ABIN DA KE SHAFIN FARKO | DON ME MASIFU SUKE FAƊA WA MUTANEN KIRKI?
Abin da Allah Zai Yi Game da Munanan Abubuwa
Littafi Mai Tsarki ya bayyana matakin da Jehobah da Ɗansa Yesu Kristi za su ɗauka a kan wahalar da Shaiɗan Iblis ya jawo. Ya ce: “Dalilin bayyanuwar Ɗan Allah [Yesu] ke nan, ya halaka [‘kawar da,’ New World Translation] ayyukan Shaiɗan.” (1 Yohanna 3:8) Hakika, za a kawar da wannan zamanin da mutane suka dulmaya cikin haɗama da ƙiyayya da kuma ƙeta. Sa’an nan Yesu ya ce “za a fitar” da Shaiɗan Iblis, “mai-mulkin wannan duniya.” (Yohanna 12:31) Za a yi sabuwar duniya inda Shaiɗan ba zai yi tasiri ba, kuma hakan zai sa salama ta kasance.—2 Bitrus 3:13.
Me zai faru da waɗanda suka ƙi gyara rayuwarsu kuma suka ci gaba da yin munanan abubuwa? Ka yi tunani a kan wannan alkawarin: “Masu-adalci za su zauna cikin ƙasan, kamilai kuma za su wanzu a cikinta. Amma za a datse miyagu daga cikin ƙasan, za a tumɓuke masu-cin amana kuma.” (Misalai 2:21, 22) Miyagu ba za su sake yin tasiri a kan mutane ba. A wannan yanayin, ’yan Adam masu biyayya za su ’yantu a hankali daga zunubin da suka gāda.—Romawa 6:17, 18; 8:21.
Ta yaya Allah zai kawar da mugunta daga sabuwar duniyar? Ba zai yi hakan ta wajen ƙwace ’yancin yin zaɓe daga ’yan Adam don su zama kamar na’urori ba. A maimakon haka, Allah zai koya wa masu biyayya tafarkunsa kuma hakan zai taimaka musu su rabu da mugun tunani da kuma munanan ayyuka.
Allah zai kawar da dukan sanadin wahala
Mene ne Allah zai yi game da tsautsayi? Ya yi alkawari cewa ba da daɗewa ba Mulkinsa zai mallaki duniya. Yesu Kristi ne Sarkin da Allah ya naɗa kuma yana da ikon warkarwa. (Matta 14:14) Ƙari ga haka, Yesu yana da iko ya hana abubuwa kamar su iska da kuma ruwa yin ɓarna. (Markus 4:35-41) Saboda haka, za a rabu da wahalar da ake sha sakamakon “sa’a, da tsautsayi.” (Mai-Wa’azi 9:11, Littafi Mai Tsarki) A lokacin sarautar Kristi, babu wata masifar da za ta faɗa wa ’yan Adam.—Misalai 1:33.
Miliyoyin mutane da suka mutu sanadin munanan haɗarurruka kuma fa? Ba da daɗewa ba kafin Yesu ya ta da abokinsa Li’azaru daga mutuwa, ya ce: “Ni ne tashin matattu, ni ne rai.” (Yohanna 11:25) Hakan ya nuna cewa Yesu yana da ikon ta da matattu!
Idan kana so ka zauna a duniyar da munanan abubuwa ba za su faɗa wa mutanen kirki ba, ka ƙoƙarta ka yi nazarin Littafi Mai Tsarki don ka daɗa sanin Allah da kuma nufinsa. Shaidun Jehobah da ke yankinku za su ji daɗin taimaka maka ka yi hakan. Muna ƙarfafa ka ka tuntuɓe su ko kuma ka rubuta wasiƙa zuwa ga mawallafan wannan mujallar.