Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • mwb19 Maris p. 7
  • Ka Yi Amfani da Bidiyoyi don Ka Koyar da Dalibanka

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ka Yi Amfani da Bidiyoyi don Ka Koyar da Dalibanka
  • Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2019
  • Makamantan Littattafai
  • Hanyoyin Kyautata Yadda Muke Wa’azi—Yin Amfani da Bidiyoyi don Koyarwa
    Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu (2016)
  • Ku Yi Amfani da Bidiyo Wajen Koyarwa
    Hidimarmu Ta Mulki—2013
  • Bitar Sashe na 2
    Ka Ji Dadin Rayuwa Har Abada!​—Don Nazarin Littafi Mai Tsarki
  • Ku Yi Amfani da Ka Ji Daɗin Rayuwa Har Abada! a Wa’azi
    Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2021
Dubi Ƙari
Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2019
mwb19 Maris p. 7
Wata ’yar’uwa tana nuna ma dalibarta bidiyo

RAYUWAR KIRISTA

Ka Yi Amfani da Bidiyoyi don Ka Koyar da Ɗalibanka

Abubuwan da mutum ya gani suna jawo hankalinsa kuma suna taimaka masa ya tuna abubuwan da ya koya. Jehobah wanda shi ne Malami Mafi Girma ma ya yi amfani da abin da ake gani don ya koyar da darussa masu muhimmanci. (Fa 15:5; Irm 18:​1-6) Yesu, Babban Malami, ma ya yi hakan. (Mt 18:​2-6; 22:​19-21) A ’yan shekarun nan, ɗaya daga cikin abubuwan da ke jan hankalin mutane sa’ad da muke wa’azi shi ne bidiyonmu. Kana yin amfani da bidiyo sosai sa’ad da kake koyar da ɗalibanka?

An shirya bidiyoyi guda goma da za su taimaka mana mu koyar da darussan da ke ƙasidar nan Albishiri Daga Allah! Kowanne bidiyon ya amsa ɗaya daga cikin tambayoyin da ke ƙasidar. A ƙasidar da ke dandalinmu na jw.org/ha, an saka bidiyoyin don ka san lokacin da ya kamata ka nuna kowannensu. Ƙari ga haka, akwai wasu bidiyoyi kuma da suke yin ƙarin haske a kan wasu littattafan da muke wa’azi da su.

Shin kuna tattauna wani batu da zai yi ma ɗalibinka wuyar fahimta? Ko kuma ɗalibinka yana fama da wata matsala? Ka bincika bidiyoyin da ke jw.org® da JW Broadcasting® na Hausa a jw.org/ha da Tashar JW don ka ga wanda zai taimaka masa. Za ku iya kalli ɗaya daga cikinsu tare kuma ku tattauna shi.

A kowane wata, mukan fitar da sabbin bidiyoyi. Yayin da kake kallon su, ka yi tunani a kan yadda za ka yi amfani da su sa’ad da kake koyar da ɗalibinka.

BIDIYOYIN DA SUKA YI ƘARIN BAYANI A KAN DARUSSAN DA KE ƘASIDAR NAN ALBISHIRI DAGA ALLAH!

  • Bidiyon nan Allah yana da suna ne?

    Darasi na 2

    Allah Yana da Suna Ne?

  • Bidiyon nan Wane ne mawallafin Littafi Mai Tsarki?

    Darasi na 3

    Wane ne Mawallafin Littafi Mai Tsarki?

  • Bidiyon nan Ta Yaya Muka San Cewa Abin da Ke Littafi Mai Tsarki Gaskiya Ne?

    Ta Yaya Muka San Cewa Abin da Ke Littafi Mai Tsarki Gaskiya Ne?

  • Bidiyon nan Me Ya Sa Yesu Ya Mutu?

    Darasi na 4

    Me Ya Sa Yesu Ya Mutu?

  • Bidiyon nan Me Ya Sa Allah Ya Halicci Duniya?

    Darasi na 5

    Me Ya Sa Allah Ya Halicci Duniya?

  • Bidiyon nan Wane Yanayi Ne Matattu Suke Ciki?

    Darasi na 6

    Wane Yanayi Ne Matattu Suke Ciki?

  • Bidiyon nan Mene ne Mulkin Allah

    Darasi na 7

    Mene ne Mulkin Allah?

  • Bidiyon nan Me Ya Sa Allah Ya Kyale Mutane Su Sha Wahala?

    Darasi na 8

    Me Ya Sa Allah Ya Ƙyale Mutane Su Sha Wahala?

  • Bidiyon nan Allah Yana Amince da Dukan Addinai Kuwa?

    Darasi na 10

    Allah Yana Amince da Dukan Addinai Kuwa?

  • Bidiyon nan Allah Yana Amsa Dukan Addu’o’i Kuwa?

    Darasi na 12

    Allah Yana Amsa Dukan Addu’o’i Kuwa?

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba