WAƘA TA 82
‘Mu Bari Haskenmu Ya Haskaka’
Hoto
	- 1. Yesu ya ce mana - Mu haskaka fa, - Kamar ranar da ke - Haska ko’ina. - Kalmar Allah tana - Da iko sosai. - Mu sa a ga hasken nan - Ta wa’azinmu. 
- 2. Mu riƙa wa’azi - Ga duk mutane. - Don mu ’yantar da su - Daga duhun nan. - Maganar Jehobah - Muke yaɗawa. - Za ta taimaka musu - Su bauta masa. 
- 3. Muna haskakawa - Ta halayenmu, - Furucinmu kuma - Na da daraja. - Bari mu haskaka - Ta ayyukanmu, - Hakan zai faranta ran - Allah Jehobah. 
(Ka kuma duba Zab. 119:130; Mat. 5:14, 15, 45; Kol. 4:6.)