WAƘA TA 38
Zai Ƙarfafa Ka
(1 Bitrus 5:10)
- 1. Akwai wani dalilin da ya sa Allah - Ya jawo ka cikin ƙungiyarsa. - Ya san cewa kana so ka san nufinsa - Don ka riƙa aikata nagarta. - Ka yi alkawarin yin nufinsa, - Shi kuma zai riƙa taimaka ma. - (AMSHI) - Ya fanshe ka da jinin, - Ɗansa Yesu Kristi. - Shi zai taimake ka, - shi zai ƙarfafa ka. - Zai ci gaba da kāre ka, - babu fasawa. - Shi zai taimake ka, - shi zai ƙarfafa ka. 
- 2. Allah ya ba da Ɗansa a madadin ka, - Domin yana son ka sami ceto. - In ya ba da Ɗansa wanda yake ƙauna, - Ka tabbata shi zai taimake ka. - Ba zai manta da amincinka ba, - Ba zai manta da abokansa ba. - (AMSHI) - Ya fanshe ka da jinin, - Ɗansa Yesu Kristi. - Shi zai taimake ka, - shi zai ƙarfafa ka. - Zai ci gaba da kāre ka, - babu fasawa. - Shi zai taimake ka, - shi zai ƙarfafa ka. 
(Ka kuma duba Rom. 8:32; 14:8, 9; Ibran. 6:10; 1 Bit. 2:9.)