WAƘA TA 149
Waƙar Nasara
Hoto
	(Fitowa 15:1)
- 1. Mu yabi Allah, mu ɗaukaka sunan Jehobah. - Ya hallaka Fir’auna da duk mayaƙansa. - Mu yabi Allah, - Babu wani Allah kamar sa. - Jehobah na da iko - A kan maƙiyansa. - (AMSHI) - Jehobah Allah Maɗaukaki, - Ba za ka canja ba har abada. - Za ka hallaka duk maƙiyanka - Don ka ɗaukaka sunanka. 
- 2. Allah Jehobah, zai kunyatar da duk al’umma, - Don suna yin tsayayya - Da Mulkinsa sosai. - Yesu Ɗan Allah, - Zai cire su da Armageddon, - Jama’a za su ɗaukaka - Sunan Jehobah. - (AMSHI) - Jehobah Allah Maɗaukaki, - Ba za ka canja ba har abada. - Za ka hallaka duk maƙiyanka - Don ka ɗaukaka sunanka. 
(Ka kuma duba Zab. 2:2, 9; 92:8; Mal. 3:6; R. Yoh. 16:16.)