Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w18 Nuwamba p. 32
  • Wace Kyauta Ce Za Mu Ba Jehobah?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Wace Kyauta Ce Za Mu Ba Jehobah?
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2018
  • Makamantan Littattafai
  • “Ba da Kyauta ga Jehobah”
    Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2018
  • Darajar Anini Biyu
    Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2020
  • A Ina Shaidun Jehobah Suke Samun Kudin Yin Ayyukansu?
    Tambayoyin da Ake Yawan Yi
  • Muna Gode wa Jehobah don Ƙaunarku
    Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2021
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2018
w18 Nuwamba p. 32
donate.jw.org

Wace Kyauta Ce Za Mu Ba Jehobah?

YESU ya taɓa cewa: “Ya fi albarka a bayar da a karɓa.” (A. M. 20:35) Abin da Yesu ya faɗa yana da alaƙa da dangantakarmu da Jehobah. Me ya sa? Domin Jehobah ya ba mu abubuwa da yawa da suke sa mu farin ciki sosai, amma za mu fi farin ciki idan muna ba Jehobah kyauta. Wace kyauta ce za mu ba Jehobah? Littafin Karin Magana 3:9 ya ce: Mu ‘girmama Yahweh da abin da muke da shi.’ Abubuwan da muke da su sun ƙunshi lokacinmu da baiwarmu da ƙarfinmu da kuma wadatarmu. Idan muna yin amfani da waɗannan abubuwan don mu tallafa wa bauta ta gaskiya, muna ba Jehobah kyauta ne kuma yin hakan yana sa mu farin ciki.

Mene ne zai taimaka mana mu ɗauki ba Jehobah kyauta da muhimmanci? Manzo Bulus ya gaya wa Kiristocin da ke Korinti cewa su riƙa ‘ajiye’ abin da za su ba Allah kyauta. (1 Kor. 16:2) Mene ne za ka yi idan kana son ƙarin bayani game da yadda ake ba da gudummawa a wurin da kuke? Don Allah ka duba akwatin da ke ƙasa.

Ba a iya ba da gudummawa ta Intane a wasu ƙasashe. Amma, akwai wasu hanyoyin ba da gudummawa da aka rubuta a shafin ba da gudummawa. A wasu ƙasashe, ana saka amsoshi ga tambayoyin da ake yawan yi game da batun ba da gudummawa a shafin.

Hanya Mai Sauƙi da Za Mu Iya Ba da Gudummawa ta Intane

YANA DA SAUƘIN SAMU

  • Shafin Intane

    Ka shigar da adireshin nan donate.jw.org a shafin intane

  • Manhajar JW Library

    A manhajar JW Library®, ka danna sashen da aka rubuta “Donations”

YANA DA SAUƘIN AMFANI

Ka ba da gudummawa sau ɗaya ko ka ce a riƙa tura gudummawa a kai a kai don:

  • Aiki na Dukan Duniya

  • Ikilisiyarku

  • Taron Yanki

  • Taron Da’ira

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba