Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • lv p. 222-p. 223 par. 3
  • Sasanta Matsala Tsakanin ’Yan Kasuwa

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Sasanta Matsala Tsakanin ’Yan Kasuwa
  • “Ku Tsare Kanku Cikin Ƙaunar Allah”
  • Makamantan Littattafai
  • Ku Biɗi Salama
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
  • Ku Sasanta Matsalolinku Cikin Kauna
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2016
  • Bari Ikilisiya Ta Ingantu
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2007
  • Dattawa—Ku Ci-gaba da Yin Koyi da Manzo Bulus
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2022
“Ku Tsare Kanku Cikin Ƙaunar Allah”
lv p. 222-p. 223 par. 3

RATAYE

Sasanta Matsala Tsakanin ’Yan Kasuwa

Kamar yadda yake rubuce a 1 Korintiyawa 6:1-8, manzo Bulus ya tattauna batun kai ƙara kotu tsakanin masu bi. Ya nuna rashin jin daɗinsa cewa wasu Kiristoci a Koranti suna kai ’yan’uwansu kotu “gaban azalumai.” (Aya ta 1) Bulus ya ba da dalilai masu ƙwari da ya sa bai kamata Kiristoci su kai juna kotu ba maimakon haka su sasanta cikin ikilisiya. Bari mu tattauna wasu dalilai domin wannan gargaɗi da aka hure kuma mu mai da hankali ga wasu yanayi kalilan waɗanda wannan umurnin bai yi magana a kan su ba.

Idan muna da wata jayayyar kasuwanci tsakanin mu da wani ɗan’uwa mai bi, da farko mu yi ƙoƙari mu magance matsalar a hanyar da Jehobah yake so. (Misalai 14:12) Kamar yadda Yesu ya nuna, ya fi a magance jayayya da wuri kafin ta girma ta zama babbar matsala. (Matta 5:23-26) Abin baƙin ciki, wasu Kiristoci sukan zama masu rikici ƙwarai, har su kai ƙara zuwa kotu. Bulus ya ce: “Ya zama abin hasara a gareku ƙwarai, da ku ke kai juna ƙara a gaban shari’a.” Me ya sa? Wani dalili shi ne cewa hakan zai shafi suna mai kyau na ikilisiya da kuma Allah da muke bauta wa. Saboda haka mu tuna da tambayar Bulus: “Ba gwamma a yi haƙuri da zalunci ba?”—Aya ta 7.

Bulus kuma ya nuna cewa Allah ya bai wa ikilisiya tsari mai kyau na sasantawa. Wannan tsarin shi ne dattawa Kiristoci da suke da hikima domin sanin da suke da shi na gaskiyar Nassosi, kuma Bulus ya ce suna iya “raba musu tsakanin ’yan’uwa.” (Ayoyi na 3-5) Yesu ya nuna cewa jayayya da ya shafi laifi mai tsanani, kamar ɓata suna ko kuma zamba, ya kamata a magance su bisa matakai uku: na farko, masu jayayya su yi ƙoƙari su magance matsala tsakaninsu su biyu: na biyu, idan matakin farko bai yi nasara ba, ka shigo da mutum ɗaya ko biyu; na uku kuma; idan matakai biyu na farko ba su yi nasara ba, ka sanar da batun ga ikilisiya da dattawa suke wakiltanta.—Matta 18:15-17.

Hakika, dattawa Kiristoci ba lauyoyi ba ne ko kuma ’yan kasuwa kuma ba sa bukatar su kasance hakan. Ba su suke kafa mizanai na sasanta jayayya ta kasuwanci tsakanin ’yan’uwa ba. Maimakon haka, suna ƙoƙari ne su taimaki dukan waɗanda abin ya shafa su yi amfani da Nassosi kuma su yarda su sasanta cikin zumunci. Idan batutuwa suka yi wuyan fahimta, suna iya tuntuɓar mai kula da da’ira ko kuma ofishin reshe na Shaidun Jehobah. Amma da akwai wasu yanayi da gargaɗin Bulus bai taɓa ba. Waɗanne yanayi ne waɗannan?

A wasu yanayi, kai ƙara kotu wajibi ne kawai na doka domin kawo ƙarshen wani abu cikin salama. Alal misali, kai ƙara kotu hanya ce da za a iya kashe aure, ɗaukan hakkin renon yaro, ba da kuɗin tallafi don kula da yara, biyan kuɗin inshora, cinye kuɗin jari, da kuma tabbatar da ingancin wata wasiyya. Da akwai kuma lokatai da ɗan’uwa ya shigar da ƙara domin ya kāre kansa daga wata ƙara da aka kai gaban kotu.a

Idan an kai irin waɗannan ƙararaki ne a kotu ba tare da ruhun tsatsaguwa ba, ba za su saɓa wa gargaɗi da Bulus ya bayar ba.b Duk da haka, abu mafi muhimmanci ga Kirista shi ne tsarkake sunan Jehobah da kwanciyar hankali da haɗin kai na ikilisiya. Abin da ya bambanta Kiristoci na gaskiya da wasu ita ce ƙaunarsu, kuma “ƙauna . . . ba ta biɗa ma kanta.”—1 Korintiyawa 13:4, 5; Yohanna 13:34, 35.

a A wasu yanayi kuma da suke faruwa da ƙyar, wani Kirista zai aikata laifi mai tsanani ga wani Kirista, kamarsu fyaɗe, kai farmaki, kisa, ko kuma sata mai yawa. A irin wannan ba zai ƙeta dokar tafarkin Kiristanci ba idan aka kai ƙara ga hukuma, ko da yake yin haka zai kai ga shari’a a kotu.

b Domin ƙarin bayani, don Allah dubi Hasumiyar Tsaro ta 15 ga Maris, 1997, shafuffuka na 17-22, da kuma na 15 ga Oktoba, 1991, shafuffuka na 25-28, a Turanci.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba