Yadda Za Ka Nuna Halin Sadaukarwa
“Idan kowane mutum yana da nufi shi bi bayana, sai shi yi musun kansa.”—MAT. 16:24.
1. Ta yaya Yesu ya kafa mana misali mai kyau na yin sadaukarwa?
YESU ya kafa mana misali mai kyau na yin sadaukarwa sa’ad da yake duniya. Ya saka yin nufin Allah da farko maimakon nasa. (Yoh. 5:30) Yesu ya kasance da aminci har mutuwa a kan gungumen azaba, kuma ta hakan, ya nuna cewa yana da halin sadaukarwa sosai.—Filib. 2:8.
2. Ta yaya za mu yi sadaukarwa, kuma me ya sa za mu yi hakan?
2 A matsayin mabiyan Yesu, ya kamata mu riƙa nuna halin sadaukarwa. Mene ne yin hakan yake nufi? Hakan yana nufin cewa mutum yana a shirye ya ba da kansa a kowane lokaci domin ya taimaka wa wasu. A taƙaice, hakan yana nufin nuna rashin son kai. (Karanta Matta 16:24) Rashin son kai zai taimaka mana mu saka bukatun wasu da farko kafin namu. (Filib. 2:3, 4) Hakika, Yesu ya nuna cewa rashin son kai yana da muhimmanci sosai a bautarmu. Ta yaya? Ƙauna ta Kirista tana motsa mu mu yi sadaukarwa kuma an san mabiyan Yesu na gaske da wannan halin. (Yoh. 13:34, 35) Kuma ka yi tunanin irin albarkar da muke samu domin muna bauta wa Jehobah tare da ’yan’uwanmu a faɗin duniya da suke yin sadaukarwa!
3. Mene ne zai iya hana mu nuna halin sadaukarwa?
3 Amma akwai wani abu da zai iya hana mu nuna halin sadaukarwa. Wannan abin shi ne halin son kai. Ka yi tunanin yadda Adamu da Hawwa’u suka nuna son kai. Hawwa’u ta nuna son kai ta wurin so ta zama kamar Allah. Ta wajen faranta ran matarsa, Adamu ma ya nuna halin son kai. (Far. 3:5, 6) Bayan Shaiɗan ya sa Adamu da Hawwa’u suka daina bauta wa Allah, ya ci gaba da ƙoƙarin sa mutane su riƙa nuna son kai. Har ma ya yi ƙoƙarin sa Yesu ya nuna son kai. (Mat. 4:1-9) A yau, Shaiɗan ya yaudari mutane da yawa don ya sa su zama masu son kai. Saboda haka, ya kamata mu mai da hankali sosai don kada halin son kai ya shafe mu.—Afis. 2:2.
4. (a) Shin za mu iya guje wa son kai gaba ɗaya yanzu kuwa? Ka bayyana. (b) Waɗanne tambayoyi ne za mu tattauna?
4 Son kai yana kama da tsatsa a jikin ƙarfe. Ƙarfe zai iya fara yin tsatsa idan ruwa ya taɓa shi. Idan ba a kankare tsatsar ba, za ta iya cinye ƙarfen. Hakazalika, ba za mu iya guje wa ajizanci da son kai kwata-kwata yanzu ba, amma wajibi ne mu san hadarin da suke haddasawa kuma mu riƙa yin iya ƙoƙarinmu don mu guje musu. (1 Kor. 9:26, 27) Ta yaya za mu iya sani ko muna son kai? Kuma ta yaya za mu ci gaba da nuna halin sadaukarwa?
KA YI AMFANI DA LITTAFI MAI TSARKI DON BINCIKA KO KANA SON KAI
5. (a) Ta yaya Littafi Mai Tsarki yake kama da madubi? (Ka duba hoton da ke shafi na 7.) (b) Mene ne ya kamata mu guje wa sa’ad da muke yin amfani da Littafi Mai Tsarki don bincika kanmu?
5 Kamar yadda muke yin amfani da madubi domin mu duba fuskarmu, za mu iya yin amfani da Littafi Mai Tsarki don duba abin da ke cikin zuciyarmu kuma mu yi gyara a inda ya dace. (Karanta Yaƙub 1:22-25.) Hakika, za mu iya ganin kanmu da kyau idan muka yi amfani da madubin da kyau. Alal misali, ba za mu iya ganin dattin da ke fuskarmu ba idan muka ɗan kalli kanmu kawai a madubi. Ko kuma idan muka tsaya a gefe muka kalli madubin, za mu iya ganin wani dabam. Hakazalika, dole mu yi amfani da Littafi Mai Tsarki da kyau don mu bincika kanmu kuma mu guji yin amfani da shi don mu ga kurakuran wasu.
6. Ta yaya za mu “lizima” a cikin cikakkiyar shari’a?
6 Alal misali, zai yiwu mu riƙa karanta Littafi Mai Tsarki kullayaumi, amma mu kasa sanin ko muna son kai. Ta yaya hakan zai yiwu? Ka yi la’akari da kwatancin madubi da ke littafin Yaƙub. Yaƙub ya ce mutumin ‘ya duba kansa.’ A nan Yaƙub ya yi amfani da kalmar Helenawa da yake nufin bincikawa a hankali. Amma mene ne matsalar da mutumin yake da shi? Yaƙub ya ci gaba da cewa: “Kāna ya tafi, nan da nan kuwa ya manta irin mutum da ya ke.” Mutumin ya tafi ba tare da gyara abin da ya gani a jikinsa ba. Amma, mutumin da ya amfana shi ne wanda ya “duba cikin cikakkiyar shari’a” kuma “ya lizima.” Maimakon ya manta da cikakkiyar shari’ar ta Kalmar Allah, ya lizima a cikinta, wato ya bi koyarwarta. Yesu ya yi irin wannan furucin sa’ad da ya ce: “Idan kun zauna cikin maganata, ku ne almajiraina na gaske.”—Yoh. 8:31.
7. Ta yaya za mu yi amfani da Littafi Mai Tsarki don mu bincika ko muna da son kai?
7 Saboda haka, idan kana son ka kawar da son kai, da farko zai dace ka karanta Kalmar Allah cikin natsuwa. Hakan zai taimaka maka ka ga wuraren da ya kamata ka yi gyara. Kada ka tsaya a nan, amma ka ci gaba da bincike kuma yayin da kake karanta wani labari a Littafi Mai Tsarki, ka saka kanka a yanayin, kuma ka tambayi kanka: ‘Da a ce ni ne, da mene ne zan yi a wannan yanayin? Shin, da na bi da yanayin a hanyar da ta dace kuwa? Bayan ka yi bimbini a kan abin ka karanta sai ka yi amfani da shi. (Mat. 7:24, 25) Bari mu bincika yadda misalan Sarki Saul da manzo Bitrus za su iya taimaka mana mu kasance da halin sadaukarwa.
KA KOYI DARASI DAGA LABARIN SARKI SAUL
8. Wane irin hali ne Sarki Saul ya nuna sa’ad da ya soma sarauta, kuma ta yaya ya yi hakan?
8 Labarin Sarki Saul ya koya mana darasi cewa halin son kai zai iya shawo kan halin sadaukarwa. Sarki Saul mutumi ne mai tawali’u da kuma filako a lokacin da ya soma sarautarsa. (1 Sam. 9:21) Bai yi wa mutanen Isra’ila da suka yi gunaguni game da sarautarsa horo ba ko da yake yana da ikon yin haka. (1 Sam. 10:27) Sarki Saul ya bi ja-gorar ruhun Allah a yin yaƙi da Ammonawa kuma ya yi nasara. Bayan haka, sai ya girmama Jehobah don nasarar da ya yi.—1 Sam. 11:6, 11-13.
9. Ta yaya Sarki Saul ya soma nuna son kai?
9 Ba da daɗewa ba, Sarki Saul ya ƙyale halin son kai ta kasance a zuciyarsa, kamar tsatsa. Bayan da ya yi nasara a kan Amalakawa, sai ya bi muradin zuciyarsa maimakon ya yi biyayya ga Jehobah. Ya kwashi ganima maimakon ya halaka kome da kome kamar yadda Jehobah ya umurce shi. Kuma da fahariya ya kafa wa kansa umudi. (1 Sam. 15:3, 9, 12) Sa’ad da Sama’ila ya gaya wa Sarki Saul cewa Jehobah bai ji daɗin abin da ya yi ba, sai ya ba da hujja kuma ya nanata dokar Allah da ya bi ya kuma ɗora alhaki a kan wasu mutane dabam. (1 Sam. 15:16-21) Ƙari ga haka, girman kai ya sa Sarki Saul ya nemi suna a gaban mutane maimakon yin biyayya ga Allah. (1 Sam. 15:30) Ta yaya za mu iya yin amfani da labarin Saul kamar madubin da zai taimaka mana mu kasance da halin sadaukarwa?
10, 11. (a) Mene ne labarin Saul ya koya mana game da kasancewa da halin sadaukarwa? (b) Ta yaya za mu guji bin misali marar kyau da Saul ya kafa?
10 Da farko, labarin Saul ya koya mana cewa bai kamata mu ɗauka cewa da yake mun nuna halin sadaukarwa a dā, za mu ci gaba da yin hakan ba. (1 Tim. 4:10) Ka tuna cewa da farko, Saul ya yi abubuwa masu kyau kuma Jehobah ya yi masa alheri, amma daga baya sai ya ƙyale son kai ta kasance a zuciyarsa. Hakan ya sa Jehobah ya ƙi shi don rashin biyayyar da ya yi.
11 Na biyu kuma shi ne, bai kamata mu riƙa mai da hankali ga abubuwa masu kyau da muke yi kaɗai ba, amma muna bukata mu lura da wuraren da muke bukatar gyara. Wannan zai iya zama kamar mutum da yake yin amfani da madubi don ya kalli sabon rigar da ya saya, maimakon share dattin da yake fuskarsa. Ko da a ce ba mu da fahariya kamar Saul ba, ya kamata mu guje wa dukan wani abin da zai sa mu bin misalinsa marar kyau. Sa’ad da aka yi mana gargaɗi, kada mu ba da hujja ko kuwa mu ɗora wa wasu laifin da muka yi. Maimakon haka, zai fi kyau mu karɓi gargaɗin.—Karanta Zabura 141:5.
12. Ta yaya halin sadaukarwa zai iya taimaka mana a lokacin da muka yi zunubi mai tsanani?
12 Idan muka yi wani zunubi mai tsanani fa? Saul ya yi ƙoƙarin ɓoye laifin da ya yi don son girma kuma hakan ya sa bai gyara dangantakarsa da Allah ba. (Mis. 28:13; Yaƙ. 5:14-16) Alal misali, akwai wani ɗan’uwa da ya soma kallon hotunan batsa tun da yake shekara 12, kuma ya yi sama da shekaru goma yana yin haka. Ya ce: “Ya yi mani wuya na gaya wa matata da kuma dattawa abin da nake yi. Amma yanzu da na gaya musu, na ji kamar an sauke mini wani kaya mai nauyi. Ko da yake wasu abokaina ba su ji daɗi cewa an sauke ni daga yin hidima a matsayin bawa mai hidima ba, amma ina da tabbaci cewa Jehobah ya amince da bauta ta yanzu fiye da dā.”
BITRUS YA SHAWO KAN SON KAI
13, 14. Ta yaya Bitrus ya nuna son kai?
13 Manzo Bitrus ya nuna halin sadaukarwa sa’ad da yake tare da Yesu. (Luk 5:3-11) Duk da haka, ya yi fama da nuna son kai. Alal misali, Bitrus ya ji haushi sa’ad da Yaƙub da Yohanna suka roƙi Yesu ya ba su wani matsayi mai girma a Mulkin Allah. Wataƙila Bitrus ya yi tunanin cewa shi ne ya kamata ya zauna a hannun damar Yesu, da yake Yesu ya riga ya gaya masa cewa zai kasance da matsayi na musamman. (Mat. 16:18, 19) Yesu ya gaya wa dukan manzannin haɗe da Yaƙub da Yohanna da kuma Bitrus cewa kada su ƙyale son kai ya sa su nuna “iko” bisa ’yan’uwansu.—Mar. 10:35-45.
14 Bayan da Yesu ya gyara tunanin Bitrus, bai daina nuna son kai ba. A lokacin da Yesu ya gaya wa manzanninsa cewa za su gudu su bar shi, Bitrus ya sa su ji kamar ya fi su adalci kuma ya ce idan sauran za su bar Yesu, shi ba zai taɓa barin sa ba. (Mat. 26:31-33) Amma a cikin daren da Bitrus ya yi wannan maganar, ya kasa nuna halin sadaukarwa domin ya dogara ga kansa. Da yake yana son ya kāre kansa, sai ya yi musun sanin Yesu sau uku.—Mat. 26:69-75.
15. Me ya sa misalin da Bitrus ya kafa a dukan rayuwarsa misali ne mai kyau?
15 Duk da kasawarsa, Bitrus ya kafa mana misali mai kyau. Bitrus ya yi ƙoƙari kuma tare da taimakon ruhu mai tsarki, ya canja tunaninsa kuma ya nuna kamewa da ƙauna da kuma sadaukarwa. (Gal. 5:22, 23) Ya jimre da gwaje-gwaje da suka fi waɗanda ya fuskanta a lokacin da Yesu yake duniya. Ya nuna tawali’u ta yin shiru sa’ad da manzo Bulus ya tsawata masa a fili. (Gal. 2:11-14) Kuma Bitrus bai riƙe Bulus a zuci ba, amma ya ci gaba da ƙaunarsa. (2 Bit. 3:15) Misalin Bitrus zai sa mu kasance da halin sadaukarwa.
16. Ta yaya za ka iya nuna halin sadaukarwa a lokacin da kake fuskantar yanayi mai wuya?
16 Wane mataki ne kake ɗauka a yanayi mai wuya? A lokacin da aka kama Bitrus da sauran manzanni aka yi musu bulala kuma aka jefa su cikin fursuna don wa’azin da suke yi, sun yi murna “sun isa su sha wulaƙanci saboda sunan Yesu.” (A. M. 5:41) Kai ma za ka iya yin koyi da Bitrus kuma ka bi misalin da Yesu ya kafa a nuna halin sadaukarwa sa’ad da ka fuskanci tsanantawa. (Karanta 1 Bitrus 2:20, 21.) Irin wannan halin zai taimaka maka sa’ad da dattawa suka yi maka horo. Ka bi misalin Bitrus maimakon ka ɓata rai.—M. Wa. 7:9.
17, 18. (a) Waɗanne tambayoyi ne za mu yi wa kanmu a kafa maƙasudan da suka shafi bautarmu? (b) Mene ne za mu iya yi idan muka lura cewa muna son kai?
17 Za ka iya amfana daga misalin Bitrus a biɗan maƙasudan da za su iya ƙarfafa dangantakarka da Allah. Za ka iya biɗan su a hanyar da za ta nuna cewa kana da halin sadaukarwa. Duk haka, zai dace ka mai da hankali don kada neman girma ya sa ka biɗan waɗannan maƙasudan. Saboda haka, za ka iya tambayar kanka, ‘Neman girma ne ya sa ina son in daɗa ƙwazo a hidimata ga Jehobah kamar yadda Yaƙub da Yohanna suka yi?’
18 Idan ka lura cewa kana da halin son kai, ka roƙi Jehobah ya gyara tunaninka kuma ka girmama shi maimakon neman suna. (Zab. 86:11) Za ka iya biɗan maƙasudan da za su sa ka kasance da tawali’u. Alal misali, za ka iya nuna hali na ’yar ruhu da yake maka wuyar nunawa. Ko kuwa za ka iya saka hannu a share Majami’ar Mulki idan ba ka yin hakan a dā. Ƙari ga haka, za ka iya bin shawarar da aka rubuta a littafin Romawa 12:16.—Karanta.
19. Me ya kamata mu yi idan binciken da muka yi a Kalmar Allah da ke kama da madubi ya sa mu sanyin gwiwa?
19 Za mu iya yin sanyin gwiwa bayan mun yi amfani da Kalmar Allah da ke kama da madubi don bincika kanmu kuma muka ga kurakuran da muke da shi ko kuma halin son kai. Idan hakan ya faru da kai, ka yi tunanin yadda mutumin da aka kwatanta a littafin Yaƙub ya yi nasara. Yaƙub bai nuna ko mutumin ya yi gyarar nan da nan ba, amma ya ce ya ci gaba da bin “cikakkiyar shari’a.” (Yaƙ. 1:25) Mutumin ya tuna da matsalar da yake da shi kuma ya ci gaba da yin gyara. Ka kasance da ra’ayi mai kyau game da kanka kuma ka tuna cewa dukanmu ajizai ne. (Karanta Mai-Wa’azi 7:20.) Jehobah yana a shirye ya taimaka maka kamar yadda ya taimaka wa wasu ’yan’uwa da su ma ajizai ne. Idan ka bi koyarwar Littafi Mai Tsarki kuma ka ci gaba da yin sadaukarwa, Jehobah zai albarkace ka kuma zai amince da kai.