Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • wp17 Na 1 pp. 5-6
  • Me Zai Sa Ka Ji Dadin Karatun?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Me Zai Sa Ka Ji Dadin Karatun?
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Wa’azi)—2017
  • Makamantan Littattafai
  • Shawara A Kan Yin Nazari
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2023
  • Yadda Za Ka Amfana Daga Karanta Littafi Mai Tsarki
    Ka Ji Dadin Rayuwa Har Abada!​—Don Nazarin Littafi Mai Tsarki
  • Littafin da Za A Iya Fahimta
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Wa’azi)—2016
  • Hanyoyi Bakwai da Za a Amfana Daga Karatun Littafi Mai Tsarki
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Wa’azi)—2017
wp17 Na 1 pp. 5-6
Wata mata tana amfani da kayan bincike yayin da take karatun Littafi Mai Tsarki

ABIN DA KE SHAFIN FARKO | YADDA ZA KA JI DAƊIN KARANTA LITTAFI MAI TSARKI

Me Zai Sa Ka Ji Daɗin Karatun?

Shin kana jin daɗin karanta Littafi Mai Tsarki ne ko a’a? Da akwai abubuwa da yawa da za ka iya yi da za su sa ka ji daɗin karatun. Bari mu yi la’akari da waɗannan abubuwan.

Ka yi amfani da fassara mai sauƙin fahimta. Ba za ka ji daɗin karatun Littafi Mai Tsarki ba idan ka yi amfani da fassarar da aka yi amfani da kalmomin dā ko kuma mai wuyan fahimta. Don haka, ka nemi juyin Littafi Mai Tsarki mai sauƙin fahimta da kuma wanda zai ratsa zuciyarka. Ƙari ga haka, ka nemi Littafi Mai Tsarki da aka fassara da kyau sosai.a

Ka yi amfani da fasaha na zamani. A yau, za a iya samu Littafi Mai Tsarki a intane. Za ka iya karanta Littafi Mai Tsarki a intane ko kuma ka saukar da shi a kwamfutarka ko kuma wayarka. Akwai wasu fasaha da za su iya sa ka duba wasu ayoyin Littafi Mai Tsarki da suka yi magana a kan batun da kake bincike a kai ko kuma ka gwada da wasu fassara dabam. Idan kuma kana so ka saurari karatun ne kawai, da akwai sautin Littafi Mai Tsarki. Mutane da yawa suna jin daɗin karatun Littafi Mai Tsarki sa’ad da suke tafiya a cikin mota ko suke wanki ko kuma suke wani aikin da zai iya barin su su saurari karatun. Ka yi amfani da wanda ka fi so.

Ka yi amfani da abubuwan da za su inganta nazarin. Yin amfani da abubuwan da za su inganta nazari za su iya taimaka maka ka ji daɗin karatun. Da akwai taswirar ƙasashen da aka ambata a cikin Littafi Mai Tsarki. Wannan zai taimaka maka ka nemi wuraren da aka ambata a karatun da kake yi kuma ka gan kamar abubuwan suna faruwa ne a gabanka. Talifofin da ke cikin wannan mujallar ko kuma a sashen “Koyarwar Littafi Mai Tsarki” a dandalinmu na jw.org/⁠ha, za su taimaka maka ka san ma’anar wasu abubuwa a cikin Littafi Mai Tsarki.

Ka riƙa canja yadda kake karatun. Idan ba ka jin daɗin karanta Littafi Mai Tsarki daga farko zuwa ƙarshe, za ka iya somawa da littafin da ka fi so. Idan kana so ka san game da mutanen da aka ambata a cikin Littafi Mai Tsarki, kana iya karanta surorin da suka yi magana game da su. An nuna hanyoyin da za ka iya bi da karatun Littafi Mai Tsarki a cikin akwatin nan “Ka San Mutanen da Aka Ambata a Cikin Littafi Mai Tsarki.” Kana kuma iya karanta Littafi Mai Tsarki bisa ga batutuwa ko kuma yadda abubuwa suka faru. Ka gwada yin amfani da waɗannan hanyoyin.

a Mutane da yawa sun ga cewa fassarar New World Translation of the Holy Scriptures daidai ne, kuma yana da sauƙi karantawa da kuma fahimta. Shaidun Jehobah ne suka buga wannan Littafi Mai Tsarki kuma ana samun sa a harsuna fiya da 130. Za ka iya saukar da na Turanci a dandalinmu na jw.org ko kuma ka saukar da manhajar JW Library. Idan kuma kana so, Shaidun Jehobah za su kawo maka shi har gidanka.

KA SAN MUTANEN DA AKA AMBATA A CIKIN LITTAFI MAI TSARKI

Wasu mata masu aminci

Abigail

1 Sama’ila sura 25

Esther

Esther surori 2-5, 7-9

Hannatu

1 Sama’ila surori 1-2

Maryamu

(Mahaifiyar Yesu) Matta surori 1-2; Luka surori 1-2; ka kuma duba Yohanna 2:​1-12; Ayyukan Manzanni 1:​12-14; 2:​1-4

Rahab

Joshua sura 2 da 6; ka kuma duba Ibraniyawa 11:​30, 31; Yaƙub 2:​24-26

Rifkatu

Farawa surori 24-27

Saratu

Farawa surori 17-18, 20-21, 23; ka kuma duba Ibraniyawa 11:11; 1 Bitrus 3:​1-6

Wasu maza masu bangaskiya

Ibrahim

Farawa surori 11-24; ka kuma duba 25:​1-11

Dauda

1 Sama’ila surori 16-30; 2 Sama’ila surori 1-24; 1 Sarakuna surori 1-2

Yesu

Linjilar Matta da Markus da Luka da kuma Yohanna

Musa

Fitowa surori 2-20, 24, 32-34; Littafin Lissafi surori 11-17, 20, 21, 27, 31; Kubawar Shari’a sura 34

Nuhu

Farawa surori 5-9

Bulus

Ayyukan Manzanni surori 7-9, 13-28

Bitrus

Matta surori 4, 10, 14, 16-17, 26; Ayyukan Manzanni surori 1-5, 8-12

ABUBUWAN DA KE INGANTA NAZARI DA SHAIDU SUKA WALLAFA

  • JW.ORG​—Wannan dandalin yana ɗauke da abubuwa da yawa da za su inganta nazari kamar sashen nan “An Amsa Tambayoyin Littafi Mai Tsarki.” Ƙari ga haka, yana ɗauke da bayanai game da yadda za a iya saukar da manhajar JW Library

  • Taimako don Nazarin Kalmar Allah​—Wannan ƙaramar ƙasidar tana ɗauke da taswirori da wasu bayanai game da tarihin Isra’ilawa da kuma zamanin Yesu

  • Littafi Mai Tsarki​—Wane Saƙo Ne Ke Cikinsa?​—Wannan ƙasida mai shafi 32 ta yi gajeriyar bayani a kan jigon Littafi Mai Tsarki

  • “See the Good Land”​—Wannan ƙasidar tana ɗauke da taswira da kuma hotunan wuraren da aka ambata a cikin Littafi Mai Tsarki

  • Insight on the Scriptures​—Littafi na ɗaya da na biyu suna ɗauke da bayanan da aka yi game da mutane da wurare da kuma wasu kalmomin da ke cikin Littafi Mai Tsarki

  • “All Scripture Is Inspired of God and Beneficial”​—Wannan littafin ya bayyana lokaci da wuri da kuma dalilin da ya sa aka rubuta kowane littafi da ke cikin Littafi Mai Tsarki kuma ya yi ɗan ­bayani a kan kowane littafi

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba