Muhimmancin Suna?
Wata ’yar Habasha ta haifi ɗan. Amma sai farin cikinta ya koma ciki da ta ga ɗan ya kwanta a miƙe ba ya motsi. Sa’ad da kakarsa ta ɗauke sa za a yi masa wanka, sai yaron ya fara motsi yana numfashi sai ya fashe da kuka! Suna uban yaron yana nufin “Mu’ujiza,” saboda da haka suka haɗa sunan da wasu kalmomin Amharinci suka kira Yaron An Yi Mu’ujiza.
A ƙasar Burundi, wan saurayi ya gudu daga hannun sojoji da suke so su kashe shi. Sa’ad da yake ɓoye a cikin daji, ya yi wa Allah alkawarin cewa idan Allah ya cece shi, zai saka wa ɗansa na fari suna Manirakiza, wato, “Allah ne Mai Ceto.” Bayan shekara biyar, domin godiya da ya yi ya kasance a raye, ya sa wa ɗansa na fari wannan sunan.
SAKA wa yara sunaye masu ma’ana zai kasance abin mamaki ne a wasu wurare, amma wannan al’ada ta kasance tun a dā. Hakika, Littafi Mai Tsarki ta ƙunshi ɗarurruwan sunaye irin waɗannan. Fahimtar ma’anar sunaye zai kyautata karatunka na Littafi Mai Tsarki. Ga wasu misalai.
Sunaye Masu Ma’anar a Nassosin Ibraniyawa
Seth yana ɗaya daga cikin sunaye da aka fara ambata a cikin Littafi Mai Tsarki, yana nufin, “sanyawa.” Mamarsa Hauwa’u, ta yi bayani game da abin da ya sa ta zaɓi wannan suna, ta ce: “Adamu ya san matatasa kuma; ta kuwa haifi ɗa, ta kira sunansa Seth: “Allah ya sanya mani zuriya maimakon Habila; gama Kayinu ya kashe shi.” (Farawa 4:25) Zuriyar Seth Lamech ya rika ɗansa Nuhu, wato “Hutu” ko kuma “Ta’aziya.” Lamech ya ce ya raɗa wa ɗansa wannan sunan ne domin “Wannan za ya ta’azantar mu domin aikinmu da wahalar hannuwanmu, da ya fito daga ƙasa wadda Ubangiji ya la’anta.”—Farawa 5:29.
Allah ma ya canja sunayen wasu manyan mutane domin annabci. Alal misali, ya canja sunan Abram, mai ma’ana “Uba Yana da Ɗaukaka,” zuwa Ibrahim, wato, “Uban Jama’a.” Hakika kamar sunansa Ibrahim ya zama uban al’ummai masu yawa. (Farawa 17:5, 6) Ka yi kuma la’akari da matar Ibrahim, Saraya, ƙila yana nufin “Mafaɗaciya.” Hakika ta yi farin ciki da Allah ya sake mata suna “Saratu,” wato, “Gimbiya,” domin za a yi sarakuna a zuriyarta.—Farawa 17:15, 16.
Allah ne kuma ya raɗa wa wasu raya suna da kansa. Alal misali, ya gaya wa Ibrahim da Saratu su raɗa wa ɗansu suna Ishaƙu, wato, “Dariya.” Wannan zai riƙa tuna wa waɗannan ma’aurata masu aminci yadda suka ɗauki labarin cewa za su sami ɗan da tsufansu. Sa’ad da Ishaku ya girma ya zama bawan Allah mai aminci, sunansa babu shakka zai riƙa faranta wa Ibrahim da Saratu sa’ad da wannan ɗa da suke ƙauna yake tare da su.—Farawa 17:17; 18:12, 15; 21:6.
’Yar surkuwar Ishaku Rahila ta raɗa wa ɗan autanta suna domin wani dalili na dabam. Sa’ad da take shure shuren mutuwa, Rahila ta rika ɗanta Ben’oni, wato, “Ɗan makokina.” Mijinta da yake makoki, Yakubu, ya ɗan canja sunan zuwa Banyamin, wato “Ɗan Hannun Dama.” Wannan nuna yana nufin tagomashi da kuma agazawa.—Farawa 35:16-19; 44:20.
A wasu lokaci kuma ana ba da suna ja jitu da yanayin mutum na zahiri. Alal misali, Ishaku da Rifkatu suna haifi ɗa mai jan gashi sai ka ce tufa mai-gashi, suna kira shi Isuwa. Me ya sa? A Ibraniyanci sunan yana nufin “Mai Gashi.” (Farawa 25:25) Kamar yadda yake rubuce a cikin Littafin Ruth, Na’omi tana da ’ya’ya biyu maza. Yana sunansa Mahlon, wato, “mai laulayi,” ɗayan kuma Chilion, wato “raunanne.” Ko an raɗa musu waɗannan suna sa’ad da aka haife su ne ba a faɗa ba, amma suna dace domin yadda waɗannan suka mutum suna samari.—Ruth 1:5.
Wani abin da ake saba yi kuma shi ne canja ko kuma gyara suna. Bayan da ta koma Bai’talami, a talauce bayan ta yi rashin mijinta da kuma ’ya’yanta, Na’omi ta ƙi a kira ta da sunanta da ke nufin “Jin Daɗi.” Maimakon haka, ta nace: “Kada ku ce da ni Na’omi; Mara [“Ɗaci”] za ku ce da ni, gama Mai-iko duka ya yi mini aiki mai-zafi ƙwarai.”—Ruth 1:20, 21.
Wani al’ada kuma shi ne a raɗa wa yaro suna domin girmama wani abu mai muhimmanci. Sunan annabci Haggai, alal misali, yana nufin “An Haife shi Ranar Biki.”a
Sunaye Masu Ma’ana a Zamanin Kiristoci
Sunan Yesu yana da ma’ana mai girma. Kafin a haife shi, Allah ya umurci iyayensa: “za ka kira sunansa Yesu” ma’anar sunan shi ne “Jehobah ne Mai Ceto.” Menene dalilin sunan? “shi ne za ya ceci mutanensa daga zunubansu,” in ji mala’ika da ya yi magana da Yusufu. (Matta 1:21) Bayan an naɗa Yesu da ruhu mai tsarki a lokacin da ya yi baftisma, aka ƙara laƙabi na Ibrananci “almasihu” ga sunan. A Hellenanci, wannan laƙabin ake ce da shi “Kristi.” Dukan waɗannan laƙabin biyu suna nufin “wanda aka naɗa.”—Matta 2:4.
Yesu da kansa ya bai wa wasu almajiransa suna na kwatanci. Alal misali, ya bai wa Siman sunan Semanci Kefas, wanda yake nufin “Dutse.” Aka zo aka fi sanin Siman da “Bitrus” fassarar Kefas a Hellenanci. (Yohanna 1:42) Yesu ya kira ’yan’uwa biyu masu ƙwazo Yaƙub da Yohanna “Buwanarjis,” ma’ana “’yan tsawa.”—Markus 3:16, 17.
Almajiran Yesu suka ci gaba da bai wa wasu sunaye domin wasu dalilai. Wani misali kuma shi ne na almajiri Yusufu, waɗanda manzanni suka kira Barnaba, wato “Ɗan Ƙarfafa Zuciya.” Barnaba ya ci sunansa, ya ƙarfafa zuciyar mutane da yawa a ruhaniya da kuma a zahiri.—Ayukan Manzanni 4:34-37; 9:27; 15:25, 26.
Muhimmancin Sunanka
Ba mu da wani iko bisa suka da aka raɗa mana sa’ada muke jarirai. Amma, mu za mu iya bai kanmu irin sunan da muka yi. (Misalai 20:11) Me ya sa ba za ka tambayi kanka ba: ‘Da a ce Yesu ko kuma manzani sun sami zarafi, wane suna za su ba ka? Wane suna zai dace da irin halina?’
Wannan tambayar tana bukatar a mai da hankali a kanta sosai. Me ya sa? “Suna mai-kyau abin zaɓa ne gaba da wadata mai-yawa,” Sarki Sulemanu ya rubuta.” (Misalai 22:1) Hakika, idan muka yi suna mai kyau, a inda muke hakika muna da arziki. Mafi muhimmanci ma, idan muka kasance da suna mai kyau a gaban Allah, za mu sami dukiya madawwamiya. Ta yaya? Allah ya yi alkawari cewa zai rubuta a cikin “littafin tunawa” sunayen waɗanda.—Malachi 3:16; Ru’ya ta Yohanna 3:5; 20:12-15.
[Hasiya]
a Shaidun Jehobah da yawa a Afirka sunaye da suke da alaƙa da taron gunduma ko kuma na da’ira da aka yi a lokacin da aka haife su.
[Bayanin da ke shafi na 31]
Wane suna zai dace da irin halina?
[Akwati/Hotunan da ke shafi na 30]
Waye Immanuel?
Sunayen wasu mutane cikin Littafi Mai Tsarki annabci ne kuma yana kwatanta irin aikin da mutumin zai yi. Alal misali, an hure annabci Ishaya ya rubuta: “Duba, budurwa za ta yi juna biyu, za ta haifi ɗa, za ta kira sunansa Immanuel.” (Ishaya 7:14) Ma’anar wannan ita ce “Allah yana tare da mu.” Wasu masana sun yi ƙoƙari su nuna cewa cikar farko na wannan annabci ya faru kan wani cikin sarakunan Isra’ila ko kuma ɗan cikin ’ya’yan Ishaya. Duk da haka, marubucin Littafi Mai Tsarki Matta ya nuna cewa annabcin Ishaya ya cika ne bisa Yesu.—Matta 1:22, 23.
Wasu kuma sun ce da yake an kira Yesu Immanuel, Littafi Mai Tsarki yana koyarwa ne cewa Yesu Allah ne. Amma fa, in aka yarda da wannan ra’ayi, saurayin nan Elihu, da ya yi wa Ayuba gyara shi ma Allah ne. Me ya sa? Sunansa yana nufin “Shi ne Allah ne.”
Yesu bai taɓa da’awar shi Allah ne ba. (Yohanna 14:28; Filibbiyawa 2:5, 6) Amma ya nuna irin mutumtakar Ubansa sosai, kuma ya cika dukan alkawuran da Allah ya yi game da Almasihu. (Yohanna 14:9; 2 Korinthiyawa 1:20) Sunan nan Immanuel ya kwatanta matsayin Yesu na Almasihu da kyau, zuriyar Dauda, wanda ya tabbatar da cewa Allah yana tare da waɗanda suka bauta masa.
[Hotunan da ke shafi na 30]
IMMANUEL “Allah Yana Tare da Mu”
[Akwati/Hotunan da ke shafi na 31]
Suna Mafi Muhimmanci
Suna Allah ya bayyana wajen sau 7,000 cikin Littafi Mai Tsarki. Sunan da baƙaƙe huɗu na Ibraniyawa יהוה suke wakilta, yana fassara shi “Jehobah” da Hausa. Menene muhimmancin wannan suna? Sa’ad da Musa ya yi tambaya game da sunan Allah, Jehobah ya amsa: “Zan kasance dukan abin da na ga dama.” (Fitowa 3:14, The Emphasised Bible, na J. B. Rotherham) Saboda haka, sunan Allah tabbaci ne cewa zai kasance dukan abin da ake bukata domin ya cika nufinsa. (Ishaya 55:8-11) Idan Allah ya yi alkawari muna iya kafa rayuwarmu a kansa domin tabbacinsa. Me ya sa? Domin sunansa Jehobah.
[Hotunan da ke shafi na 29]
IBRAMHIM “Uban Jama’a”
[Hotunan da ke shafi na 29]
SARATU “Gimbiya”