sa samu. Samun hutu ga ranka shi ne ka samu kwanciyar rai, farin ciki, gamsuwa, da kuma cika ta ruhaniya. Irin wannan hutu tana nufin kana da tabbacin cewa kana bin hanyar rayuwa mai kyau. Irin wannan kwanciyar rai albarka ce mai wuyar samu a wannan duniya!

18. Wace albarka Jehobah yake so ya ba ka, kuma menene ƙudurinka?

18 Hakika, rayuwa kanta albarka ce mai girma. Gajeriyar tafiya ta fi rashinta. Amma, Jehobah bai nufi tafiyarka ta kasance gajeriya daga ƙuruciya ta samartaka zuwa azaba ta tsufa ba. Jehobah yana so ka sami albarka mafi girma. Yana so ka yi tafiya tare da shi har abada! An furta wannan a Mika 4:5: “Ko da ya ke al’ummai suna bin gumakansu, amma mu za mu bi Ubangiji Allahnmu har abada abadin.” Za ka so ka sami wannan albarkar? Za ka so ka more abin da Jehobah ya kira “rai wanda yake na hakika”? (1 Timoti 6:19) Saboda haka, ka ƙuduri aniyar bin Jehobah a yau, da gobe, da kuma kowace rana bayan haka har abada abadin!

[Hasiya]

a Wasu fassaran Littafi Mai Tsarki sun canja “taƙi” zuwa wasu kalmomin gwaji, kamar su minti. Amma, kalmar ainihi da aka yi amfani da ita tana nufin taƙi, wato mai tsawon inci 18.

Yaya Za Ka Amsa?

• Menene bin Allah yake nufi?

• Me ya sa kake bukatar ka bi Allah?

• Menene zai taimake ka ka bi Allah?

• Wace albarka ce waɗanda suka bi Allah za su samu?

[Hotuna a shafi na 27]

Daga Littafi Mai Tsarki, muna jin muryar Jehobah a bayanmu tana cewa ‘ga hanya’

[Hoto a shafi na 29]

A taro, muna samun abinci a kan kari

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba