Abubuwan Da Ke Kawo Farin Ciki A Iyali
Yi Wa Yara Horo
John:a Kafin iyaye na su yi mini horo don laifi da na yi, sukan yi ƙoƙari su fahimci abin da ya sa na yi haka da kuma yanayin. Ina koyi da haka sa’ad da na ke yi wa ’ya’yana horo. Yadda aka yi renon matata ya bambanta. Iyayenta suna da zafin zuciya. Kamar dai suna yi wa yaransu horo ba tare da sun kula da yanayin da ya sa yaron ya aikata abin da bai kamata ba. Wani lokaci ina ganin cewa matata tana yi wa yaranmu horo kamar yadda iyayenta suka yi mata.
Carol: Babana ya bar mu sa’ad da na ke ɗan shekara biyar da haihuwa. Bai nuna yana ƙaunata ko kuma ƙannena uku ba. Mamarmu ta yi ƙoƙari sosai don ta biya bukatunmu, kuma na ɗauki hakkin kula da ƙannena mata. Yana da wuya in yi wasan da yara suke yi don ina yin abubuwan da iyaye suke yi. Har a yanzu kullum ina cikin natsuwa. Idan ina son in yi wa ’ya’yana horo, ina yin tunani sosai game da kuskuren da suka yi. Ina son in san dalilin da ya sa hakan ya faru da kuma abin da suke tunani. Amma maigidana, Mark, ba ya damuwa sosai game da abin da ya faru. Mahaifinsa mutum ne mai nuna wa iyalinsa ƙauna kuma yana kula da matarsa. Maigidana yana magance matsaloli da sauri da yaranmu. Yakan yi tunanin yanayin, sai ya yi gyara kuma ba zai sake tunanin sa ba.
KAMAR yadda kalaman John da Carol suka nuna, yadda aka yi renonka yana iya shafan yadda za ka yi wa yaranka tarbiyya da horo. Saboda mata da miji sun fito daga iyali dabam, suna iya kasancewa da ra’ayi da ya bambanta game da tarbiyyar da yara. Wani lokaci waɗannan sukan jawo matsala a cikin aure.
Matsaloli za su yi yawa idan iyaye sun gaji. Iyaye da suka haifi yaronsu na farko sun fahimta cewa koyar da yaro zai ɗauki lokaci sosai. Joan, wadda ita da maigidanta, Darren, sun yi renon ’ya’ya biyu mata, ta ce: “Ina son ’ya’yana, amma wani lokaci sukan ki su yi barci lokacin da na ke bukata su yi. Sukan tashi a barci a lokacin da bai kamata ba. Sukan hana ni yin magana. Sukan bar takalmansu, tufafinsu da kuma kayan wasansu kuma ba sa mayar da man shanu a inda suka ɗauka ta.”
Jack, wanda matarsa ta shiga cikin wani irin yanayi na bakin ciki da mata suke samu bayan da ta haifi ɗanta na biyu, ya ce: “Zan dawo gida a gajiye daga wajen aiki kuma in zauna har cikin dare da jaririnmu. Hakan ya sa ya kasance da wuya mu yi wa ’yarmu ta fari horo kamar yadda ya dace. Tana kishi don mun mai da hankalinmu ga ƙanwarta.”
Idan iyaye da suka gaji suka yi gardama a kan yadda za su yi wa yaronsu horo, gardamar takan yi tsanani. Idan ba a sasanta ba za ta iya raba ma’auratan kuma za ta iya sa yaron ya riƙa haɗa iyayen rigima. Wane ka’ida na Littafi Mai Tsarki ne zai taimaki ma’aurata su riƙe gami na aure sosai sa’ad da suke koyar da yaransu?
Ma’aurata Su Kasance Tare da Juna
Sun kasance tare da juna kafin su haihu, kuma za su kasance da juna bayan yaran sun bar gida. Game da aure, Littafi Mai Tsarki ya ce: “Abin da Allah ya gama fa, kada mutum shi raba.” (Matta 19:6) Akasin haka, wannan ayar ta nuna cewa nufin Allah shi ne yaro ya “bar ubansa da uwatasa.” (Matta 19:5) Hakika, renon yara wani bangare ne na aure, amma ba shi ne ainihin dalilin aure ba. Hakika, iyaye suna bukatar su ba da lokaci a wajen koyar da yaransu, kuma su tuna cewa aure mai ƙarfi shi ne tushen yadda za a iya yin irin wannan koyarwa.
Wace hanya ɗaya ce za ta sa dangantakar ma’aurata ta ƙarfafa a lokacin da suke renon yaransu? Idan zai yiwu, ku kafa lokaci don ku kasance tare ba tare da yaranku ba. Yin hakan zai sa ku tattauna abubuwa masu muhimmanci a iyalinku kuma ku more kasancewa da juna. Hakika, keɓe lokaci don a zauna tare ban da yara yana da wuya. Alison matar da aka ambata a baya, ta ce, “A lokacin da ni da maigidana muke son mu yi hira tare, sai ’yarmu ƙarama ta soma neman a mai da mata hankali, ko kuma ’yarmu mai shekara shida tana kuka don ba ta ga fencirinta ba.”
Joan da Darren, da aka ambata a baya, sun kafa lokacin da yaransu za su yi barci kuma sun tabbata cewa sun shiga barci a daidai lokacin. Joan ta ce: “Muna bukatar ’ya’yanmu su kwanta a gado su jira lokacin da za mu kashe musu wuta don su yi barci. Wannan ya ba mu ni da Darren lokacin hutu da kuma tattaunawa.”
Ta wajen kafa lokacin kwanciya, ma’aurata za su taimaki ’ya’yansu don kada su ’aza kansu gaba da inda ya kamata.’ (Romawa 12:3) Daga baya, yaran da aka koya musu su yi biyayya ga lokacin da aka kafa na barci za su fahimci cewa ba su kaɗai ba ne suke da muhimmanci a cikin iyali ba, kuma dole ne su yi biyayya ga dokokin iyalin maimakon su sa rai cewa iyalin za ta yi musu abin da suke bukata a kowane lokaci.
GWADA WANNAN: Ka kafa lokacin barci kuma ku tabbata sun kwanta a daidai lokacin. Idan yaronka ya ce zai sha ruwa kafin ya kwanta, za ka iya ƙyale shi ya sha ruwa. Amma kada ka bar yaronka ya canja lokacin barci na dindindin don roƙon abubuwa. Idan yaronka ya roƙa cewa yana son a kara masa minti biyar kuma ka yarda, ka sa agogo ya yi kara idan lokacin da ka kara masa ya cika. Idan agogon ya yi kara, ka sa yaron ya shiga barci ba tare da sauraransa ba. Bari ‘I, da ka ce ya zama I; da A’a, A’a.’—Matta 5:37.
Ku Nuna Haɗin Kai
“Ɗana, ka ji koyarwar ubanka, dokar uwarka kuma kada ka yarda ita,” in ji Misalai. (Misalai 1:8) Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa uba da uwa suna da ’yancin ja-gorancin yaransu. Amma, idan ma’aurata sun fito daga wurare dabam, za su iya samun bambanci game da yadda za su yi wa yaransu horo da kuma irin dokar da ya kamata su kafa. Ta yaya iyaye za su magance wannan matsalar?
John da aka ambata a baya, ya ce, “Bai dace mu nuna rashin jituwa da juna ba a gaban yaranmu.” Amma, ya amince cewa nuna haɗin kai yana da sauƙin faɗi amma da wuyan aikata. John ya ce, “Yara suna lura sosai da abin da ke faruwa. Idan ma ba mu nuna rashin jituwa ba, yaranmu suna gane cewa akwai saɓani a tsakanin mu.”
Ta yaya ne John da Alison suka magance wannan matsalar? Alison ta ce: “Idan ban yarda da yadda maigidana yake yi wa ’yar mu horo ba, ina bari sai ta bar wajen kafin in bayana yadda nake ji. Ba na son ta yi tunani cewa za ta iya ‘raba mu kuma ta yi nasara’ ta wurin yin amfani da bambancin da ke tsakaninmu game da yin horo. Idan ta lura cewa ba mu jitu da juna ba, ina gaya mata cewa kowane a cikin iyali ya kamata ya bi umurnin Jehobah game da shugabanci kuma ina yin biyayya ga shugabancin mahaifinta kamar yadda ita ma za ta yi biyayya ga shugabancinmu.” (1 Korinthiyawa 11:3; Afisawa 6:1-3) John ya ce: “Idan iyalin suna tare, ina yi wa yaranmu gyara. Amma idan Alison ta fahimci yanayin sosai, ina barinta ta yi musu horo sannan in goyi bayanta. Idan ban yarda da abin da ta yi ba, ina tattauna da ita a wani lokaci.”
Yaya za ka hana rashin jituwa game da horon yaro ya jawo matsala tsakaninka da matarka, kuma ya sa yaranka su daina yi maka biyayya?
GWADA WANNAN: Ku zaɓi wani lokaci a kowane mako don ku tattauna game da tarbiyyar da yara, kuma ku tattauna dukan wani rashin jituwa da kuke da shi. Ka fahimci ra’ayin matarka, kuma ka daraja dangantakar da matarka take da shi da ɗanku.
Ku Kusanci Juna
Babu shakka, renon yara ba shi da sauƙi. Wani lokaci, yana gajiyarwa. Amma lokaci zai zo da yaranku za su bar gida, kuma kai da matarka za ku rage ku biyu. Aurenku zai ƙarfafa ko kuma ya lalace domin renon yara? Amsar za ta kasance bisa yadda ka yi amfani da ƙa’idar da ke cikin Mai-Wa’azi 4:9, 10: “Gwamma biyu da ɗaya; domin suna da arziki cikin aikinsu. Gama idan sun fāɗi, ɗaya za ya ɗaga ɗan’uwansa: amma kaiton wanda shi ke shi kaɗai sa’anda ya fāɗi, ba shi da wanda za ya tashe shi.”
Idan iyaye suka yi aiki tare, sakamakon zai yi kyau sosai. Carol da aka ambata a baya, ta ce: “Na san cewa maigidana yana da halaye masu kyau, amma yin renon yaranmu tare ya nuna mini wasu halaye da yawa da yake da su. Daraja da ƙauna da nike yi masa ya ƙarfafa sa’ad da na lura da yadda yake kula da yaranmu cikin ƙauna.” John ya ce wa Alison, “Ganin yadda matata ta zama uwa mai ƙauna ya sa ina ƙaunarta sosai kuma ina darajata.”
Idan ka ba matarka lokaci kuma kuka kasance tare a wajen renon yaranku, aurenku zai ƙarfafa sa’ad da yaranku suna girma. Wataƙila yaranku za su yi koyi da misalinku mai kyau.
[Hasiya]
a An canja sunayen
KA TAMBAYI KANKA . . .
▪ Minti nawa nike yi da matata kowane mako ba tare da yaranmu ba?
▪ Ta yaya nake goyi bayan matata idan tana yi wa yaranmu horo?