Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • Jehobah “Mai-bayyana Asirai” Ne
    Hasumiyar Tsaro—2012 | 15 Yuni
    • Jehobah “Mai-bayyana Asirai” Ne

      “Hakika Allahnka shi ne Allah na allohi, Ubangijin sarakuna kuwa, mai-bayyana asirai.”—DAN. 2:47.

      MECE CE AMSARKA?

      Waɗanne abubuwa da za su faru a nan gaba ne Jehobah ya bayyana mana?

      Mene ne kai na ɗaya zuwa shida na dabbar yake wakilta?

      Wace nasaba ce ke tsakanin dabbar da kuma sifar da Sarki Nebuchadnezzar ya gani?

      1, 2. Mene ne Jehobah ya bayyana mana, kuma me ya sa ya yi hakan?

      WACE mulki ce za ta riƙa sarauta a duniya sa’ad da Mulkin Allah zai kawo ƙarshe ga sarautar ’yan Adam? Mun san amsar domin Jehobah Allah, “Mai-bayyana asirai” ne. Kuma ya bayyana mana wannan asiran ta littattafan da annabi Daniyel da manzo Yohanna suka rubuta.

      2 Jehobah ya saukar wa Daniyel da Yohanna wahayi da yawa game da dabbobin. Ya kuma bayyana wa Daniyel ma’anar wani mafarkin da ya yi game da wani babban gunki na ƙarfe. Jehobah ya sa an rubuta kuma an adana waɗannan abubuwan a cikin Littafi Mai Tsarki don amfaninmu. (Rom. 15:4) Ya yi hakan don ya sa mu kasance da bege cewa nan ba da daɗewa ba, Mulkin Allah zai halaka dukan mulkokin ’yan Adam.—Dan. 2:44.

      3. Idan muna son mu fahimci wannan annabcin sosai, mene ne ya kamata mu fara fahimta kuma me ya sa?

      3 Annabce-annabcen da Daniyel da kuma Yohanna suka rubuta sun bayyana abubuwa game da sarakai takwas ko kuma sarautar ’yan Adam da kuma yadda za su soma sarauta ɗaya bayan ɗaya. Amma, idan muna son mu fahimci waɗannan annabce-annabcen, wajibi ne mu fahimci ma’anar annabci na farko da ke cikin Littafi Mai Tsarki. Me ya sa? Domin Littafi Mai Tsarki gabaki ɗaya da kuma annabce-annabcen da ke cikinsa suna da nasaba da wannan annabcin. Shi ne tushen dukan annabce-annabcen da ke cikin Littafi Mai Tsarki.

      ZURIYAR MACIJIN DA DABBAR

      4. Su wane ne sashen wannan zuriyar kuma mene ne zuriyar za ta yi?

      4 Ba da daɗewa ba bayan Adamu da Hauwa’u sun yi rashin biyayya a gonar Adnin, Jehobah ya yi alkawari cewa wata ‘mace’ za ta haifi ‘zuriya.’a (Karanta Farawa 3:15.) Zuriyar za ta ƙuje kan macijin, wato, Shaiɗan. Daga baya, Jehobah ya bayyana cewa zuriyar za ta taho daga Ibrahim ta al’ummar Isra’ila daga kabilar Yahuda kuma daga iyalin Dauda. (Far. 22:15-18; 49:10; Zab. 89:3, 4; Luk 1:30-33) Kuma Yesu ne ainihin wannan zuriyar. (Gal. 3:16) Ikilisiyar shafaffu ita ce sashe na biyu na wannan zuriyar. (Gal. 3:26-29) Yesu da shafaffu ne suka kafa Mulkin Allah. Kuma Allah zai yi amfani da su wajen halaka Shaiɗan.—Luk 12:32; Rom. 16:20.

      5, 6. (a) Gwamnatoci masu iko nawa ne Daniyel da Yohanna suka bayyana? (b) Mene ne kawunan dabbar da aka ambata a Ru’ya ta Yohanna suke wakilta?

      5 A wannan annabci na farko da Jehobah ya ba da a gonar Adnin, ya ce Shaiɗan zai haifi ‘zuriya.’ Zuriyarsa za ta yi magabtaka da zuriyar macen. Su waye ne zuriyar macijin? Dukan waɗanda suka tsane Jehobah kuma suke tsananta wa bayin Allah kamar yadda Shaiɗan yake yi. Da daɗewa, Shaiɗan ya tsara zuriyarsa zuwa gwamnatoci dabam-dabam. (Luk 4:5, 6) Amma dai, ƙalilan ne cikin waɗannan gwamnatocin suka yi tsayayya da mutanen Allah, wato, al’ummar Isra’ila da Kiristoci shafaffu. Hakan ya taimaka mana mu fahimci dalilin da ya sa wahayin Daniyel da Yohanna suka ambata gwamnatoci takwas masu iko ko da yake sun fi takwas.

      6 Yesu ya sauko wa da Yohanna wahayi mai ban mamaki kusan shekara dubu biyu da suka shige. (R. Yoh. 1:1) A ɗaya cikin wahayin, Yohanna ya ga Iblis wanda aka nuna kamar babban maciji yana tsaye a bakin teku. (Karanta Ru’ya ta Yohanna 13:1, 2.) Yohanna ya kuma ga wata irin dabba tana fitowa daga cikin teku. Tana da kawuna bakwai kuma ta karɓi iko sosai daga wurin Iblis. Daga baya, Yohanna ya ga wata dabba ja wur kuma tana da kawuna bakwai. Wannan ita ce gunkin babbar dabbar da aka ambata a littafin Ru’ya ta Yohanna 13:1. Wani mala’ika ya gaya wa Yohanna cewa kawuna bakwai na dabbar ja wur tana nufin “sarakuna bakwai” ko gwamnati. (R. Yoh. 13:1, 14, 15; 17:3, 9, 10) Sa’ad da Yohanna ya rubuta littafin Ru’ya ta Yohanna, sarakuna biyar sun riga sun gama mulkinsu, ɗaya ne yake mulki a lokacin kuma ɗayan da ya rage “bai zo ba tukuna.” Su waye ne waɗannan gwamnatocin? Bari mu tattauna kowane cikin waɗannan kawunan dabbar da aka ambata a littafin Ru’ya ta Yohanna. Za mu kuma koyi abubuwa da yawa game da waɗannan gwamnatocin a littafin Daniyel. Annabce-annabcen Daniyel sun ba da bayani dalla-dalla game da wasu gwamnatoci darurruwan shekaru kafin su soma sarauta.

      MASAR CE KAI NA FARKO, NA BIYU KUMA ASSURIYA

      7. Mene ne kai na farko yake wakilta kuma me ya sa?

      7 Kai na farko na dabbar yana wakiltar ƙasar Masar domin ita ce farkon gwamnatin da ta tsani mutanen Allah. Allah ya yi wa Ibrahim alkawari cewa shi ne zai haifi zuriyar macen. Kuma Isra’ilawa ’ya’yan Ibrahim ne. Bayan sun ƙaura zuwa ƙasar Masar kuma suka mamaye ƙasar sosai, Masarawa suka soma wulakanta su. Shaiɗan ya yi ƙoƙari ya halaka mutanen Allah kafin a haifi zuriyar. Ta yaya ya yi hakan? Ta wajen sa Fir’auna ya yi ƙoƙarin kashe dukan ’ya’ya maza na Isra’ilawa. Amma, Jehobah bai ƙyale hakan ya faru ba kuma ya ’yantar da mutanensa daga ƙasar Masar. (Fit. 1:15-20; 14:13) Daga baya, ya sa Isra’ilawa suka gāji Ƙasar Alkawari.

      8. Mene ne kai na biyu yake wakilta kuma me ya yi ƙoƙari ya yi?

      8 Kai na biyu na dabbar yana wakiltar ƙasar Assuriya. Wannan gwamnati mai iko sosai ta yi ƙoƙarin halaka mutanen Allah. Jehobah ya yi amfani da Assuriyawa don yi wa ƙabila goma na Isra’ila horo. Ya yi hakan domin Isra’ilawa sun bauta wa gumaka kuma sun yi tawaye da Allah. Amma dai, Assuriyawa suka nemi su halaka Urushalima. Wataƙila Shaiɗan ya yi ƙoƙari ya halaka iyalan sarakai a Urushalima domin ya san cewa Yesu zai fito daga wannan iyalin. Jehobah ba ya son a halaka Urushalima. Saboda haka, ya halaka rundunar Assuriyawa kuma ya cece mutanensa.—2 Sar. 19:32-35; Isha. 10:5, 6, 12-15.

      BABILA CE KAI NA UKU

      9, 10. (a) Mene ne Jehobah ya ƙyale Babiloniyawa su yi? (b) Mene ne ya kamata ya faru kafin wannan annabcin ya cika?

      9 Kai na uku na dabbar da Yohanna ya gani yana wakiltar mulkin Babila. Jehobah ya ƙyale Babiloniyawa su halaka Urushalima kuma ta kai mutanen birnin bauta. Amma, tun kafin hakan ya faru, Jehobah ya riga ya yi wa Isra’ilawa gargaɗi cewa hakan zai faru. (2 Sar. 20:16-18) Jehobah ya gaya wa Isra’ilawa cewa ba zai ƙyale sarakansu su zauna a bisa “kursiyin” Jehobah a Urushalima ba. (1 Laba. 29:23) Amma dai, Jehobah ya sake yin alkawari cewa zuriyar Sarki Dauda, wanda yake da isa zai zo ya yi sarauta.—Ezek. 21:25-27.

      10 Wani annabci ya nuna cewa Yahudawa za su riƙa yin bauta a haikali na Urushalima sa’ad da Almasihun da aka yi alkawarinsa zai zo. (Dan. 9:24-27) Kuma kafin a kai Isra’ilawa bauta a Babila, wani annabci ya ce za a haifi Almasihu a Bai’talami. (Mi. 5:2) Idan Yahudawa ba su fita daga Babila ba, sun koma ƙasarsu kuma sun sake gina haikalin, wannan annabcin ba zai cika ba. Amma, haram ne Babiloniyawa su saki waɗanda suka kai bauta a ƙasarsu. Yaya mutanen za su iya koma ƙasarsu? Jehobah ya bayyana wa annabawa amsar.—Amos 3:7.

      11. A wace hanyoyi dabam-dabam ne aka bayyana sarautar Babila? (Ka duba hasiya.)

      11 Annabi Daniyel yana cikin waɗanda aka kama zuwa Babila. (Dan. 1:1-6) Jehobah ya yi amfani da Daniyel don bayyana cewa akwai wasu gwamnatoci da za su yi sarauta bayan Babila. Jehobah ya yi amfani da alamomi da yawa don annabta abin da zai faru. Alal misali, ya sa Sarkin Babila Nebuchadnezzar ya yi mafarkin wani babbar sifa da aka ƙera ta da abubuwa dabam-dabam. (Karanta Daniyel 2:1, 19, 31-38.) Jehobah ya yi amfani da Daniyel don bayyana cewa sifar da ke da kan zinariya tana wakiltar mulkin Babila.b Ƙirjinta da hannuwanta na azurfa suna wakiltar gwamnatin da za ta yi sarauta bayan faɗuwar Babila. Wace ƙasa ce wannan?

      MIDIYA DA FARISA NE KAI NA HUƊU

      12, 13. (a) Mene ne Jehobah ya bayyana game da yadda za a ci nasara a kan Babila? (b) Me ya sa za mu iya cewa Midiya da Farisa ce kai na huɗu na dabbar?

      12 Shekaru da yawa kafin zamanin Daniyel, Jehobah ya bayyana ta bakin annabi Ishaya game da mulkin da zai ci nasara a kan Babila. Jehobah ya bayyana yadda za a ci nasara a kan Babila da kuma sunan wanda zai ja-goranci waɗannan rundunar. Wannan mai ja-gorar shi ne Sairus, sarkin ƙasar Midiya da Farisa. (Isha. 44:28-45:2) Jehobah ya kuma saukar wa da Daniyel wahayi biyu game da mulkin ƙasar Midiya da Farisa. A wahayi na ɗaya, Daniyel ya ga wata dabba mai kama da bear, wadda gefen jikinta ɗaya ya ɗara ɗayan. Kuma an ce za ta cinye nama da yawa. (Dan. 7:5) A wani wahayi dabam, Daniyel ya ga wani rago mai ƙahoni biyu.—Dan. 8:3, 20.

      13 Jehobah ya yi amfani da Midiya da Farisa don ta ci nasara a kan Babila kuma Isra’ilawa su samu damar koma ƙasarsu yadda aka annabta. (2 Laba. 36:22, 23) Amma daga baya, Midiya da Farisa ta yi ƙoƙarin ta halaka mutanen Allah. Littafin Esther ya ba da labarin wani minista na ƙasar Farisa mai suna Haman wanda ya yi ƙulle-ƙulle don ya kashe dukan Isra’ilawa da suke wannan Daular. Haman ya zaɓi kwanan wata kuma ya ba mutanensa umurni cewa su kashe dukan Yahudawa. Amma, Jehobah ya hana zuriyar Shaiɗan su halaka mutanen Allah. (Esther 1:1-3; 3:8, 9; 8:3, 9-14) Saboda haka, za mu iya cewa Midiya da Farisa ita ce kai na huɗu na dabbar da aka ambata a littafin Ru’ya ta Yohanna.

      HELLAS CE KAI NA BIYAR

      14, 15. Waɗanne bayanai ne Jehobah ya ba da game da mulkin ƙasar Hellas na zamanin dā?

      14 Kai na biyar na dabbar da aka kwatanta a littafin Ru’ya ta Yohanna yana wakiltar Hellas. A mafarkin da Daniyel ya bayyana wa sarki Nebuchadnezzar, cikin sifar da cinyoyinta na jangaci suna wakiltar Hellas. Jehobah ya saukar wa da Daniyel wasu wahayi biyu da suka bayyana mulkin ƙasar Hellas da kuma sarkinta.

      15 A wahayi guda, Daniyel ya ga damisa mai fukafukai biyu. Kuma wannan damisar tana wakiltar ƙasar Hellas wadda za ta hanzarta wajen halaka al’ummai. (Dan. 7:6) A wani wahayi kuma, Daniyel ya ga wani bunsuru mai babbar ƙaho guda. Kuma nan da nan ya kashe wani rago mai ƙaho biyu wanda ke wakiltar ƙasar Midiya da Farisa. Jehobah ya gaya wa Daniyel cewa bunsurun yana wakiltar Hellas kuma babbar ƙahonsa yana wakiltar ɗaya cikin sarakunan ƙasar. Daniyel ya kuma rubuta cewa za a karya ƙahon kuma ƙahoni huɗu za su yi girma maimakon guda. Dukan abin da aka annabta game da wannan ƙasar ta cika ko da yake an rubuta shi shekaru da yawa kafin ƙasar Hellas ta soma sarauta. Iskandari mai girma ne wannan babbar ƙahon. Shi ne sarki mai iko na ƙasar Hellas ta dā kuma ya halaka ƙasar Midiya da Farisa. An karya wannan ƙahon sa’ad da Iskandari ya mutu. A lokacin, shi ɗan shekara 32 ne kuma yana da iko sosai. Bayan mutuwarsa, aka raba mulkinsa wuri huɗu kuma aka ba wa janarorinsa guda huɗu.—Karanta Daniyel 8:20-22.

      16. Mene ne Antiochus na Huɗu ya yi?

      16 Bayan ƙasar Hellas ta halaka Farisa, sai ta soma mulki a kan Isra’ila. A lokacin Yahudawa suna zama a Ƙasar Alkawari kuma sun sake gina haikalin da ke Urushalima. Suna bauta wa Jehobah kuma yana amince da bauta da suke yi a haikalin da ke Urushalima. Amma, a ƙarni na biyu kafin zamanin Yesu, Hellas ta kai wa mutanen Allah hari. Hakan ya faru sa’ad da Antiochus na Huɗu, wanda ya gaji ɗaya cikin mulkoki huɗu na Iskandari, ya gina bagadi don bautar gunki a haikalin Urushalima. Kuma ya ce a kashe duk wanda bai bauta wa gunkin ba. A wannan lokacin ma, zuriyar Shaiɗan tana gaba da mutanen Allah. Amma, ba da daɗewa ba bayan haka, aka yi wa ƙasar Hellas juyin mulki. Mene ne zai zama kai na shida na dabbar?

      ROMA KAI NA SHIDA “MAI-BAN RAZANA, MAI-IKO” NE

      17. Yaya ne Farawa 3:15 ya cika a kan kai na shidan?

      17 Ƙasar Roma ce take sarauta sa’ad da aka saukar wa da Yohanna wahayin dabbar. (R. Yoh. 17:10) Ƙasar Roma ce kai na shida na dabbar kuma ta cika wani sashe na annabcin da ke littafin Farawa 3:15. Shaiɗan ya yi amfani da ƙasar Roma don ƙuje “duddugen” zuriyar. Romawa sun ɗauki Yesu a matsayin maƙiyi da ke gaba da sarautar ta. Sun hukunta shi kuma sun kashe shi. (Mat. 27:26) Amma, wannan ƙujewar ba ta daɗe ba domin Jehobah ya ta da Yesu daga matattu.

      18. (a) Wace sabuwar al’umma ce Jehobah ya zaɓa kuma me ya sa? (b) Me ya sa zuriyar macijin ta ci gaba da yin gaba da zuriyar macen?

      18 Shugabannin addinai na Isra’ila sun haɗa baki da ƙasar Roma don su yi gaba da Yesu. Kuma yawancin Isra’ilawa ba su amince cewa Yesu ne Almasihu ba. Dalilin da ya sa Jehobah ya ƙi da Isra’ilawa ke nan. (Mat. 23:38; A. M. 2:22, 23) Daga baya ya zaɓi sabon al’umma, wato, “Isra’ila na Allah.” (Gal. 3:26-29; 6:16) Wannan sabon al’ummar ita ce ikilisiyar Kiristoci shafaffu wadda ta haɗa da Yahudawa da kuma ’Yan Al’ummai. (Afis. 2:11-18) Har bayan Yesu ya mutu ya kuma tashi daga matattu, zuriyar macijin ta ci gaba da yin gaba da zuriyar macen. Ƙasar Roma ta yi ƙoƙari sau da yawa don ta halaka ikilisiyar Kiristoci gabaki ɗaya, wadda ita ce sashe na biyu na zuriyar macen.c

      19. (a) Ta yaya Daniyel ya bayyana mulki na shida da zai yi sarauta bisa duniya? (b) Mene ne za mu tattauna a talifi na gaba?

      19 A mafarkin da Daniyel ya bayyana wa sarki Nebuchadnezzar, ƙasar Roma ce take wakiltar ƙafafu na baƙin ƙarfe. (Dan. 2:33) Daniyel ya sake ganin wahayin da ta bayyana Daular Roma da kuma mulkin da zai yi sarauta bayan ita. (Karanta Daniyel 7:7, 8.) A cikin shekaru da yawa, Roma ta zama ƙasa “mai-ban razana, mai-iko, mai-ƙarfi ƙwarai” ga maƙiyan ta. Amma, wannan annabcin ya nuna cewa wannan daular za ta haifar da “ƙaho goma.” Kuma ɗaya cikinsu zai yi girma kuma ya samu iko sosai. Mene ne waɗannan ƙahoni goma kuma wane ne wannan ƙaramin ƙahon? A wace hanya ce babbar sifar da Sarki Nebuchadnezzar ya gani a mafarkinsa take da nasaba da ƙaramin ƙahon? Talifin da ke shafi na 14 zai ba da amsa ga waɗannan tambayoyin.

      [Hasiya]

      a Wannan macen tana nufin dukan bayin Jehobah da ke sama. Littafi Mai Tsarki ya kwatanta su kamar matar Jehobah.—Isha. 54:1; Gal. 4:26; R. Yoh. 12:1, 2.

      b Kan sifar a littafin Daniyel da kuma kai na uku na babbar dabbar a littafin Ru’ya ta Yohanna suna wakiltar Babila. Ka duba taswirar da ke shafuffuka na 12-13.

      c Ko da yake ƙasar Roma ta halaka Urushalima a shekara ta 70 a zamanin Yesu, amma wannan halakar ba ta cika annabcin da ke littafin Farawa 3:15 ba. A lokacin, Allah ya riga ya yasar da al’ummar Isra’ila.

  • Jehobah Ya Bayyana Al’amura Da Lallai “Za Su Faru Ba Da Daɗewa Ba”
    Hasumiyar Tsaro—2012 | 15 Yuni
    • Jehobah Ya Bayyana Al’amura Da Lallai “Za Su Faru Ba Da Daɗewa Ba”

      “Ru’ya ta Yesu Kristi, wanda Allah ya ba shi domin ya bayyana ma bayinsa, al’amura da za su faru ba da daɗewa ba.”—R. YOH. 1:1.

      MECE CE AMSARKA?

      Wane ɓangaren babbar sifa ne yake wakiltar Mulkin Biritaniya da Amirka?

      Ta yaya Yohanna ya kwatanta dangantakar da ke tsakanin Mulkin Biritaniya da Amirka da kuma Majalisar Ɗinkin Duniya?

      Ta yaya Daniyel da Yohanna suka kwatanta yadda za a kawo ƙarshen mulkin ɗan Adam?

      1, 2. (a) Mene ne za mu fahimta idan muka tattauna wahayin Yohanna da na Daniyel? (b) Mene ne kai na ɗaya zuwa shida na dabbar suke wakilta?

      ANNABCE-ANNABCEN Daniyel da kuma Yohanna sun sa mun fahimci abubuwan da suke faruwa a yau da waɗanda za su faru a nan gaba. Mene ne za mu koya daga wahayin Yohanna na dabba mai kawuna guda bakwai da kuma daga wahayin Daniyel game da dabba mai ƙahoni guda goma da babbar sifar da Nebuchadnezzar ya yi mafarkinta? Kuma mene ne fahimtar waɗannan annabce-annabcen ya kamata ya motsa mu mu yi?

      2 Bari mu tattauna wahayin Yohanna game da dabbar. (R. Yoh., sura ta 13) Mun koyi cewa kai na ɗaya zuwa shida na dabbar suna wakiltar ƙasar Masar da Assuriya da Babila da Midiya-da-Farisa da Hellas da kuma Roma. Shaiɗan ya yi amfani da waɗannan masu mulkin duniya wajen tsananta wa mutanen Allah. (Far. 3:15) Roma ita ce mai mulkin duniya na shida kuma ta ci gaba da kasancewa hakan shekaru da yawa bayan Yohanna ya rubuta wahayinsa. Amma, da shigewar lokaci, kai na bakwai, wato mai mulkin duniya na bakwai zai sauya Roma. Wace ƙasa ce wannan, kuma yaya za ta bi da zuriyar macen?

      BIRITANIYA DA AMIRKA SUN SAMU IKO SOSAI

      3. Mece ce dabba mai ƙahoni goma mai ban tsoro take wakilta, kuma mene ne ƙahoni guda goma suke wakilta?

      3 Za mu gane kai na bakwai na dabbar da aka yi maganarsa a Ru’ya ta Yohanna sura ta 13 idan muka kwatanta wahayin Yohanna da na Daniyel wanda yake maganar wata dabba mai ban tsoro mai ƙahoni goma.a (Karanta Daniyel 7:7, 8, 23, 24.) Wannan dabbar da Daniyel ya gani a wahayinsa tana wakiltar Roma a matsayin mai mulkin duniya. (Duba taswira da ke shafuffuka na 12-13.) A ƙarni na biyar, Sarautar Roma ta fara taɓarɓarewa. Ƙahoni guda goma da Daniyel ya gani suna nufin ƙananan mulkoki da suka fito daga sarautar Roma.

      4, 5. (a) Mene ne ƙaramin ƙahon ya yi? (b) Mene ne kai na bakwai na dabbar yake wakilta?

      4 A annabcin Daniyel game da dabba mai ƙahoni goma, an ambata cewa wani ƙaramin ƙaho ya fito daga kan dabbar kuma ya sauya ƙahoni uku daga cikin goma. Wannan annabcin ya cika sa’ad da Biritaniya wata ƙasar da Roma take mallaka ta zama mai mulkin kanta. Kafin ƙarni na 17 a zamaninmu, ƙasar Biritaniya ba ta da ƙarfi sosai. Wasu ƙasashe guda uku, wato Sifen da Holan da kuma Faransa sun fi ta iko. Ƙasar Biritaniya ta yaƙe su ɗaya bayan ɗaya kuma ta zama ƙasa mafi iko a cikinsu. A ƙarni na 18 a zamaninmu, Biritaniya tana gab da zama ƙasa mafi iko a duniya amma ba ta zama kai na bakwai na dabbar ba.

      5 Ko da yake Biritaniya ta zama ƙasa mafi iko, amma ƙananan ƙasashe da ke ƙarƙashinta a Arewancin Amirka sun yi tawaye kuma suka haɗa kai suka zama ƙasar Amirka. Duk da haka, Biritaniya ba ta hana ƙasar Amirka ci gaba ba, har ta kāre ta da rundunar yaƙi na jiragen ruwa kuma hakan ya sa ƙasar Amirka ta samu ci gaba sosai. Sa’ad da ranar Ubangiji ta soma a shekara ta 1914, Biritaniya, ƙasa mafi iko ta mallaki ƙasashe da yawa a faɗin duniya kuma Amirka ta zama ƙasa mafi samun ci gaba a duniya.b A lokacin Yaƙin Duniya na ɗaya, Biritaniya ta ƙulla yarjejeniya ta musamman da ƙasar Amirka. Wannan haɗin kai na Biritaniya da Amirka ne ya haifar da Mulkin Biritaniya da Amirka. Ta yaya Mulkin Biritaniya da Amirka ta bi da zuriyar macen?

      6. Yaya kai na bakwai na dabbar ya bi da mutanen Allah?

      6 Ba da daɗewa ba da ranar Ubangiji ta soma, kai na bakwai na dabbar ya fara kai wa mutanen Allah hari, wato, ’yan’uwan Kristi da suka rage a duniya. (Mat. 25:40) Yesu ya nuna cewa a somawar ranar Ubangiji wato a bayyanuwarsa, zuriyar macen za su riƙa yin aikin da ya ce su yi. (Mat. 24:45-47; Gal. 3:26-29) Mulkin Biritaniya da Amirka sun yaƙe waɗannan tsarkakku. (R. Yoh. 13:3, 7) A lokacin Yaƙin Duniya na ɗaya, mulkin ya tsananta wa mutanen Allah, ya hana su buga littattafansu kuma ya jefa wakilan rukunin bawa nan mai-aminci cikin kurkuku. Kai na bakwai na dabbar nan ya kusan sa a daina yin wa’azi gabaki ɗaya a lokacin. Jehobah ya bayyana wa Yohanna a cikin wahayi cewa hakan zai faru. Allah ya ƙara gaya wa Yohanna cewa waɗannan tsarkakkun sashen zuriyar macen za su soma aikin wa’azi kuma. (R. Yoh. 11:3, 7-11) Tarihin Shaidun Jehobah ya nuna cewa waɗannan abubuwa sun faru.

      MULKIN BIRITANIYA DA AMIRKA DA KUMA SAWUN ƘARFE DA YUMƁU

      7. Wace irin dangantaka ce ke tsakanin kai na bakwai na dabbar da kuma babbar sifar?

      7 Wace irin dangantaka ce ke tsakanin kai na bakwai na dabbar da babbar sifar? Biritaniya da Amirka sun fito daga ƙarƙashin Mulkin Roma. Sawayen sifar kuma fa? An kwatanta su a matsayin haɗin ƙarfe da yumɓu. (Karanta Daniyel 2:41-43.) Wannan kwatancin yana maganar lokacin da kai na bakwai na dabbar, wato Mulkin Biritaniya da Amirka zai fara sarauta. Kamar yadda ginin da aka yi da yumɓu da ƙarfe ba zai kai wanda aka yi da ƙarfe zalla ƙarfi ba, hakan ma Mulkin Biritaniya da Amirka ba zai kai Roma ƙarfi ba. Ta yaya hakan ya faru?

      8, 9. (a) Ta yaya mai mulkin duniya na bakwai ya nuna iko da ke kama da ƙarfe? (b) Mene ne sawayen sifar suke nufi?

      8 A wasu lokatai, mulkin Biritaniya da Amirka ya nuna cewa yana da ƙarfi kamar ƙarfe. Alal misali, ya yi hakan ta wajen samun nasara a Yaƙin Duniya na ɗaya. Kuma a Yaƙin Duniya na biyu ya sake samun nasara.c A wasu lokatai bayan yaƙin, kai na bakwai na dabbar yana nuna ƙarfinsa da ke kamar ƙarfe. Amma, daga lokacin da Mulkin Biritaniya da Amirka ya fara sarauta, an garwaya ƙarfen da yumɓu.

      9 Da daɗewa bayin Jehobah sun yi ƙoƙari su fahimci abin da sawayen sifar suke nufi. Littafin Daniyel 2:41 ya kwatanta ƙarfe da ke garwaye da yumɓu a matsayin “mulki” ɗaya ba mulkoki dabam-dabam ba. Yumɓun yana nufin wani abin da ke rage ƙarfin Mulkin Biritaniya da Amirka kuma hakan ya sa Mulkin Roma wanda ƙarfe ne zalla ya fi shi ƙarfi. Annabcin Daniyel ya ce yumɓun yana nufin “zuriyar mutane” ko kuma talakawa. (Dan. 2:43) A Mulkin Biritaniya da Amirka, jama’a sun tashi tsaye a kan neman ’yancinsu, sun yi hakan ta yin zanga-zanga cikin lumana, ta ƙungiyar ƙwadago kuma ƙasashe sun nemi ’yanci kai. Waɗannan abubuwa da mutane suke yi suna sa ya yi wa Mulkin Biritaniya da Amirka wuya ya yi ƙarfi kamar ƙarfe. Mutane suna da ra’ayoyi dabam-dabam game da siyasa. Kuma sa’ad da wani ya ci zaɓe da ƙarin ƙuri’o’i kaɗan, ba ya samun isashen iko ya aiwatar da abubuwan da ya yi alkawarinsu. Daniyel ya annabta cewa: “Mulkin za ya kasance, rabi da ƙarfi, rabi mara-ƙarfi.”—Dan. 2:42; 2 Tim. 3:1-3.

      10, 11. (a) Mene ne zai faru da ‘sawayen’ a nan gaba? (b) Mene ne za mu iya kammala game da adadin yatsun sifar?

      10 A zamaninmu, Biritaniya da Amirka sun ci gaba da ƙawanci, sau da yawa suna haɗa kai kuma su saka hannu a al’amuran duniya. Annabcin babbar sifar da kuma dabbar sun nuna cewa ba wani mulki da zai sauya Mulkin Biritaniya da Amirka, shi ne mulki na ƙarshe. Ko da yake, wannan mulkin ba shi da ƙarfi kamar mulkin Roma, wato, ƙafar ƙarfen, ba zai ragargaje da kanta ba.

      11 Adadin yatsun sifar yana da wata ma’ana ne? A wasu wahayi, Daniyel ya ambata adadin abubuwa, alal misali, adadin ƙahoni da ke kan dabbobi dabam-dabam. Waɗannan adadin suna da muhimmanci. Amma, sa’ad da Daniyel yake kwatanta sifar, bai ambata adadin yatsun ba. Wannan ya nuna cewa adadin yatsun bai da wani muhimmanci, matsayinsu ɗaya ne da adadin hannuwan da yatsun da ƙafafuwan da kuma sawayen. Amma, Daniyel ya ambata cewa yatsun za su kasance na ƙarfe da yumɓu. A nan za mu fahimta cewa Mulkin Biritaniya da Amirka ne zai riƙa mulkin duniya sa’ad da ‘dutsen,’ wato Mulkin Allah zai rugurguje sawayen sifar.—Dan. 2:45.

      MULKIN BIRITANIYA DA AMIRKA DA KUMA DABBA MAI ƘAHONI BIYU

      12, 13. Mece ce dabba mai ƙahoni biyu take wakilta, kuma me ta yi?

      12 Ko da yake Mulkin Biritaniya da Amirka haɗin ƙarfe da yumɓu ne, wahayin da Yesu ya nuna wa Yohanna ya bayyana cewa wannan mulkin zai yi abu mai muhimmanci a kwanaki na ƙarshe. Ta yaya zai yi hakan? Yohanna ya ga wahayin wata dabba mai ƙahoni biyu mai magana kamar dragon. Mene ne wannan dabba mai ban tsoro take wakilta? Tana da ƙahoni biyu, wato ƙasashe guda biyu da suka haɗa kai a yin sarauta. Wannan dabbar tana wakiltar Mulkin Biritaniya da Amirka amma tana yin wani abu na musamman.—Karanta Ru’ya ta Yohanna 13:11-15.

      13 Wannan dabbar tana gaya wa jama’a su ƙera sifar dabbar da ke da kawuna bakwai. Yohanna ya rubuta cewa sifar dabbar za ta bayyana kuma ta ɓace, daga baya ta sake bayyana. Hakan ya faru da wata ƙungiyar da Biritaniya da Amirka suke ja-gora, burin wannan ƙungiyar shi ne ta haɗa kan dukan gwamnatocin duniya kuma ta wakilce su.d Wannan ƙungiyar ta bayyana bayan Yaƙin Duniya na ɗaya, ita ce Majalisar Ɗinkin Duniya ta dā. Sa’ad da aka soma Yaƙin Duniya na biyu, wannan ƙungiyar ta daina aiki. A lokacin wannan yaƙin, mutanen Allah sun bayyana cewa ƙungiyar za ta sake tasowa kamar yadda littafin Ru’ya ta Yohanna ya annabta. Kuma hakan ya faru, ta taso a matsayin Majalisar Ɗinkin Duniya ta yanzu.—R. Yoh. 17:8.

      14. Me ya sa Yohanna ya kira sifar dabbar sarki “na takwas”?

      14 Yohanna ya kwatanta sifar dabba mai kawuna bakwai a matsayin sarki “na takwas.” Me ya sa ya kira shi sarki? Bai bayyana a matsayin kai na takwas na ainihin dabbar ba. Ya bayyana ne a matsayin sifarta. Tana samun ikonta daga ƙasashen da Majalisar Ɗinkin Duniya ke wakiltar su ne, musamman daga Mulkin Biritaniya da Amirka. (R. Yoh. 17:10, 11) Yohanna ya ce sarki ne don yana samun ikon yin abubuwan da zai shafi dukan duniya.

      SIFAR DABBAR TA HALAKA KARUWAR

      15, 16. Mene ne karuwar da Yohanna ya gani a wahayinsa take wakilta kuma mene ne yake faruwa da addinai a yau?

      15 Yohanna ya sake kwatanta wata karuwa da take zaune a kan wata dabba ja wur. Sunanta “Babila Babba.” (R. Yoh. 17:1-6) Wannan karuwar tana nufin dukan addinan ƙarya, kuma a cikin waɗannan addinan ƙarya, Kiristendam ne ta fi rinjaya. Addinai sun goyi bayan Majalisar Ɗinkin Duniya na dā da na yanzu kuma suna ƙoƙarin yi mata ja-gora.

      16 An ce Babila Babba tana zaune a kan ‘ruwa.’ Wannan ruwan yana nufin jama’an da suke goyon bayanta. Amma a ranar Ubangiji, goyon bayan da suke yi mata ya ragu sosai. (R. Yoh. 16:12; 17:15) Alal misali, lokacin da sifar dabbar ta bayyana da farko, coci na Kiristendam suna da iko sosai a ƙasashe da yawa. Amma a yanzu jama’a ba sa daraja coci da limamanta kamar yadda suke yi a dā. Mutane da yawa sun tabbata cewa addini ne yake haddasa tashin hankali a wurare da yawa a duniya. Wasu suna so a kawo ƙarshen dukan addinai.

      17. Mene ne zai faru da addinan ƙarya nan ba da daɗewa ba, kuma me ya sa?

      17 Ba za a kawo ƙarshen addinan ƙarya da sannu-sannu ba. Karuwar za ta ci gaba da kasancewa da iko kuma ta riƙa sa sarakuna su aikata nufinta har sai Allah ya sa cikin zuciya masu mulki su yi nufinsa. (Karanta Ru’ya ta Yohanna 17:16, 17.) Nan ba da daɗewa ba, Jehobah zai yi amfani da gwamnatocin ’yan Adam wanda Majalisar Ɗinkin Duniya na yanzu take wakilta don ya kai wa addinan ƙarya hari. Karuwar ba za ta sake iya rinjayar waɗannan gwamnatoci ba kuma za ta rasa dukan dukiyoyinta. Shekaru ashirin ko talatin da suka wuce, mutane da yawa ba su taɓa tsammani cewa wannan abin zai iya faruwa ba. Amma a yau, abubuwa sun fara canjawa, duk da haka karuwar ba za ta faɗo daga kan dabbar ja wur a hankali ba. Za a halaka ta ne nan take.—R. Yoh. 18:7, 8, 15-19.

      AN HALAKA DABBOBIN

      18. (a) Mene ne dabbar za ta yi, kuma mene ne sakamakon? (b) Waɗanne mulkoki ne littafin Daniyel 2:44 ya ce Mulkin Allah zai halaka? (Duba akwatin da ke shafi na 17.)

      18 Bayan an halaka addinan ƙarya, Shaiɗan zai sa dabbar, wato gwamnatocin da ke ƙarƙashin ikonsa ta kai hari ga Mulkin Allah. Tun da sarakunan duniya ba za su iya kai hari ga Mulkin Allah a sama ba, za su yi yaƙi da waɗanda suke goyon bayan Mulkin Allah a nan duniya. Sakamakon haka shi ne yaƙin ƙarshe da Allah zai yi da su. (R. Yoh. 16:13-16; 17:12-14) Daniyel ya bayyana abin da zai faru a wannan yaƙin. (Karanta Daniyel 2:44.) Za a halaka dabbar da aka ambata a littafin Ru’ya ta Yohanna 13:1 da sifarta da kuma dabba mai ƙahoni biyu.

      19. Wane tabbaci ne muke da shi, kuma yanzu ne lokacin yin mene ne?

      19 Muna zama ne a kwanakin kai na bakwai na dabbar. Ba za a sake yin wani kai kafin a halaka wannan dabbar ba. Mulkin Biritaniya da Amirka zai riƙa sarauta a lokacin da za a halaka addinan ƙarya. Dukan annabce-annabcen Daniyel da na Yohanna sun cika daidai yadda aka rubuta. Bari mu kasance da gaba gaɗi cewa za a halaka addinan ƙarya nan ba da daɗewa ba. Allah ya bayyana mana waɗannan abubuwa tun da wuri. Amma, za mu yi biyayya da gargaɗin da ke cikin waɗannan annabcin ne? (2 Bit. 1:19) Yanzu ne ya kamata mu yi biyayya ga Jehobah kuma mu goyi bayan Mulkinsa.—R. Yoh. 14:6, 7.

      [Hasiya]

      a A cikin Littafi Mai Tsarki goma yana nufin cikakke. Wato wannan ƙahoni goma suna nufin dukan sarautar da suka fito daga ƙarƙashin Sarautar Roma.

      b Ko da yake fasalolin Mulkin Amirka da Biritaniya sun bayyana tun ƙarni na 18, Yohanna ya annabta cewa za su fara sarauta a matsayin Mulki guda a somawar ranar Ubangiji. Hakika, wahayin Yohanna annabci ne da ke cika a “ranar Ubangiji.” (R. Yoh. 1:10) A lokacin Yaƙin Duniya na ɗaya ne Biritaniya da Amirka suka haɗa kai a matsayin masu mulkin duniya.

      c Kamar yadda Daniyel ya annabta, Mulkin Biritaniya da Amirka ya yi “hallakaswa da ban mamaki.” (Dan. 8:24) Alal misali, Amirka ta jefa bama-bamai na atam guda biyu da suka halaka abubuwa sosai a ƙasar da ke gaba Mulkin Biritaniya da Amirka.

      d Duba littafin nan Revelation—Its Grand Climax at Hand!, shafuffuka na 240 da 241 da kuma 253 na Turanci.

      [Akwati a shafi na 17]

      SU WAYE NE ‘DUKAN WAƊANNAN MULKOKIN’?

      Annabcin da ke littafin Daniyel 2:44 ya ce Mulkin Allah ‘za ya farfashe dukan waɗannan mulkokin.’ Wannan annabcin yana maganar mulkoki da babbar sifar take wakilta ne kawai.

      Sauran Gwamnatocin ’yan Adam kuma fa? Annabcin da ke Ru’ya ta Yohanna da ya yi magana game da wannan batun ya ba da ƙarin haske. Ya nuna cewa “sarakunan dukan duniya” za su haɗa kai don su yaƙi Jehobah a “babbar rana ta Allah Mai-iko duka.” (R. Yoh. 16:14; 19:19-21) Saboda haka, ba mulkokin da sifar take wakilta ba ne kawai za a halaka a Armageddon, amma dukan gwamnatocin ’yan Adam.

  • An Bayyana Sarakuna Takwas
    Hasumiyar Tsaro—2012 | 15 Yuni
    • An Bayyana Sarakuna Takwas

      Annabce-annabce da ke cikin littafin Daniyel da Ru’ya ta Yohanna sun ba da bayani game da sarakuna takwas, ko kuma sarautar ’yan Adam da kuma tsarin yadda suka bayyana. Za mu iya sanin ma’anar waɗannan annabce-annabcen, idan mun fahimci annabci na farko da ke cikin Littafi Mai Tsarki.

      Shekaru da yawa yanzu, Shaiɗan ya tsara zuriyarsa zuwa gwamnatoci ko kuma mulki na siyasa dabam-dabam. (Luk 4:5, 6) Wasu cikin waɗannan gwamnatoci sun kai farmaki kai tsaye ga mutanen Allah, wato, al’ummar Isra’ila ko kuma ikilisiyar Kiristoci shafaffu. Wahayin da Daniyel da kuma Yohanna suka gani ya kwatanta sarakuna takwas kaɗai masu iko sosai.

      [Taswira/Hotona a shafi na 12, 13]

      (Don ganin cikakken rubutun, ka duba littafin)

      ANNABCE-ANNABCE ANNABCE-ANNABCEN DA

      DA KE CIKIN KE CIKIN LITTAFIN

      LITTAFIN DANIYEL RU’YA TA YOHANNA

      1. Masar

      2. Assuriya

      3. Babila

      4. Midiya

      da Farisa

      5. Hellas

      6. Roma

      7. Biritaniya

      da Amirkaa

      8. Tsohuwa da kuma

      sabuwar Majalisar

      Ɗinkin Duniyab

      MUTANEN ALLAH

      2000 Kafin zamaninmu

      Ibrahim

      1500

      Al’ummar Isra’ila

      1000

      Daniyel 500

      Kafin zamaninmu/a zamaninmu

      Yohanna

      Isra’ila na Allah 500

      1000

      1500

      2000 A zamaninmu

      [Hasiya]

      a Dukansu sun wanzu a kwanaki na ƙarshe. Ka duba shafi na 19.

      b Dukansu sun wanzu a kwanaki na ƙarshe. Ka duba shafi na 19.

      [Hotona]

      Babbar sifar (Dan. 2:31-45)

      Dabbobi huɗu da suka fito daga teku (Dan. 7:3-8, 17, 25)

      Ragon da bunsurun (Dan., sura ta 8)

      Bisa mai kawuna bakwai (R. Yoh. 13:1-10, 16-18)

      Bisa mai ƙaho biyu ta gaya wa mutane su yi gunkin dabbar (R. Yoh. 13:11-15)

      [Wuraren da Aka Ɗauko]

      Inda aka samo hotuna: Masar da Roma: British Museum ne suka ɗauka hoton; Midiya da Farisa: Musée du Louvre, Paris

  • Tambayoyi Daga Masu Karatu
    Hasumiyar Tsaro—2012 | 15 Yuni
    • Tambayoyi Daga Masu Karatu

      A wane lokaci ne Biritaniya da Amirka suka zama masu mulkin duniya na bakwai da aka kwatanta a cikin Littafi Mai Tsarki?

      ▪ A mafarkin da sarki Nebukadnezzar ya yi, ya ga wata babbar sifa na ƙarfe, wannan sifar ba ta wakiltar dukan masu mulki na duniya. (Dan. 2:31-45) Amma tana wakiltar masu mulki na duniya guda biyar kaɗai da suka kai wa mutanen Allah farmaki a zamanin Daniyel da kuma bayan hakan.

      Yadda Daniyel ya kwatanta sifa ta ƙarfe ya koya mana cewa Mulkin Biritaniya da Amirka ba za ta yi wa Roma juyin mulki ba amma za ta taso ne daga cikinta. Daniyel ya ce ƙarfen ya soma daga ƙafafun har zuwa sawun da kuma yatsun. (An kwaɓa ƙarfen da yumɓu a sawun da kuma yatsun.)a Wannan kwatancin ya nuna cewa Mulkin Biritaniya da Amirka zai fito daga Roma, wato, ƙafafun ƙarfe. Kuma hakan ya faru. Biritaniya ƙaramin sashe ne na Mulkin Roma, amma ta soma kasancewa da iko sosai a ƙarshen ƙarni na 17. Bayan haka, Amirka ta zama ƙasa mai iko sosai. Amma a lokacin, Biritaniya da Amirka ba su zama masu mulkin duniya na bakwai da aka kwatanta a cikin Littafi Mai Tsarki ba tukuna. Me ya sa? Domin ba su soma aiki tare a hanya ta musamman ba. Sun soma aiki a lokacin Yaƙin Duniya na ɗaya.

      A wannan lokacin, “’ya’yan mulki” sun fi ƙwazo sosai a ƙasar Amirka, kuma hedkwatarsu yana Brooklyn, New York. (Mat. 13:36-43) Shafaffu suna wa’azi sosai a ƙasashe da suke ƙarƙashin sarautar Biritaniya. A lokacin Yaƙin Duniya na ɗaya, Biritaniya da Amirka suka zama abokai na musamman. Sun haɗa hannu suka yaƙi magabta ’yan siyasa. Da yake yaƙin ya sa Biritaniya da Amirka su ƙara zama masu ƙishin ƙasa, sun kai farmaki ga waɗanda suka zama sashen zuriyar “macen” Allah. Sun hana a rarraba da kuma yi amfani da littattafan da zuriyar macen ta wallafa da kuma saka waɗanda suke shugabanci a aikin wa’azi a cikin kurkuku.—R. Yoh. 12:17.

      Saboda haka, abin da muka karanta a cikin annabci na Littafi Mai Tsarki ya koya mana cewa masu mulki na bakwai ba su bayyana ba a ƙarshen ƙarni na 17 ba sa’ad da Biritaniya ta fara zama mulki mai iko sosai. Maimakon haka, ya samu iko a somawar ranar Ubangiji.b

      [Hasiya]

      a Yumɓu da aka kwaɓa da ƙarfe yana nufin mutanen da ke cikin Mulkin Biritaniya da Amirka. A cikin shekaru da yawa yanzu, wannan yumɓun ya sa ya kasance wa wannan mulkin wuya ya nuna ikonsa yadda yake so.

      b Wannan bayani ya soke abin da aka bayyana a shafi na 57, sakin layi na 24 na littafin nan Pay Attention to Daniel’s Prophecy! da kuma taswirar da ke shafuffuka na 56 da 139.

      [Hoto a shafi na 19]

      An aika ’yan’uwa takwas da ke hedkwata na Shaidun Jehobah kurkuku a watan Yuni na shekara ta 1918

Littattafan Hausa (1987-2026)
Fita
Shiga Ciki
  • Hausa
  • Raba
  • Wadda ka fi so
  • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
  • Ka'idojin Amfani
  • Tsarin Tsare Sirri
  • Saitin Tsare Sirri
  • JW.ORG
  • Shiga Ciki
Raba