Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w15 5/1 pp. 4-7
  • Tsarin Nazari don Kowa

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Tsarin Nazari don Kowa
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2015
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • AMSOSHIN TAMBAYOYIN DA AKE YAWAN YI GAME DA NAZARIN LITTAFI MAI TSARKI DA MUKE YI DA MUTANE
  • Yaya Shaidun Jehobah Suke Nazarin Littafi Mai Tsarki da Mutane?
    Tambayoyin da Ake Yawan Yi
  • A Ina Ne Za Mu Sami Amsoshin Muhimman Tambayoyi?
    A Ina Ne Za Mu Sami Amsoshin Muhimman Tambayoyi?
  • Ka ji dadin abubuwan da ka koya?
    Ka Ji Dadin Rayuwa Har Abada!—Gabatarwar Nazarin Littafi Mai Tsarki
  • Za Ka So Ka Ƙara Sanin Littafi Mai Tsarki?
    Za Ka So Ka Ƙara Sanin Littafi Mai Tsarki?
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2015
w15 5/1 pp. 4-7
Nazarin Littafi Mai Tsarki

ABIN DA KE SHAFIN FARKO | SHIN YA DACE KA YI NAZARIN LITTAFI MAI TSARKI?

Tsarin Nazarin Littafi Mai Tsarki Don Kowa

An san Shaidun Jehobah sosai da yin wa’azi ga jama’a. Amma ka san cewa muna nazari da mutane a duk duniya?

Ana nazarin Littafi Mai Tsarki da wani mutum a wajen aikinsa

A shekara ta 2014, Shaidun Jehobah sama da 8,000,000 a ƙasashe 240 sun yi nazari da mutane kusan 9,500,000 a kowane wata.a Hakika, adadin mutanen da muke nazarin Littafi Mai Tsarki da su ya wuce adadin mutane a ƙasashe ɗaya-ɗaya har wajen guda 140.

Don su sami kayan yin wa’azi, Shaidun Jehobah suna buga Littafi Mai Tsarki da littattafai da mujallu da dai sauran littattafai masu bayyana Littafi Mai Tsarki kusan biliyan ɗaya da rabi a harsuna 700 kowace shekara. Irin waɗannan littattafan da ake bugawa suna ba mutane damar yin nazarin Littafi Mai Tsarki a yaren da suka zaɓa.

“Ban ji daɗin yin nazari ba sa’ad da nake makaranta, amma na ji daɗin wannan sosai. Abubuwan da na koya sun sanyaya zuciyata!”—Katlego, Afirka ta Kudu.

“Nazarin ya amsa tambayoyina da dai sauransu.”—Bertha, Meziko.

“An yi nazarin a gidana kuma a lokacin da ya dace da ni. To, me kuma nake bukata!”—Eziquiel, Brazil.

“Nazarin yakan ɗauki tsawon minti 15 zuwa 30, amma a wasu lokuta yakan wuce hakan idan na ga dama.”—Viniana, Ostareliya.

“Abin mamaki, ba a karɓi ko sisi don nazarin ba!”—Aimé, Ƙasar Bini.

“Matar da ta yi nazari da ni tana da kirki sosai. Dangantakarmu ta yi danƙo.”—Karen, Arewacin Ireland.

“Mutane da yawa suna yin nazarin ba tare da sun zama Shaidun Jehobah ba.”—Denton, Ingila.

AMSOSHIN TAMBAYOYIN DA AKE YAWAN YI GAME DA NAZARIN LITTAFI MAI TSARKI DA MUKE YI DA MUTANE

Yaya ake yin nazarin?

Muna zaɓan batutuwa dabam-dabam daga cikin Littafi Mai Tsarki, sa’an nan mu bincika nassosin da suka shafi batutuwan. Alal misali, Littafi Mai Tsarki ya ba da amsoshin waɗannan tambayoyi: Wane ne Allah? Mene ne kamanninsa da kuma halayensa? Shin yana da suna? A ina yake da zama? Za mu iya ƙulla dangantaka da shi kuwa? Abu mafi wuya shi ne inda za mu ga amsoshin a cikin Littafi Mai Tsarki.

Don mu taimaki mutane su sami waɗannan amsoshin, muna yin amfani da littafin nan mai shafuffuka 224, wato Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?b An buga wannan littafin ne don a taimaki mutane su fahimci koyarwar Littafi Mai Tsarki. Littafin yana ɗauke da darussa game da Allah da Yesu Kristi da wahalar da mutane suke sha da tashin matattu da addu’a da dai sauransu.

A wane lokaci ne ake yin nazarin kuma a ina?

Za a yi nazarin a lokacin da ya dace da kai da kuma a inda kake so.

Nazarin zai ɗauki tsawon minti nawa?

Mutane da yawa suna keɓe awa ɗaya ko sama da hakan kowane mako don su yi nazarin Littafi Mai Tsarki. Amma ba lallai sai an kai awa ɗaya ba. Wasu suna yin nazarin na mintoci 10 ko 15 a kowane mako.

Nawa ake biya don nazarin?

Ba a biyan ko sisi. Hakan ya yi daidai da abin da Yesu ya ce wa almajiransa: “Kyauta kuka karɓa, sai ku bayar kyauta.”—Matta 10:8.

Nazarin zai ɗauki tsawon wata nawa?

Kai ne za ka zaɓi tsawon lokacin da kake so ka yi nazarin. Littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa? yana ɗauke da darussa 19. Za ka iya kammala kowane darasi a tsawon lokacin da ya dace da kai.

Wajibi ne in zama Mashaidin Jehobah bayan nazarin?

A’a. Mun fahimci cewa kowane mutum yana da ’yanci ya zaɓi addinin da yake so. Amma mutumin da ya fahimci abin da Littafi Mai Tsarki yake koyarwa zai iya yin zaɓi mai kyau.

A ina ne zan sami ƙarin bayani?

Dandalinmu na jw.org/ha yana ɗauke da bayani a kan abubuwan da Shaidun Jehobah suka yi imani da su da kuma ayyukansu.

Ta yaya zan ce a yi nazari da ni?

Mutane suna aika sako ta hanyoyi dabam-dabam cewa a yi nazari da su: ta intane, ta wasika, da dai sauransu
  • Ka cika fom a dandalin www.pr418.com/ha.

  • Ka rubuta wasiƙa zuwa ga adireshin da ke shafi na biyu na wannan mujallar.

  • Za ka iya tambayar Shaidun Jehobah da ke yankinku.

a A yawancin lokaci, ana yin nazari da mutane ɗai-ɗai ko kuma mutane da yawa.

b Shaidun Jehobah ne suka wallafa. An buga littafin nan fiye da kofi miliyan 230 a harsuna sama da 260.

WANI ABU DA KE TAIMAKA WA IYALAI

Eziquiel

“Sa’ad da matata ta soma nazarin Littafi Mai Tsarki, na lura cewa halayenta sun gyaru. Rayuwar iyalinmu ta daɗa kyau. Sai ni ma na soma nazarin Littafi Mai Tsarki don in san abin da matata take koya. Abin da na koya ya taimake ni sosai in zama mutumin kirki. Yin nazarin Littafi Mai Tsarki ya sa dangantakarmu ta yi danƙo.”—Eziquiel.

Karen

“Nazarin Littafi Mai Tsarki da nake yi ya sa na daina yin maye da giya, da shan miyagun ƙwayoyi da kuma zafin rai. A yanzu haka, gidana yana da kyau da kuma tsabta fiye da dā. Ina son iyalina sosai yanzu kuma ina yin abin da zai sa su farin ciki. Ina matuƙar farin ciki.”—Karen.

Viniana

“Wasu mutane sun yi mini ba’a don ina nazarin Littafi Mai Tsarki. Amma maigidana ya goyi bayana kuma ya ce: ‘Ba ruwana da abin da mutane suke cewa. Ina dai farin cikin ganin yadda kike canja halayenki. Kada ki yi sanyin gwiwa.’ Yanzu, ina jin daɗin rayuwar iyalinmu sosai!”—Viniana.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba