WAƘA TA 123
Mu Riƙa Bin Ja-gorancin Jehobah
Hoto
1. Mu bayin Jehobah muna wa’azi,
Wa’azi game da Mulkin Allahnmu.
Ja-gorancin Allah za mu riƙa bi,
Mu riƙe aminci, mu yi haɗin kai.
(AMSHI)
Allah Jehobah ne ya kamata
Mu riƙa bauta wa.
Yana ƙaunar mu, yana da iko,
Za mu riƙe aminci.
2. Allahnmu Jehobah ya yi tanadi,
Tanadin ruhunsa da wakilinsa.
Za mu yi biyayya da gaba gaɗi,
Mu riƙa wa’azin Mulkin Allahnmu!
(AMSHI)
Allah Jehobah ne ya kamata
Mu riƙa bauta wa.
Yana ƙaunar mu, yana da iko,
Za mu riƙe aminci.
(Ka kuma duba Luk. 12:42; Ibran. 13:7, 17.)