Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • lff darasi na 19
  • Shaidun Jehobah Kiristoci Ne na Gaske?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Shaidun Jehobah Kiristoci Ne na Gaske?
  • Ka Ji Dadin Rayuwa Har Abada!​—Don Nazarin Littafi Mai Tsarki
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • KA YI BINCIKE SOSAI
  • TAƘAITAWA
  • KA BINCIKA
  • Yadda Za Ka San Kiristoci na Gaske
    Ka Ji Dadin Rayuwa Har Abada!​—Don Nazarin Littafi Mai Tsarki
  • Ka San Gaskiya Game da Allah Kuwa?
    Ka Ji Dadin Rayuwa Har Abada!​—Don Nazarin Littafi Mai Tsarki
  • Me Ya Sa Ake Kiran Mu Shaidun Jehobah?
    Su Wane Ne Suke yin Nufin Jehobah A Yau?
  • Su Wane ne Suke Wa’azin Labari Mai Dadi?
    Ka Ji Dadin Rayuwa Har Abada!​—Don Nazarin Littafi Mai Tsarki
Dubi Ƙari
Ka Ji Dadin Rayuwa Har Abada!​—Don Nazarin Littafi Mai Tsarki
lff darasi na 19
Darasi na 19. Shaidun Jehobah suna magana da juna a gaban Majami’ar Mulkinsu.

DARASI NA 19

Shaidun Jehobah Kiristoci Ne na Gaske?

Hoto
Hoto
Hoto

Me ya sa Shaidun Jehobah suka gaskata cewa su Kiristoci ne na gaske? Daga ina ne muka sami abin da muka yi imani da shi? Ta yaya muka sami sunan nan Shaidun Jehobah? Ta yaya muke nuna cewa muna ƙaunar juna?

1. Daga ina ne Shaidun Jehobah suka samo abin da suka yi imani da shi?

Yesu ya ce: “Kalmar [Allah] kuwa ita ce gaskiya.” (Yohanna 17:17) Kamar Yesu, Shaidun Jehobah sun samo abin da suka yi imani da shi daga Kalmar Allah. Alal misali, ka yi la’akari da tarihinmu. A misalin shekara ta 1870, wasu mutane sun soma nazarin Littafi Mai Tsarki don su fahimci ainihin abin da yake koyarwa. Sun yi imani da duk abin da Littafi Mai Tsarki ya faɗa, ko da ya yi dabam da abin da ake koyarwa a coci. Sai suka soma koya wa mutane abin da suka koya daga Littafi Mai Tsarki.a

2. Ta yaya muka sami sunan nan Shaidun Jehobah?

Jehobah yana kiran bayinsa shaidunsa domin suna koyar da gaskiya game da shi. (Ibraniyawa 11:4–12:1) Alal misali, a zamanin dā, Allah ya gaya wa mutanensa cewa: “Ku ne shaiduna.” (Karanta Ishaya 43:10.) An kira Yesu “amintacce mai shaida.” (Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 1:5) Abin da ya sa muka zaɓi sunan nan Shaidun Jehobah a shekara ta 1931 ke nan. Muna alfahari da wannan sunan.

3. Ta yaya Shaidun Jehobah suke nuna ƙauna kamar Yesu?

Yesu ya ƙaunaci almajiransa sosai, har sun zama kamar iyali a gare shi. (Karanta Markus 3:35.) Hakazalika, Shaidun Jehobah suna da haɗin kai kamar iyali a duk faɗin duniya. Shi ya sa muke kiran juna ’yan’uwa. (Filimon 1, 2) Muna biyayya da umurnin nan da ya ce: “Ku ƙaunaci ’yan’uwa masu bin Yesu.” (1 Bitrus 2:17) Shaidun Jehobah suna nuna wannan ƙaunar a hanyoyi da yawa. Alal misali, muna taimakon ’yan’uwanmu a faɗin duniya a lokacin da suke cikin matsala.

KA YI BINCIKE SOSAI

Za mu koyi tarihin Shaidun Jehobah da kuma wasu abubuwan da suka nuna cewa mu Kiristoci ne na gaske.

Hotuna: Shaidun Jehobah suna wa’azi. 1. Wata ’yar’uwa tana karanta wani nassi kuma tana bayyana ma wata mata. 2. Wani dan’uwa yana ma wani wa’azi a wurin da ake wa’azi da amalanke.

Kiristoci na gaske sun samo abin da suka yi imani da shi a Littafi Mai Tsarki kuma suna koya wa mutane

4. Mun samo abin da muka yi imani da shi daga Littafi Mai Tsarki

Jehobah ya annabta cewa za mu ƙara fahimtar koyarwar Littafi Mai Tsarki. Ku karanta Daniyel 12:​4, sai ku tattauna tambayar nan:

  • Mene ne zai ‘ƙaru’ yayin da mutanen Allah suka ci gaba da nazarin Littafi Mai Tsarki?

Za ka koyi yadda ɗaliban Littafi Mai Tsarki, har da Charles Russell suka yi nazarin Kalmar Allah. Ku kalli BIDIYON nan, sai ku tattauna tambayar da ke gaba.

BIDIYO: Yadda Aka Sake Gano Gaskiyar da Ke Littafi Mai Tsarki (7:45)

  • A bidiyon, ta yaya Charles Russell da sauran ɗaliban suka yi nazarin Littafi Mai Tsarki?

Ka sani?

A wasu lokuta, mukan canja wasu abubuwan da muka yi imani da su. Me ya sa? Kamar yadda hasken rana yake ɓullowa a hankali, haka ma Allah yake sa mu fahimci Kalmarsa a hankali. (Karanta Karin Magana 4:18.) Ko da yake Littafi Mai Tsarki bai canja ba, mukan ɗan yi gyara a kan abubuwan da muka yi imani da su yayin da muka ƙara fahimtar Littafi Mai Tsarki.

5. Muna rayuwar da ta yi daidai da sunanmu

Me ya sa muka zaɓi sunan nan Shaidun Jehobah? Ku kalli BIDIYON nan, sai ku tattauna tambayar da ke gaba.

BIDIYO: Sunan da Yake Bambanta Mu (2:40)

  • Me ya sa sunan nan Shaidun Jehobah ya dace?

Me ya sa Jehobah ya zaɓi mutane su zama shaidunsa? Domin su ne za su gaya wa mutane cewa shi ne Allah na gaskiya, da yake an yi ƙaryace-ƙaryace da yawa game da shi. Ka yi la’akari da biyu cikinsu.

Wasu addinai suna koya wa mabiyansu cewa Allah yana so su yi amfani da gumaka a bautarsu. Amma ku karanta Littafin Firistoci 26:​1, sai ku tattauna tambayoyin nan:

  • Abin da suka faɗa gaskiya ne? Yaya Jehobah yake ji game da gumaka?

Wasu malaman addinai suna koyar cewa Yesu shi ne Allah. Amma, ku karanta Yohanna 20:​17, sai ku tattauna tambayoyin nan:

  • Abin da suka faɗa gaskiya ne? Yesu shi ne Allah?

  • Yaya kake ji game da yadda Jehobah ya tura Shaidunsa su koyar da gaskiya game da shi da kuma Ɗansa?

6. Muna ƙaunar juna

Littafi Mai Tsarki ya ce ya kamata Kiristoci su kasance da haɗin kai kamar gaɓoɓin jikin ’yan Adam. Ku karanta 1 Korintiyawa 12:​25, 26, sai ku tattauna tambayoyin nan:

  • Mene ne ya kamata Kiristoci na gaske su yi sa’ad da ’yan’uwansu suke shan wahala?

  • Mene ne ra’ayinka game da yadda Shaidun Jehobah suke ƙaunar juna?

Idan Shaidun Jehobah a wani wuri suna shan wahala, ’yan’uwansu a faɗin duniya suna taimaka musu nan da nan. Don ku ga wani misali, ku kalli BIDIYON nan. Sai ku tattauna tambayar da ke gaba.

BIDIYO: Yadda ’Yan’uwa a Haiti Suka Jimre Guguwar Hurricane Matthew (5:​29)

  • Ta yaya yadda Shaidun Jehobah suke tsara aikin ba da agaji ya nuna cewa suna ƙaunar juna?

Shaidu biyu suna taimaka ma wata mata da danta da bala’i ya auku a wurin da suke. Sun lullube su da bargo kuma suka ba su ruwan sha.

Kiristoci na gaske suna taimaka wa waɗanda suke cikin matsala

WASU SUN CE: “Shaidun Jehobah sabon addini ne kawai.”

  • Tun wane lokaci ne Jehobah ya soma kiran bayinsa shaidu?

TAƘAITAWA

Shaidun Jehobah Kiristoci ne na gaske. Mu ’yan’uwa ne a faɗin duniya, mun samo abin da muka yi imani da shi a Littafi Mai Tsarki kuma muna koya wa mutane gaskiya game da Jehobah.

Bita

  • Me ya sa muka zaɓi sunan nan Shaidun Jehobah?

  • Ta yaya muke nuna cewa mun damu da juna?

  • Kana ganin Shaidun Jehobah Kiristoci ne na gaske?

Maƙasudi

KA BINCIKA

Ku kalli bidiyon nan don ku koyi game da tarihinmu.

Shaidun Jehobah Sun Nuna Bangaskiya, Kashi na 1: Sun Sami Haske (English) (1:00:53)

Ku kalli bidiyon nan don ku ga yadda Shaidun Jehobah suka fallasa koyarwar ƙarya.

Bayin Allah Suna Ɗaukaka Sunansa (7:08)

Ku karanta talifin nan don ku sami amsoshin tambayoyi game da Shaidun Jehobah.

“Tambayoyin da Ake Yawan Yi Game da Shaidun Jehobah” (talifin jw.org)

Stephen ya tsani mutanen da launin fatarsu dabam ne da nasa, har ma yana kai musu hari. Ku karanta talifin nan don ku ga abin da ya sa ya canja ra’ayinsa sa’ad da ya soma cuɗanya da Shaidun Jehobah.

“Na Yi Rayuwar Banza Sosai a Dā” (Hasumiyar Tsaro, 1 ga Satumba, 2015)

a Tun daga shekara ta 1879 ne bayin Jehobah suka soma wallafa mujallar Hasumiyar Tsaro don su bayyana abin da Littafi Mai Tsarki yake koyarwa.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba