MASU KARATU SUN YI TAMBAYA . . .
Ya Kamata Kiristoci Su Yi Bikin Kirsimati Ne?
Miliyoyin mutane a faɗin duniya sun yi imani cewa Kirsimati bikin tuna da ranar haihuwar Yesu Kristi ne. Amma ka taɓa yin tunani ko Kiristocin ƙarni na farko sun taɓa yin bikin Kirsimati? Ka san abin da Littafi Mai Tsarki ya faɗa game da bikin ranar haihuwa? Neman amsoshin waɗannan tambayoyin zai taimaka mana mu san ko ya dace Kiristoci su yi bikin Kirsimati.
Babu wani wuri a cikin Littafi Mai Tsarki da ya nuna cewa Yesu ko kuma sauran amintattun bayin Allah sun yi bikin ranar haihuwarsu. Mutane biyu ne kawai suka yi bikin ranar haihuwarsu a cikin Littafi Mai Tsarki. Dukansu biyun ba sa bauta wa Jehobah, Allah na Littafi Mai Tsarki kuma sun aikata mugunta a ranar bikin haihuwarsu. (Farawa 40:20; Markus 6:21) Littafin Encyclopædia Britannica ya nuna cewa, Kiristocin ƙarni na farko ba su amince da bikin ranar haihuwa ba domin “arna ne suka fara yin sa.”
A yaushe ne aka haifi Yesu?
Littafi Mai Tsarki bai faɗi ainihin ranar da aka haifi Yesu ba. Littafin nan McClintock and Strong’s Cyclopedia ya ce: “Ba za a iya ganin ainihin ranar haihuwar Yesu a Sabon Alkawari ko kuma a wani waje ba.” A gaskiya, da a ce Yesu yana son mabiyansa su riƙa yin bikin ranar haihuwarsa, da ya gaya musu su yi hakan kuma da sun san ainihin ranar haihuwarsa.
Na biyu, Littafi Mai Tsarki bai nuna cewa Yesu ko kuma ɗaya daga cikin mabiyansa sun yi bikin Kirsimati ba. Littafin New Catholic Encyclopedia ya ce: “A wani kalandar Romawa mai jigo, Chronograph of Philocalus, wanda aka rubuta tun shekara ta 336 bayan haihuwar Yesu” ne a aka fara ambata bikin Kirsimati. Hakan ya nuna cewa an riga an kammala rubuta Littafi Mai Tsarki a lokacin kuma Yesu ya yi shekaru da yawa da barin duniya. Shi ya sa littafin McClintock and Strong ya ce “ba Allah ne ya kafa bikin Kirsimati ba kuma bikin ba ya cikin Sabon Alkawari.”a
Wane biki ne Yesu ya ce wa mabiyansa su riƙa yi?
A matsayinsa na Babban Malami, Yesu ya gaya wa mabiyansa dalla-dalla abin da yake so su yi kuma an rubuta shi a cikin Littafi Mai Tsarki. Amma bikin Kirsimati ba ya cikin abin da Yesu ya gaya wa mabiyansa. Kamar yadda malamin makaranta ba zai so ɗalibansa su yi abin da bai gaya musu ba, Yesu ma ba zai so mabiyansa su “zarce abin da an rubuta” a cikin Littafi Mai Tsarki ba.—1 Korintiyawa 4:6.
A maimakon haka, akwai wani abu mai muhimmanci da Kiristocin ƙarni na farko suka san da shi sosai. Wannan shi ne taron Tunawa da Mutuwar Yesu. Yesu ya gaya wa mabiyansa lokacin da za su yi taron da kuma yadda za su yi shi. An rubuta wannan umurnin da kuma ainihin ranar mutuwar Yesu a cikin Littafi Mai Tsarki.—Luka 22:19; 1 Korintiyawa 11:25.
Kamar yadda muka gani, Kirsimati bikin ranar haihuwa ne kuma Kiristocin ƙarni na farko ba su yi wannan bikin ba. Ƙari ga haka, Littafin Mai Tsarki bai ce Yesu ko wani mabiyinsa ya yi bikin Kirsimati ba. Wannan gaskiyar ta sa miliyoyin Kiristoci a faɗin duniya ba sa yin bikin Kirsimati.
a Don ƙarin bayani game da tarihin Kirsimati, ka duba talifin nan “Our Readers Ask . . . What Are the Facts About Christmas?” a Hasumiyar Tsaro ta 1 ga Disamba 2014, za ka iya samun ta a www.pr418.com.