Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • lff darasi na 53
  • Ka Zabi Nishadi da Zai Faranta Ran Jehobah

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ka Zabi Nishadi da Zai Faranta Ran Jehobah
  • Ka Ji Dadin Rayuwa Har Abada!​—Don Nazarin Littafi Mai Tsarki
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • KA YI BINCIKE SOSAI
  • TAƘAITAWA
  • KA BINCIKA
  • Yadda Za Mu Zabi Nishadin da Ya Dace
    Ku Ci Gaba da Kaunar Allah
  • Yadda Za a Zabi Nishadi Mai Kyau
    “Ku Tsare Kanku Cikin Ƙaunar Allah”
  • Ka Zabi Nishadi Mai Kyau
    Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2019
  • Mu Bauta wa Jehobah da Dukan Zuciyarmu
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2019
Dubi Ƙari
Ka Ji Dadin Rayuwa Har Abada!​—Don Nazarin Littafi Mai Tsarki
lff darasi na 53
Darasi na 53. Baba da mama da yaransu biyu suna cin guguru yayin da suke kallon talabijin.

DARASI NA 53

Ka Zaɓi Nishaɗin da Zai Faranta Ran Jehobah

Hoto
Hoto
Hoto

Jehobah Allah ne mai farin ciki. (1 Timoti 1:11) Yana so mu yi farin ciki kuma mu ji daɗin rayuwa. Yana kuma so mu riƙa hutawa daga aikin da muke yi. A wannan darasin, za mu ga yadda za mu yi amfani da lokacin da muke hutawa a hanyoyi da za mu ji daɗi kuma mu faranta ran Jehobah.

1. Me ya kamata mu yi tunani a kai sa’ad da muke zaɓan nishaɗi?

Me kake jin daɗin yi sa’ad da kake shaƙatawa? Wasu mutane sun fi so su huta a gida suna karatu ko suna shan kiɗi ko kallon fim ko kuma su shiga Intane. Wasu kuma suna jin daɗin kasancewa da abokansu, suna hawan duwatsu ko su yi iyo ko su yi wasanni iri-iri. Ko da wane irin nishaɗi ne muka fi so, ya kamata mu tabbata cewa “abin da zai gamshi Ubangiji” ne. (Afisawa 5:10) Yana da muhimmanci mu san hakan domin ana nuna zalunci ko lalata ko kuma sihiri a nishaɗi da yawa da ake da su a yau kuma hakan ba su jitu da ra’ayin Jehobah ba. (Karanta Zabura 11:5.) Mene ne zai taimaka mana mu zaɓi nishaɗin da ya dace?

Idan abokanmu masu ƙaunar Jehobah ne, za su iya taimaka mana mu zaɓi nishaɗin da ya dace. Kamar yadda muka koya a darasi na 48, “wanda ya yi tafiya tare da masu hikima zai kasance da hikima.” Amma idan muna abota da mutanen da ba sa bin ƙa’idodin Allah, za mu sha wahala kuma mu “lalace.”​—Karin Magana 13:20.

2. Me ya sa yake da muhimmanci mu rage yawan lokaci da muke nishaɗi?

Ko da nishaɗin da muke yi ba zai shafi dangantakarmu da Jehobah ba, bai kamata mu ɓata lokaci da yawa muna yin su ba. Idan muna yin haka, ba za mu sami isashen lokaci na yin ayyuka masu muhimmanci ba. Littafi Mai Tsarki ya gaya mana cewa mu ‘yi amfani da lokacinmu da kyau.’​—Karanta Afisawa 5:​15, 16.

KA YI BINCIKE SOSAI

Za mu koyi yadda za mu tsai da shawarwari masu kyau game da nishaɗi.

3. Ka guji nishaɗi marar kyau

Me ya sa za mu mai da hankali sa’ad da muke zaɓan nishaɗi? Ku kalli BIDIYON nan, sai ku tattauna tambayoyin da ke gaba.

BIDIYO: Wane Irin Nishaɗi Ne Zan Zaɓa? (4:​39)

  • Ta yaya wasannin da ake yi a ƙasar Roma ta dā suka yi kama da nishaɗin da ake yi a yau?

  • A bidiyon, mene ne Danny ya koya game da nishaɗi?

Ku karanta Romawa 12:​9, sai ku tattauna tambayar nan:

  • Ta yaya wannan ayar za ta taimaka maka ka zaɓi nishaɗi mai kyau?

Waɗanne abubuwa ne Jehobah ya tsana? Ku karanta Karin Magana 6:​16, 17 da Galatiyawa 5:​19-21. Bayan kun karanta kowane nassi, sai ku tattauna tambayar nan:

  • Wanne cikin abubuwan da aka ambata a ayoyin nan ne ake yawan gani a nishaɗin da ake yi a yau?

Tambayoyin da za su taimaka maka ka zaɓi nishaɗi mai kyau

Ka tambayi kanka:

  • Nishaɗin ya ƙunshi wani abin da Jehobah ya tsana?

  • Zai hana ni yin abubuwa masu muhimmanci ne?

  • Zai sa in riƙa cuɗanya a kai a kai da mutanen da ba sa ƙaunar Jehobah?

Zai fi kyau mu yi nisa daga wani abin da ke da haɗari. Shi ya sa zai dace mu guji duk wani nishaɗin da muke ganin zai ɓata halinmu

Wata mota tana tafiya a kan dutse kusa da bakin wani kwari. Bayan motar tana kokarin kauce wa hanya.

4. Ka yi amfani da lokacinka da kyau

Ku kalli BIDIYON nan, sai ku tattauna tambayar da ke gaba.

BIDIYO: Me Yake Cinye Lokacinka? (2:​45)

  • Ko da yake ɗan’uwan da ke bidiyon ba ya kallon wani abu marar kyau, mece ce matsalarsa?

Ku karanta Filibiyawa 1:​10, sai ku tattauna tambayar nan:

  • Ta yaya wannan ayar za ta taimaka mana mu san yawan lokacin da za mu yi muna yin nishaɗi?

5. Ka zaɓi nishaɗi mai kyau

Ko da yake wasu nishaɗi suna ɓata wa Jehobah rai, akwai waɗanda ba sa ɓata wa Jehobah rai da za mu iya jin daɗinsu. Ku karanta Mai-Wa’azi 8:15 da Filibiyawa 4:​8, sai ku tattauna tambayar nan:

  • Wane nishaɗi ne kake jin daɗinsa?

Hotuna: Yara da manya suna jin dadin tarayya. 1. Wata yarinya tana zane tana sauraron waka. 2. Yara maza uku suna kwalon raga. 3. Yara biyu suna tuka keke. 4. Wani yaro yana kera mota. 5. Wani mutum yana buga ganga. 6. Wani yaro da babansa suna wasa bidiyo. 7. Wata mata tana daukan hoto.

Za ka iya more nishaɗi mai kyau

WASU SUN CE: “Nishaɗin da ya ƙunshi zalunci ko lalata ko sihiri ba laifi ba ne muddin ba na aikata su.”

  • Me za ka ce?

TAƘAITAWA

Jehobah yana so mu zaɓi nishaɗi mai kyau kuma mu ji daɗin sa.

Bita

  • Wane irin nishaɗi ne bai kamata Kiristoci su yi ba?

  • Me ya sa za mu mai da hankali game da yawan lokacin da muke amfani da shi wajen yin nishaɗi?

  • Me ya sa za ka zaɓi nishaɗin da ke faranta ran Jehobah?

Maƙasudi

KA BINCIKA

Ku karanta talifin nan don ku ga wanda yake da hakkin zaɓar mana nishaɗin da za mu yi.

“Shin Kun Haramta Kallon Wasu Fina-Finai ko Karanta Wasu Littattafai ko Kuma Saurarar Wasu Waƙoƙi Ne?” (Talifin jw.org)

Ku karanta talifin nan don ku ga ko waye ne yake da hakkin zaɓar mana nishaɗin da za mu yi.

“Nishaɗin Da Kake Yi Yana Amfane Ka Kuwa?” (Hasumiyar Tsaro, 15 ga Oktoba, 2011)

Ku karanta talifin nan “Na Daina Nuna Ƙiyayya,” don ku ga abin da ya sa wani mutum ya daina nishaɗin da yake yi.

“Littafi Mai Tsarki Yana Canja Rayuka” (Hasumiyar Tsaro, 1 ga Yuli, 2010)

Ku kalli bidiyon nan don ku ga yadda wata mahaifiya ta tsai da shawara mai kyau game da fina-finan sihiri da take kallo.

Ka Guji Nishaɗi da Ake Nuna Sihiri (2:02)

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba