Abubuwan Da Ke Kawo Farin Ciki A Iyali
Ƙalubalen da Sababbin Iyaye Suke Fuskanta
Charles:a “Ni da Mary mun yi farin ciki sosai sa’ad da muka haifi ’yarmu. Amma ban samu isashen barci ba a cikin ’yan watanni bayan haihuwar ta. Mun riga mun tsara yadda za mu kula da ita kuma mu yi renon ta sosai, amma duk waɗannan shirye-shiryen suka ɓace nan da nan.”
Mary: “Tun da na haifi ’yarmu, na kasa sarrafa rayuwata. Abubuwan da kawai suka fi muhimmanci a gare ni su ne abincinta, canja famfas ɗin da ta saka, ko kuma yin lallasa don ta yi shiru. Canjin ba ƙarami ba ne. Sai da na yi watanni kafin dangantakata da Charles ta koma yadda take a dā.”
MUTANE da yawa za su yarda cewa samun ’ya’ya yana ɗaya daga cikin abubuwa masu kawo farin ciki mafi girma a rayuwa. Littafi Mai Tsarki ya kwatanta yara a matsayin ‘lada’ daga Allah. (Zabura 127:3) Sababbin iyaye kamar su Charles da Mary sun san cewa yara suna iya canja aure a wasu hanyoyin da ba a zato. Alal misali, mahaifiyar da ta yi haihuwar farko tana iya mai da hankalinta ga jaririnta sosai har ta yi mamakin yadda take saurin biyan kowace ’yar ƙaramar bukatarsa. Shi kuwa mahaifin da ya yi haihuwar farko, yana iya yin mamakin irin dangantakar da matarsa ta ƙulla da jaririn. Yana kuma iya damuwa cewa an yi watsi da shi.
Hakika, haihuwar farko yana iya jawo tarzoma a cikin aure. Matsalolin da ke tsakanin ma’aurata, da kuma rashin kwanciyar hankalin da ke damun wani a cikinsu yana iya bayyanuwa sosai domin aikin da ke tattare da rainon yara.
Ta yaya iyayen da suka yi haihuwar farko za su iya daidaita yanayinsu don ya jitu da ’yan watannin farko na haihuwa da ke cike da wahala, lokacin da jaririn zai bukaci dukan hankalinsu? Mene ne ma’aurata za su iya yi domin su ci gaba da kasancewa da dangantakarsu ta kud da kud? Ta yaya za su iya warware rashin jituwa game da rainon yara? Bari mu bincika waɗannan ƙalubalen kuma mu duba yadda mizanan Littafi Mai Tsarki za su iya taimaka wa ma’aurata su warware su.
ƘALUBALE NA 1: Hankali ya koma kan jaririn gabaki ɗaya.
Sabon jariri yana ɗauke lokaci da hankalin mahaifiyarsa. Kula da jaririnta yana iya sa ta samu gamsuwa sosai. A lokacin, maigidanta yana iya jin cewa an yi watsi da shi. Manuel, wanda yake zaune a ƙasar Brazil, ya ce: “Wani canjin da ya yi mini wuyar amincewa da shi shi ne yadda matata ta ƙyale ni kuma ta mai da hankalinta ga jaririnmu. A dā, matata tana mai da hankali ne a kan dangantakarmu, amma farat ɗaya, sai hankalinta ya koma kan jaririn kaɗai.” Yaya za ka jure da wannan canjin na ba zato?
▪ Abin da zai sa ku yi nasara: Ka yi haƙuri. “Ƙauna tana da yawan haƙuri, tana da nasiha,” in ji Littafi Mai Tsarki. Ƙauna “ba ta biɗa ma kanta, ba ta jin cakuna.” (1 Korintiyawa 13:4, 5) Sa’ad da suka haifi jariri, mene ne mata da miji za su iya yi don su yi amfani da wannan shawarar?
Miji mai hikima zai tabbatar da ƙaunarsa ga matarsa ta wajen ilimantar da kansa game da yadda haihuwa take shafar mace. Idan ya yi haka, zai gane dalilin da ya sa yanayin matarsa zai iya canjawa daga annashuwa zuwa baƙin ciki.b Adam, wani mahaifi da ke zaune a ƙasar Faransa, kuma yana da ɗiya ’yar wata 11, ya ce: “Canjin yanayin matata yana da wuyan ganewa, kuma hakan yana ƙure ni a wasu lokatai. Amma ina tuna wa kaina cewa ba da ni take fushi ba. Maimakon haka, yadda take bi da matsalolin da canjin yanayinmu ya kawo ne ke sa hakan.”
Matarka tana rashin fahimtar ƙoƙarce-ƙoƙarcenka na taimakawa a wasu lokatai? Idan haka ne, kada ka yi saurin fushi. (Mai-Wa’azi 7:9) A maimakon haka, ka yi haƙuri, ka sa bukatunta a gaban naka, kuma ka guji yin fushi.—Misalai 14:29.
Hakazalika, matar aure mai basira za ta yi ƙoƙarin ƙarfafa maigidanta a sabon matsayinsa. Ya kamata ta sa shi ya saka hannu wajen kula da jaririn, ta nuna masa a hankali yadda ake haɗa abincin jaririn ko kuma canja masa famfas, ko da da farko maigidan bai yi hakan ba da kyau.
Ellen, wata mahaifiya mai shekara 26, ta fahimci cewa tana bukatar yin gyare-gyare a yadda take bi da mijinta. Ta ce, “Ina bukatar in daina mamaye jaririyar. Kuma na tuna wa kaina cewa bai kamata in riƙa nuna rashin gamsuwa ba sa’ad da mijina ya yi ƙoƙarin yin aiki da shawarwarin da na ba shi game da rainon jaririyar.”
KU GWADA WANNAN: Mata, idan mijinku ya yi wani aikin raino a hanyar da ta bambanta da ta ku, ku guji sūkar sa ko kuma ku sake yin aikin da ya yi. Ku yaba masa domin abin da ya yi, kuma ta haka za ku ba shi ƙarfin gwiwa da ƙarfafawa don ya ba ku goyon bayan da kuke bukata. Magidanta, kada ku ɓata lokaci wajen yin ayyukan da ba su da muhimmanci sosai don ku sami isashen lokaci na taimaka wa matarku, musamman ma a cikin ’yan watanni bayan haihuwa.
ƘALUBALE NA 2: Dangantakarku a matsayin ma’aurata ta raunana.
Sababbin iyaye sukan yi gwagwarmaya sosai don su ci gaba da kasancewa kusa da juna saboda rashin samun isashen barci da kuma matsalolin da suke tasowa ba zato. Vivianne, wata mahaifiya a ƙasar Faransa mai ’ya’ya biyu, ta ce: “Da farko, na mai da hankali ne kawai ga cika aiki na a matsayin mahaifiya har na kusan mance da matsayina na matar aure.”
A wani ɓangare kuma, maigida yana iya kasa fahimtar cewa juna biyu ya shafi jikin matarsa da kuma motsin ranta. Yin rainon jariri zai iya ɗauke lokacin da kai da matarka kuka saba yin soyayya da shi a dā. Ta yaya ma’aurata za su tabbata cewa wannan jaririn da ya cancanci ƙaunarsu ba zai jawo saɓani tsakaninsu ba?
▪ Abin da zai sa ku yi nasara: Ku sake tabbatar da ƙaunarku ga juna. Sa’ad da yake kwatanta aure, Littafi Mai Tsarki ya ce: “Mutum za ya rabu da ubansa da uwatasa, ya manne wa matatasa: za su zama nama ɗaya kuma.”c (Farawa 2:24) Nufin Jehobah Allah shi ne cewa yara za su rabu da iyayensu da shigewar lokaci. Akasin haka, Allah yana son gami guda da ke tsakanin mata da miji ya kasance duk rayuwarsu. (Matta 19:3-9) Ta yaya ne sanin wannan gaskiyar zai taimaki ma’aurata da suke da jariri su saka abubuwa masu muhimmanci a gaba?
Vivianne, wacce aka yi ƙaulinta ɗazu, ta ce: “Na yi tunani game da kalmomin da ke Farawa 2:24, kuma wannan ayar ta taimaka mini in fahimci cewa na zama ‘nama ɗaya’ ne da mijina, ba yarona ba. Na ga bukatar ƙarfafa aurenmu.” Theresa, mahaifiyar wata yarinya ’yar shekara biyu, ta ce: “Idan na soma jin cewa na fara nisanta kaina daga mijina, ina ɗaukan mataki nan da nan domin in ba shi dukan hankalina, ko da na ɗan lokaci kaɗan ne kawai a kowace rana.”
Idan kai maigida ne, mene ne za ka iya yi don ka ƙarfafa aurenka? Ka gaya wa matarka cewa kana ƙaunarta. Ka tabbatar da abin da ka ce ta wajen nuna mata ƙauna. Ka ƙoƙarta ka kawar da duk wani tsoron da matarka ke da shi. Sarah, wata mahaifiya ’yar shekara 30, ta ce: “Mace tana bukatar ta san cewa ana daraja ta kuma ana ƙaunar ta, duk da cewa jikinta ya canja saboda tana da ciki.” Alan, wani mahaifin yara biyu da ke da zama a ƙasar Jamus, ya ga muhimmancin biyan bukatar motsin ran matarsa. Ya ce: “A kowane lokaci, ina ƙoƙarin ƙarfafa matata sa’ad da take baƙin ciki.”
Babu shakka, haihuwar jariri yakan katse yin jima’i tsakanin ma’aurata. Saboda haka, maigida da matarsa suna bukatar su tattauna bukatun juna. Littafi Mai Tsarki ya faɗi cewa duk wani canji a batun jima’i tsakanin mata da miji ya kasance cewa su biyun sun amince da hakan da “yardar juna.” (1 Korintiyawa 7:1-5) Hakan yana bukatar tattaunawa. Bisa ga tarbiyyarku ko al’adarku, kuna iya yin jinkirin tattaunawa game da batutuwan da suka shafi jima’i da matarku ko mijinku. Amma irin wannan tattaunawar yana da muhimmanci yayin da ma’aurata suke daidaita yanayinsu sa’ad da suka zama iyaye. Ku kasance da tausayi, haƙuri da kuma gaskiya. (1 Korintiyawa 10:24) Hakan zai sa kai da matarka ku guje wa rashin jituwa kuma ƙaunar da kuke yi wa juna za ta ƙaru.—1 Bitrus 3:7, 8.
Ma’aurata za su kuma iya zurfafa ƙaunar da suke yi wa juna ta wajen nuna godiya. Miji mai hikima zai gane cewa ba a ganin yawancin ayyukan da sabuwar mahaifiya take yi. Vivianne ta ce: “A ƙarshen kowace rana, sau da yawa nakan ji kamar ban yi kome ba, duk da cewa na wuni ne ina hidimar kula da jaririn!” Ko da yake tana hidimomi da dama, mace mai hikima za ta mai da hankali don kada ta rena tallafin da mijinta yake ba iyalin.—Misalai 17:17.
KU GWADA WANNAN: Iyaye mata, idan zai yiwu, ku ma ku ɗan yi barci sa’ad da jaririnku yake barci. Idan kuka yi hakan, za ku samu ƙarin kuzarin tafiyar da al’amuran aurenku. Magidanta, a duk lokacin da ya yiwu, ku tashi da daddare ku ciyar da jaririn ko kuma ku canja masa famfas domin matarku ta huta. Ku riƙa nuna wa matarku ƙauna a kowane lokaci ta wajen rubuta mata ’yar wasiƙa, aika mata saƙo ta wayar tarho, ko kuma tattaunawa da ita a wayar tarho. A matsayin ma’aurata, ku keɓe lokaci don ku zauna ku tattauna da juna. Ku tattauna game da juna, ba game da jaririnku kawai ba. Ku sa dangantakarku a matsayin ma’aurata ta kasance da ƙarfi, hakan zai taimaka muku ku warware matsalolin da ke tattare da zama iyaye.
ƘALUBALE NA 3: Kuna samun rashin jituwa game da yin raino.
Ma’aurata suna iya ganin cewa saboda yadda suka taso, hakan yana yawan sa su yin gardama. Wasu ma’aurata daga ƙasar Japan, Asami da Katsuro, sun fuskanci wannan matsalar. Asami ta ce: “Ina jin cewa Katsuro ya cika yi wa ɗiyarmu sassauci, shi kuma yana jin cewa na cika tsananta mata.” Ta yaya za ku guji samun saɓani a kan wannan batu?
▪ Abin da zai sa ku yi nasara: Ku riƙa tattaunawa da juna, kuma ku taimaka wa juna. Sarki Sulemanu mai hikima ya rubuta: “Ta hanyar girman kai babu abin da ke zuwa sai husuma: amma hikima tana wurin masu karɓan shawarar kirki.” (Misalai 13:10) Me da me kuka sani game da yadda matarku take rainon yara? Idan kuka jira har sai an haifi jaririnku kafin ku soma tattauna hanyoyin raino na musamman, maimakon shawo kan matsalar za ku riƙa yin jayayya da juna.
Alal misali, waɗanne shawarwari ne kuka yanke game da tambayoyin da ke gaba: “Ta yaya za mu iya koya wa ɗanmu ko ’yarmu ɗabi’u masu kyau game da cin abinci da kuma kwanciya?” Ya kamata mu ɗauki jaririn ne a duk lokacin da ya yi kuka sa’ad da muke barci? Ta yaya za mu koya wa jaririn yadda ake amfani da wurin ba-haya?” Babu shakka, shawarwarin da za ku yanke za su bambanta da na wasu ma’auratan. Ethan, mai ’ya’ya guda biyu, ya ce: “Kuna bukatar ku tattauna sosai domin ku kasance da ra’ayi ɗaya.” Da haka, za ku iya biyan bukatun jaririnku tare.
KU GWADA WANNAN: Ku yi tunani a kan dabarun da iyayenku suka yi amfani da su sa’ad da suke rainon ku. Ku tsai da shawara a kan irin halayensu da za ku so ku yi amfani da su sa’ad da kuke rainon ɗanku ko ɗiyarku. Kuma ku tsai da shawara a kan halayen da za ku guje wa, idan akwai. Ku tattauna shawarwarin da kuka yanke da abokiyar aurenku.
Yaro Yana Iya Shafan Aure a Hanya Mai Kyau
Kamar yadda mutum yake bukatar lokaci da haƙuri don ya saba da sabon takalmin da ya saya, kuna bukatar lokaci don ku saba da sabon matsayinku na iyaye. Da sannu sannu, za ku ƙware.
Yin rainon yara ba ƙaramin ƙalubale ba ne, zai jarraba soyayyar da kuke yi wa juna a matsayin mata da miji, kuma zai shafi dangantakarku har abada. Amma, hakan zai ba ku zarafin koyon halaye masu kyau. Idan kuka yi amfani da shawarwari masu kyau da ke cikin Littafi Mai Tsarki, za ku more abin da wani mahaifi mai suna Kenneth ya mora. Ya ce: “Rainon yara ya taimaka wa ni da matata sosai. Mun daina nuna son kai sosai, ƙaunar da muke yi wa juna ta ƙaru kuma muna fahimtar juna sosai.” Hakika ana bukatar irin waɗannan canje-canje a aure.
[Hasiya]
a An canja sunaye a wannan talifin.
b Makonni bayan haihuwa, iyaye mata da yawa suna ɗan yin baƙin ciki. Wasu sukan kamu da wani irin baƙin ciki mai tsanani wanda ake kira postpartum depression. Don ƙarin bayani game da yadda za a gane da kuma jure wannan yanayin, ka duba talifofin nan “I Won My Battle With Postpartum Depression,” a Awake! na 22 ga Yuli, 2002, da kuma “Understanding Postpartum Depression,” a Awake! na 8 ga Yuni, 2003, Shaidun Jehobah ne suka wallafa.
c In ji binciken da wani masani ya yi, wannan aikatau na Ibrananci da aka fassara “manne” a Farawa 2:24 za a iya cewa tana ‘nufin maƙale wa wani a cikin ƙauna da aminci.’
KU TAMBAYI KANKU . . .
▪ A makon da ya shige, mene ne na yi don in nuna wa mijina ko matata cewa ina godiya da abubuwan da take yi ko yake yi wa iyalinmu?
▪ Yaushe rabona da tattaunawa sosai da matata ko mijina game da kanmu ba rainon yara ba?