Ka Yi Wa Sarki Kristi Hidima Da Aminci
“Aka ba shi sarauta da daraja, da mulki, domin dukan al’ummai, da dangogi, da harsuna su bauta masa.”—DANIEL 7:14.
1, 2. Ta yaya muka sani cewa Kristi bai samu cikakken ikon sarautar Mulki ba a shekara ta 33 A.Z.?
WANE sarki ne zai ba talakawansa ransa kuma ya sake rayuwa ya zama sarki? Wane sarki ne zai yi rayuwa a duniya, domin ya sa talakawansa su dogara gare shi kuma su amince da shi, sa’annan ya yi sarauta daga sama? Yesu Kristi ne kaɗai zai iya yin haka har ma fiye da haka. (Luka 1:32, 33) A Fentakos na shekara ta 33 A.Z., bayan mutuwar Kristi da tashinsa daga matattu, da kuma sa’ad da ya hau sama, Allah “ya sanya shi kuma shi zama kai a bisa abu duka ga ikilisiya.” (Afisawa 1:20-22; Ayukan Manzanni 2:32-36) Kristi ya soma sarauta amma ba gabaki ɗaya ba. Kiristoci da aka shafa da ruhu ne talakawansa na farko, suna cikin Isra’ila ta ruhaniya, wato, ‘Isra’ila na Allah.’—Galatiyawa 6:16; Kolossiyawa 1:13.
2 Kusan shekara 30 bayan Fentakos na shekara ta 33 A.Z., manzo Bulus ya tabbatar cewa Kristi bai soma cikakkiyar sarauta ta Mulki ba, amma “ya zauna ga hannun dama na Allah; daga nan gaba yana tsumayi har an mayarda maƙiyansa matashin sawayensa.” (Ibraniyawa 10:12, 13) Kusan ƙarshen ƙarni na farko A.Z., manzo Yohanna tsoho ya ga Jehobah Mamallakin Dukan Halitta a cikin wahayi yana naɗa Yesu Kristi Sarki na sabon Mulkin samaniya da aka kafa. (Ru’ya ta Yohanna 11:15; 12:1-5) Za mu iya maimaita tabbacin da ya nuna cewa Kristi ya soma sarauta na Sarki Almasihu a sama a shekara ta 1914.a
3. (a) An soma bisharar Mulki da wane sabon fasali tun shekara ta 1914? (b) Waɗanne tambayoyi ne za mu yi wa kanmu?
3 Hakika, tun shekara ta 1914 an soma bisharar Mulki da sabon fasali mai ban mamaki. Kristi yana sarauta, shi ne Sarki na Mulkin samaniya na Allah, amma a ‘tsakiyar maƙiyansa.’ (Zabura 110:1, 2; Matta 24:14; Ru’ya ta Yohanna 12:7-12) Ƙari ga haka, a dukan duniya talakawansa masu aminci suna bin ikonsa ta wurin sa hannu a tsarin ilimantarwa na Littafi Mai Tsarki da babu kamarsa a tarihin ’yan adam da ake yi a dukan duniya. (Daniel 7:13, 14; Matta 28:18) Kiristoci da aka shafa da ruhu, “ya’yan mulki ke nan,” suna hidima na “manzanni . . . madadin Kristi.” Taron “waɗansu tumaki” na Kristi da suke aikin wakilan Mulkin Allah suna tallafa musu cikin aminci. (Matta 13:38; 2 Korinthiyawa 5:20; Yohanna 10:16) Duk da haka, ya kamata kowanenmu ɗaɗɗaya ya bincika ko ya amince da ikon Kristi da gaske. Muna da aminci a gare shi kuwa? Ta yaya za mu kasance da aminci ga Sarkin da ke sarauta a sama? Bari mu fara tattauna dalilan da ya sa za mu kasance da aminci ga Kristi.
Sarki da Ke Sa a Kasance da Aminci
4. Menene Yesu ya cim ma da yake shi Sarki ne da aka naɗa a lokacin hidimarsa na duniya?
4 Muna kasancewa da aminci ga Kristi don mu nuna godiya ga abin da ya yi da kuma halayensa na musamman. (1 Bitrus 1:8) Sa’ad da yake duniya, Yesu da aka naɗa Sarki ya nuna kaɗan cikin abubuwan da zai yi sa’ad da zai soma sarauta a dukan duniya idan lokacin da Allah ya ƙayyade ya yi. Ya ciyar da mayunwata. Ya warkar da masu ciwo, makafi, naƙasassu, kurame da kuma bebaye. Ya ma ta da matattu. (Matta 15:30, 31; Luka 7:11-16; Yohanna 6:5-13) Ƙari ga haka, sani game da rayuwar Yesu a duniya na taimakonmu mu san halayensa da yake shi ne Sarkin duniya na nan gaba, abin da ya fi muhimmanci shi ne ƙaunarsa na sadaukar da kai. (Markus 1:40-45) Napoléon Bonaparte ya ce game da wannan: “Iskandari, Kaisar, Charlemagne, da ni mun kafa dauloli, amma ta yaya muka cim ma waɗannan abubuwa? An tilasta mana. Yesu Kristi ne kaɗai ya kafa mulkinsa a kan ƙauna, kuma a yanzu mutane miliyoyi za su mutu domin shi.”
5. Me ya sa halin Yesu yake jawo mutane?
5 Domin Yesu mai tawali’u ne marar girman kai, koyarwarsa masu ƙarfafawa da halin kirkinsa sun wartsake masu wahala domin matsi da masu fama da kaya. (Matta 11:28-30) Yara sun saki jiki wajensa. Mutane masu tawali’u masu fahimi suna ɗokin su zama almajiransa. (Matta 4:18-22; Markus 10:13-16) Halinsa na yin la’akari da mutane da kuma ladabinsa ya sa mata da yawa masu jin tsoron Allah su amince da shi, da yawa cikinsu sun ba da lokacinsu, kuzarinsu, da dukiyarsu don su kula da shi yayin da yake hidimarsa.—Luka 8:1-3.
6. Wane juyayi ne Yesu ya nuna sa’ad da Li’azaru ya mutu?
6 Kristi ya nuna wasu cikin halayensa sa’ad da abokinsa Li’azaru ƙaunatacce ya mutu. Ya yi baƙin ciki sosai sa’ad da Maryamu da Martha suke kuka da bai iya riƙe zafin da yake ji a ransa ba, kuma “ya yi kuka.” Ya ji “zafi a ransa” ya yi baƙin ciki sosai, ko da ya san cewa ba da daɗewa ba zai ta da Li’azaru. Ƙauna da juyayi sun motsa Yesu ya nuna ikon da Allah ya ba shi kuma ya ta da Li’azaru daga matattu.—Yohanna 11:11-15, 33-35, 38-44.
7. Me ya sa Yesu ya cancanci mu yi masa hidima? (Ka duba akwati da ke shafi na 31.)
7 Muna mamaki game da yadda Yesu yake ƙaunar abin da ke daidai da yadda ya tsane riya da mugunta. Sau biyu ya ɗauki mataki da gaba gaɗi ya kawar da attajirai masu haɗama daga haikali. (Matta 21:12, 13; Yohanna 2:14-17) Ban da haka, da yake ya zauna a duniya, ya sha wahala iri iri, wannan ya taimake shi ya san matsi da matsaloli da muke fuskanta. (Ibraniyawa 5:7-9) Yesu ya kuma san yadda mutum yake ji idan ya fuskanci ƙiyayya da rashin gaskiya. (Yohanna 5:15-18; 11:53, 54; 18:38–19:16) A ƙarshe, ya ba da ransa, da gabagaɗi ya yi mutuwa ta zalunci don ya cika nufin Ubansa kuma ya ba talakawansa rai madawwami. (Yohanna 3:16) Irin wannan halaye na Kristi bai motsa ka ka ci gaba da yi masa hidima cikin aminci ba? (Ibraniyawa 13:8; Ru’ya ta Yohanna 5:6-10) Menene ake bukata don a zama talakan Sarki Kristi?
Yadda Za a Cancanci Zama Talaka
8. Menene ake bukatar daga talakawan Kristi?
8 Ka yi tunanin wannan kwatancin: Kafin mutum ya zama mazaunin wata ƙasa yana bukatar ya cika wasu farillai. Za a bukaci waɗanda za su zama mazauna su kasance da halin kirki da cikakkiyar lafiyar jiki. Hakanan ma, talakawan Kristi suna bukatar su kasance da mizanan ɗabi’a masu kyau da kuma koshin lafiya ta ruhaniya.—1 Korinthiyawa 6:9-11; Galatiyawa 5:19-23.
9. Ta yaya za mu nuna mu masu aminci ne ga Kristi?
9 Yesu Kristi na bukatar talakawansa su kasance da aminci gare shi da kuma Mulkinsa. Suna kasancewa da aminci ta wajen rayuwa cikin jituwa da abin da ya koyar sa’ad da yake duniya, da yake shi ne Sarki da aka naɗa. Alal misali, suna saka abubuwa na Mulki da nufin Allah a kan gaba da biɗan abin duniya. (Matta 6:31-34) Suna iya ƙoƙarinsu su nuna halin Kristi, har lokacin da suke cikin yanayi mai wuya. (1 Bitrus 2:21-23) Ƙari ga haka, talakawan Kristi suna bin misalinsa ta wajen yi wa mutane nagarin abu.—Matta 7:12; Yohanna 13:3-17.
10. Ta yaya za a nuna aminci ga Kristi (a) a cikin iyali da (b) ikilisiya?
10 Mabiyan Yesu suna kuma nuna amincinsu gare shi ta wajen nuna halinsa cikin iyali. Alal misali, magidanta suna nuna aminci ga Sarkinsu na samaniya ta yin koyi da Kristi a yadda suke bi da matansu da yaransu. (Afisawa 5:25, 28-30; 6:4; 1 Bitrus 3:7) Mata suna nuna aminci ga Kristi ta halayensu masu kyau da kuma nuna “ruhu mai-ladabi mai lafiya.” (1 Bitrus 3:1-4; Afisawa 5:22-24) Yara suna nuna aminci ga Kristi sa’ad da suka bi misalinsa na biyayya. Lokacin da yake matashi, Yesu ya yi wa iyayensa biyayya, ko da su ajizai ne. (Luka 2:51, 52; Afisawa 6:1) Talakawan Kristi suna ƙoƙari su yi koyi da shi da aminci ta wajen zama “masu-juyayi, [s]una yin ƙauna kamar ’yan’uwa” da kuma zama “masu-tabshin zuciya.” Suna ƙoƙari su zama kamar Kristi, su zama “masu-tawali’u; ba masu-rama mugunta da mugunta ba, ba kuwa zagi da zagi ba.”—1 Bitrus 3:8, 9; 1 Korinthiyawa 11:1.
Talakawa Masu Bin Doka
11. Talakawan Kristi suna biyayya ga waɗanne dokoki?
11 Kamar yadda waɗanda suke son su zama mazaunan ƙasa suke bin dokoki na sabuwar ƙasarsu, talakawan Kristi suna biyayya ga “shari’ar Kristi” ta yin rayuwa daidai da dukan abin da Yesu ya koyar da kuma umurninsa. (Galatiyawa 6:2) Musamman suna rayuwa cikin aminci ta “shari’an nan ba’sarauciya” ta ƙauna. (Yaƙub 2:8) Menene waɗannan dokoki suka ƙunsa?
12, 13. Ta yaya muke miƙa kai ga “shari’ar Kristi”?
12 Talakawan Kristi ajizai ne kuma suna da kasawa. (Romawa 3:23) Saboda haka, suna bukatar su ci gaba da koyan “sahihiyar ƙauna ta ’yan’uwa” domin su ‘yi ƙaunar junansu daga zuciya mai-gaskiya.’ (1 Bitrus 1:22) “Idan kowanne mutum yana da maganar ƙara game da wani,” Kiristoci cikin aminci suna amfani da shari’ar Kristi ta ‘haƙuri da juna, suna gafarta ma juna.’ Yin biyayya da wannan dokokin na taimakonsu su ƙyale ajizanci kuma su nemi dalilin ƙaunar juna. Ba ka godiya ka kasance da waɗanda suke miƙa kai cikin aminci ga Sarkinmu mai ƙauna kuma su yafa kansu da ƙauna, “magamin kamalta”?—Kolossiyawa 3:13, 14.
13 Bugu da ƙari, Yesu ya yi bayani cewa ƙauna da ya nuna ta fi ƙauna da mutane ke wa juna. (Yohanna 13:34, 35) Idan muna ƙaunar waɗanda suke ƙaunarmu kawai, ba mu “fi waɗansu” ba. Idan haka ne, ba ma ƙauna. Yesu ya aririce mu mu yi koyi da ƙaunar Ubansa ta wurin nuna ƙauna mai ƙa’ida har ga magabta da suka tsane mu kuma suke tsananta mana. (Matta 5:46-48) Wannan ƙaunar na motsa talakawa na Mulki su nace ga yin ainihin aikinsu cikin aminci. Wane aiki ne wannan?
An Gwada Amincinsu
14. Me ya sa aikin wa’azi yake da muhimmanci ainun?
14 Talakawan Mulkin Allah yanzu suna da aiki mai muhimmanci na “shaida mulkin Allah.” (Ayukan Manzanni 28:23) Yin hakan na da muhimmanci domin Mulkin Almasihu zai kunita ikon mallaka na Jehobah. (1 Korinthiyawa 15:24-28) Sa’ad da muke wa’azin bishara, masu sauraro suna da zarafin zama talakawan Mulkin Allah. Ƙari ga haka, yadda mutane suke aikata ga wannan saƙon zai zama mizanin da Kristi Sarki zai yi amfani da shi ya shari’anta ’yan adam. (Matta 24:14; 2 Tassalunikawa 1:6-10) Saboda haka, hanya ta musamman da za mu nuna amincinmu ga Kristi ita ce ta yin biyayya ga umurninsa na gaya wa mutane game da Mulkin.—Matta 28:18-20.
15. Me ya sa ake gwada amincin Kiristoci?
15 Hakika, Shaiɗan na iyakar ƙoƙarinsa ya hana aikin wa’azi, kuma sarakunan ’yan adam ba su amince da ikon da Allah ya ba Kristi ba. (Zabura 2:1-3, 6-8) Shi ya sa, Yesu ya gargaɗi manzanninsa: “Bawa ba ya fi ubangijinsa girma ba. Idan suka yi mani tsanani, su a yi maku tsanani kuma.” (Yohanna 15:20) Saboda haka, mabiyan Kristi suna yaƙi na ruhaniya da ke gwada amincinsu.—2 Korinthiyawa 10:3-5; Afisawa 6:10-12.
16. Ta yaya talakawan Mulki suka ba “Allah kuma abin da ke na Allah”?
16 Saboda haka, talakawan Mulkin Allah suna kasancewa da aminci ga Sarkinsu marar ganuwa amma ba sa rashin biyayya ga masu mulki na ’yan adam. (Titus 3:1, 2) Yesu ya ce: “Ku ba Kaisar abin da ke na Kaisar, Allah kuma abin da ke na Allah.” (Markus 12:13-17) Shi ya sa, talakawan Kristi suke biyayya ga dokokin gwamnati da ba su saɓa da dokokin Allah ba. (Romawa 13:1-7) Amma, sa’ad da babban kotu na Yahudawa suka ƙeta dokokin Allah ta wurin ba almajiran Yesu umurni su daina wa’azi, almajiran sun faɗa da gabagaɗi cewa za su “fi biyayya ga Allah da mutane.”—Ayukan Manzanni 1:8; 5:27-32.
17. Me ya sa za mu bi da gwajin aminci da gaba gaɗi?
17 Hakika, talakawan Kristi suna bukatar gaba gaɗi sosai don su kasance da aminci ga Sarkinsu sa’ad da suke fuskantar tsanani. Duk da haka Yesu ya ce: “Masu-albarka ne ku lokacinda ana zarginku, ana tsananta muku, da ƙarya kuma ana ambatonku da kowacce irin mugunta, sabili da ni. Ku yi farinciki, ku yi murna ƙwarai: gama ladarku mai-girma ce cikin sama.” (Matta 5:11, 12) Mabiyan Kristi na farko sun shaida gaskiyar waɗannan kalmomin. Ko lokacin da aka yi musu bulala don sun ci gaba da wa’azi game da Mulkin, sun yi farin ciki domin “sun isa su sha ƙanƙanci sabili da Sunan. Kowace rana fa, cikin haikali da cikin gida, ba su fāsa koyarwa da yin wa’azi kuma Yesu Kristi ne.” (Ayukan Manzanni 5:41, 42) Kun cancanci a yaba muku, yayin da kuke nuna irin wannan aminci sa’ad da kuke jimrewa da wahala, ciwo, rashin wanda kuke ƙauna, ko kuma hamayya.—Romawa 5:3-5; Ibraniyawa 13:6.
18. Menene abin da Yesu ya gaya wa Bilatus Babunti ya nuna?
18 Sa’ad da aka naɗa Yesu Sarki, ya yi wa Bilatus Babunti Gwamna daga Roma, bayani cewa: “Mulkina ba na wannan duniya ba ne: da mulkina na wannan duniya ne, da ma’aikatana su a yi yaƙi, domin kada a bashe ni cikin hannun Yahudawa, amma yanzu mulkina ba daga nan ya ke ba.” (Yohanna 18:36) Shi ya sa talakawan Mulkin samaniya ba sa ɗaukan makamai ko kuwa su goyi bayan yaƙi na ’yan adam. Domin suna aminci ga “Sarkin Salama,” ba sa saka hannu cikin harkokin rukuni na wannan duniya.—Ishaya 2:2-4; 9:6, 7.
Talakawa Masu Aminci Suna da Lada na Dindindin
19. Me ya sa talakawan Kristi za su jira nan gaba da tabbaci?
19 Talakawan Kristi “Sarkin sarakuna,” masu aminci suna sauraron nan gaba da tabbaci. Suna ɗokin ganin yadda zai nuna ikon sarautarsa mafifici ba daɗewa ba. (Ru’ya ta Yohanna 19:11–20:3; Matta 24:30) Masu aminci da suka rage da aka shafa da ruhu, wato, “ ’ya’yan mulki” suna sauraron gadōnsu mai tamani na zaman sarakuna da Kristi a sama. (Matta 13:38; Luka 12:32) “Waɗansu tumaki” na Kristi masu aminci suna jiran amincewar Sarkinsu, sa’ad da zai ce: “Zo, ku masu-albarka na Ubana, ku gaji [aljanna a duniya na] mulkin da an shirya dominku tun kafawar duniya.” (Yohanna 10:16; Matta 25:34) Saboda haka, bari dukan talakawan Mulkin su ƙuduri aniya su ci gaba da yi wa Kristi Sarki hidima cikin aminci.
[Hasiya]
a Ka duba littafin nan Reasoning From the Scriptures, “Me ya sa Shaidun Jehobah suka ce an kafa Mulkin Allah a shekara ta 1914?” shafuffuka 95-97, Shaidun Jehobah ne suka wallafa.
Za Ka Iya Bayanawa?
• Me ya sa ya dace mu amince da Kristi?
• Ta yaya talakawan Kristi suke nuna amincinsu gare shi?
• Me ya sa ya kamata mu kasance da aminci ga Sarki Kristi?
[Akwati a shafi na 31]
ƘARIN HALAYEN KRISTI NA MUSAMMAN
Rashin son kai—Yohanna 4:7-30.
Juyayi—Matta 9:35-38; 12:18-21; Markus 6:30-34.
Ƙauna na sadaukar da kai—Yohanna 13:1; 15:12-15.
Aminci—Matta 4:1-11; 28:20; Markus 11:15-18.
Tausayi—Markus 7:32-35; Luka 7:11-15; Ibraniyawa 4:15, 16.
Sanin ya kamata—Matta 15:21-28.
[Hoto a shafi na 29]
Ta wajen ƙaunar juna, muna bin “shari’ar Kristi” cikin aminci
[Hotuna a shafi na 31]
Halayen Kristi suna motsa ka ka yi masa hidima ne?