Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • th darasi na 9 p. 12
  • Ka Yi Amfani da Abubuwan da Ake Gani

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ka Yi Amfani da Abubuwan da Ake Gani
  • Ka Mai da Hankali Ga Karatu da Kuma Koyarwa
  • Makamantan Littattafai
  • Ka Yi Amfani da Bidiyoyi don Ka Koyar da Dalibanka
    Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2019
  • Ka Koyi Darasi Daga Hotuna
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2025
  • Hanyoyin Kyautata Yadda Muke Wa’azi—Yin Amfani da Bidiyoyi don Koyarwa
    Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu (2016)
  • Maganarka ta Ratsa Zuciya
    Ka Mai da Hankali Ga Karatu da Kuma Koyarwa
Ka Mai da Hankali Ga Karatu da Kuma Koyarwa
th darasi na 9 p. 12

DARASI NA 9

Ka Yi Amfani da Abubuwan da Ake Gani

Nassin da aka rubuta

Farawa 15:5

ABIN DA ZA KA YI: Ka yi amfani da abubuwan da ido ke gani don a fahimci muhimman darussa da kake son masu sauraronka su tuna da su.

YADDA ZA KA YI HAKAN:

  • Ka zaɓi abubuwan da ake gani da za su sa koyarwarka ta yi kyau. Ka yi amfani da hotuna ko zane ko taswira don ka fitar da muhimman darussa. Ka taimaka wa masu sauraronka su fahimci ainihin darasin da ka koya musu ba kawai abin da suka gani ba.

  • Ka tabbata cewa masu sauraronka suna ganin abin da kake misali da shi.

    Shawara mai amfani

    Tun kafin ka soma tattaunawar, ka tabbata cewa duk wani abin da kake son ka yi misali da shi yana nan a shirye.

SA’AD DA KAKE WA’AZI

Ka jawo hankalin mai sauraronka ga hotuna ko zanen da ke cikin littattafanmu, kuma ka sa ya yi kalami a kan abin da ya gani. Idan da bukata, ka yi ƙarin tambayoyi don ka nanata muhimman darussa. Idan kana nuna bidiyo ga masu sauraronka, ka juya na’urar yadda za su iya ganin abin da ke cikin bidiyon. Ka tuna cewa ba ka bukatar ka yi magana a lokacin da kake nuna musu bidiyon.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba