WAƘA TA 57
Ku Yi wa Dukan Mutane Wa’azi
(1 Timotawus 2:4)
- 1. Muna so mu yi koyi da Allah, - Shi ba ya nuna wa kowa son kai. - Yana son kowa ya sami ceto, - Yana son kowa ya bauta masa. - (AMSHI) - Muna neman mutane, - Ba ma duba fuskarsu, - Abin da Allah yake so ke nan. - Don yaɗa bisharar nan, - Muna zuwa ko’ina - Don mutane su bauta wa Allah. 
- 2. Za mu yi wa’azi a ko’ina, - Ko da yaya yanayinsu yake. - Halinsu ne ke da muhimmanci, - Jehobah ne ke ganin zucinsu. - (AMSHI) - Muna neman mutane, - Ba ma duba fuskarsu, - Abin da Allah yake so ke nan. - Don yaɗa bisharar nan, - Muna zuwa ko’ina - Don mutane su bauta wa Allah. 
- 3. Jehobah na son dukan mutane, - Su guje wa halin duniyar nan. - Shi ne ya sa muke yin wa’azi, - Ga dukan mutanen da za su ji. - (AMSHI) - Muna neman mutane, - Ba ma duba fuskarsu, - Abin da Allah yake so ke nan. - Don yaɗa bisharar nan, - Muna zuwa ko’ina - Don mutane su bauta wa Allah. 
(Ka kuma duba Yoh. 12:32; A. M. 10:34; 1 Tim. 4:10; Tit. 2:11.)