Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w20 Mayu pp. 8-11
  • Sarakuna da Ke Gāba da Juna a Kwanaki na Karshe

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Sarakuna da Ke Gāba da Juna a Kwanaki na Karshe
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2020
  • Makamantan Littattafai
  • “Sarkin Arewa” a Kwanaki na Karshe
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2020
  • Jehobah Ya Bayyana Al’amura Da Lallai “Za Su Faru Ba Da Daɗewa Ba”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
  • Wane ne “Sarkin Arewa” a Yau?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2020
  • Abin da Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna Ta Ce Zai Faru da Maƙiyan Allah
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2022
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2020
w20 Mayu pp. 8-11

Sarakuna da Ke Gāba da Juna a Kwanaki na Ƙarshe

Wasu cikin annabci da aka ambata a taswirar nan sun faru a lokaci ɗaya. Dukansu sun nuna cewa muna rayuwa a “kwanakin ƙarshe.”​—Dan. 12:4.

Taswirar da ke nuna annabce-annabce da kuma sarkin arewa da sarkin kudu daga shekara ta 1870 zuwa zamaninmu.
  • Taswira na 1 cikin 4, da ke nuna annabce-annabce da suka cika a lokaci daya a kwanaki na karshe daga misalin shekara ta 1870 zuwa 1918. Daga shekara ta 1914 zuwa yanzu ne kwanaki na karshe. Annabci na 1: Dabba mai kawuna bakwai da ta bayyana kafin kwanakin wata da aka ambata a taswirar. An ji wa kai na bakwai rauni a lokacin Yakin Duniya na Daya. Daga shekara ta 1917 kai na bakwai ya warke, kuma dabbar ta sake samun karfi. Annabci na 2: An san sarkin arewa da sarkin kudu a shekara ta 1870. Sarkin arewa ya sake kunno kai a 1871 a matsayin Jamus. Da farko Birtaniya ce sarkin kudu, amma a shekara ta 1917 Birtaniya da Amirka ne suka sauye Birtaniya. Annabci na 3: Daga shekara ta 1870, Russell da abokan aikinsa ne masu idar da sako. Daga shekara ta 1881, an karfafa masu karanta mujallar Zion’s Watch Tower cewa su rika yin wa’azi. Annabci na 4: Daga shekara ta 1914, lokacin girbi. An ware ciyayi daga alkama. Annabci na 5: Daga shekara ta 1917 mun san kafafun bakin karfe hade da laka. Taswirar ta kuma nuna abubuwan da za su faru a duniya daga shekara ta 1914 zuwa 1918 a Yakin Duniya na Daya. Abubuwan da za su shafi bayin Jehobah: Daga shekara ta 1914 zuwa 1918 an saka Daliban Littafi Mai Tsarki a kurkuku a Britaniya da Jamus. A shekara ta 1918 an saka ’yan’uwan da ke ja-goranci a hedkwatarmu da ke Amirka a kurkuku.
    Annabci na 1.

    Nassosi R. Yar. 11:7; 12:​13, 17; 13:​1-8, 12

    Annabci “Dabbar” ta yi dubban shekaru tana mulki a kan mutane. A kwanaki na ƙarshe, an ji wa kai na bakwai na dabbar rauni. Daga baya, kan ya warke kuma “dukan duniya” ta soma bin dabbar. Shaiɗan ya yi amfani da ita don ya yaƙi “sauran zuriyar macen.”

    Yadda ya cika Bayan ambaliyar ruwa na zamanin Nuhu, gwamnatocin da ke gāba da Jehobah sun soma mulki. Bayan ƙarnuka da yawa, wato a lokacin Yaƙin Duniya na 1, ikon Birtaniya ya ragu sosai. Ta sake samun ƙarfi sa’ad da ta haɗa kai da Amirka. A kwanaki na ƙarshe, Shaiɗan yana amfani da dukan gwamnatoci don ya tsananta wa bayin Allah.

  • Annabci na 2.

    Nassosi Dan. 11:​25-45

    Annabci A kwanaki na ƙarshe, sarkin arewa da sarkin kudu za su yi jayayya da juna.

    Yadda ya cika Jamus ta yaƙi Amirka da Birtaniya. A shekara ta 1945, Tarayyar Soviet da magoya bayanta sun zama sarkin arewa. A 1991, Tarayyar Soviet ta wargaje, kuma daga baya, Rasha da magoya bayanta sun zama sarkin arewa.

  • Annabci na 3.

    Nassosi Isha. 61:1; Mal. 3:1; Luk. 4:18

    Annabci Jehobah ya tura mai idar da ‘saƙonsa’ don ya ‘shirya hanya’ kafin a kafa Mulkin Almasihu. Wannan mai idar da saƙon ya soma “shelar labari mai daɗi ga talakawa.”

    Yadda ya cika Daga shekara ta 1870, Ɗan’uwa C. T. Russell da abokansa sun yi aiki tuƙuru don su koya wa mutane gaskiya. A shekara ta 1881, sun soma nanata cewa bayin Allah suna bukatar yin wa’azi. Sun wallafa talifofin nan “Wanted 1,000 Preachers” (Ana Bukatar Masu Shela 1,000) da kuma “Anointed to Preach” (An Naɗa Masu Wa’azi.)

  • Annabci na 4.

    Nassosi Mat. 13:​24-30, 36-43

    Annabci Wani magabci ya shuka ciyawa a cikin gonar alkama kuma aka bar ta ta girma ta sha kan alkamar har lokacin girbi. A lokacin, za a ware ciyayin daga alkamar.

    Yadda ya cika Daga shekara ta 1870, ana iya ganin bambancin da ke tsakanin Kiristoci na ƙarya da Kiristoci na gaskiya. A kwanaki na ƙarshe, an tattare Kiristoci na gaskiya a cikin ikilisiyoyi kuma aka ware su daga Kiristoci na ƙarya.

  • Annabci na 5.

    Nassosi Dan. 2:​31-33, 41-43

    Annabci Wani gunki da aka ƙera da ƙarafuna dabam-dabam yana da ƙafafun baƙin ƙarfe gauraye da laka.

    Yadda ya cika Lakar tana wakiltar mutanen da Birtaniya da Amirka suke mulki a kansu da suka yi tawaye. Waɗannan mutanen suna hana waɗannan gwamnatoci yin amfani da ikonsu sosai..

  • Taswira na 2 cikin 4 tana nuna annabce-annabce da suka cika a kwanaki na karshe daga misalin shekara ta 1919 zuwa 1945. Jamus ne sarkin arewa har shekara ta 1945. Birtaniya da Amirka ne sarkin kudu. Annabci na 6: A shekara ta 1919, an tattara Kiristoci shafaffu cikin ikilisiyar da aka tsarkake. Daga shekara ta 1919, mun kara kwazo a wa’azi. Annabci na 7: A shekara ta 1920, an kafa tsohuwar Majalisar Dinkin Duniya kuma ta ci gaba har somawar Yakin Duniya na Biyu. Taswirar ta kuma nuna: Annabci na 1, dabba mai kai bakwai ta ci gaba. Annabci na 5, kafafun karfe hade da lada ya ci gaba. Abubuwan da suka faru a duniya daga 1939 zuwa 1945 a Yakin Duniya na Daya. Abubuwan da suka shafi Shaidun Jehobah: A Jamus an saka Shaidun Jehobah fiye da 11,000 a kurkuku daga shekara ta 1939 zuwa 1945. A Birtaniya an saka Shaidun Jehobah kusan 1,600 a kurkuku daga shekara ta 1939 zuwa 1945. An kai wa Shaidun Jehobah fiye da 2,500 hari a Amirka daga shekara ta 1940 zuwa 1944.
    Annabci na 6.

    Nassosi Mat. 13:30; 24:​14, 45; 28:​19, 20

    Annabci An tattara alkamar cikin ‘rumbu’ kuma an naɗa “bawan nan mai aminci, mai hikima” don ya kula da bayin maigidansa. An soma wa’azin “mulkin” ga “dukan al’umma.”

    Yadda ya cika A shekara ta 1919, an naɗa bawan nan mai aminci ya riƙa kula da mutanen Allah. Daga wannan lokacin ne Ɗaliban Littafi Mai Tsarki suka soma wa’azi sosai. A yau, Shaidun Jehobah suna wa’azi a ƙasashe fiye da 200 kuma suna wallafa littattafai a yaruka fiye da 1,000.

  • Annabci na 7.

    Nassosi Dan. 12:11; R. Yar. 13:​11, 14, 15

    Annabci Dabba mai ƙahoni biyu ta ce mutane su gina “siffa domin a girmama wannan dabbar” kuma “ta ba da numfashin rai ga wannan siffar.”

    Yadda ya cika Birtaniya da Amirka sun yi ja-goranci wajen kafa Tsohuwar Majalisar Ɗinkin Duniya. Wasu al’ummai suna goyon bayan wannan ƙungiyar. Daga baya, sarkin arewa ya goyi bayan wannan Majalisar daga shekara ta 1926 zuwa 1933. Kamar Tsohuwar Majalisar Ɗinkin Duniya, mutane suna ganin cewa Majalisar Ɗinkin Duniya za ta sa a yi zaman lafiya. Amma Mulkin Allah ne kaɗai zai yi hakan.

  • Taswira na 3 cikin 4, na dauke da annabce-annabce da suka cika a lokaci daya a kwanaki na karshe daga shekara ta 1945 zuwa 1991. Tarayyar Soviet ne sarkin arewa har zuwa shekara ta 1991, bayan haka, Rasha da magoya bayanta ta zama sarkin arewa. Mulkin Birtaniya da Amirka ne suka zama sarkin kudu. Annabci na 8: Wutar bam din da ya tashi, yana wakiltar yadda irin hallaka da Birtaniya da Amirka suka jawo. Annabci na 9: An kafa Majalisar Dinkin Duniya a shekara ta 1945, kuma ta sauye Tsohuwar Majalisar Dinkin Duniya. Taswirar ta kuma nuna: Annabci na 1, dabba mai kai bakwai ya ci gaba. Annabci na 5, kafafun karfe hade da laka ya ci gaba. Annabci 6, a shekara ta 1945 akwai masu shela fiye da 156,000. A shekara ta 1991, akwai masu shela fiye da 4,278,000. Abubuwan da suka faru da suka shafi bayin Jehobah: Daga shekara ta 1945 zuwa 1951, Tarayyar Soviet ta kai dubban Shaidun Jehobah kurkuku a Siberiya.
    Annabci na 8.

    Nassosi Dan. 8:​23, 24

    Annabci Mugun sarki mai taurin fuska “zai kawo halakarwa mai ban tsoro.”

    Yadda ya cika Birtaniya da Amirka sun kashe mutane da yawa kuma sun yi ɓarna sosai. Alal misali, lokacin Yaƙin Duniya na 2, Amirka ta hallaka mutane da yawa sa’ad da ta jefa wa maƙiyinta bam-bamai guda biyu.

  • Annabci na 9.

    Nassosi Dan. 11:31; R. Yar. 17:​3, 7-11

    Annabci “Wata jar dabba” mai ƙahoni goma ta fito daga rami marar matuƙa kuma ita ce sarki na takwas. Littafin Daniyel ya kira wannan sarkin “abin ƙazanta mai kawo halakarwa.”

    Yadda ya cika Tsohuwar Majalisar Ɗinkin Duniya ta wargaje a lokacin Yaƙin Duniya na 2. Bayan yaƙin, an kafa Majalisar Ɗinkin Duniya. Kamar Tsohuwar Majalisar Ɗinkin Duniya, mutane suna ganin cewa Majalisar Ɗinkin Duniya za ta sa a sami zaman lafiya a duniya. Amma Majalisar Ɗinkin Duniya za ta kai wa addinai hari.

  • Taswira na 4 cikin 4, annabce-annabce da suka cika a lokaci daya a kwanaki na karshe da kuma zamani har zuwa Armageddon. An gano cewa Rasha da magoya bayanta ne sarkin arewa. An gano cewa Birtaniya da Amirka ne sarkin kudu. Annabci na 10: Shugabanan duniya sun yi shelar “zaman lafiya da salama.” Bayan haka, za a soma kunci mai girma. Annabci na 11: Al’ummai sun kai wa kungiyoyin addinai farmaki. Annabci na 12: Gwamnatocin duniya sun kai wa bayin Allah farmaki. An kai shafaffu da suka rage a duniya zuwa sama. Annabci na 13: Armageddon. Wanda yake hawan farin doki ya ci nasara. An hallaka dabba mai kawuna bakwai; an hallaka kafafun bakin karfe hade da laka na babbar gunkin. An kuma nuna: Annabci na 1, dabba mai kawuna bakwai, ya ci gaba har Armageddon. Annabci na 5, kafafun bakin karfe hade da laka, ya ci gaba har Armageddon. Annabci na 6, a yau da akwai masu shela fiye da 8,580,000. Abubuwan da suka shafi mutanen Jehobah: A shekara ta 2017, hukumar Rasha ta saka Shaidu a kurkuku kuma ta kwace ofisoshinsu.
    Annabci na 10 da 11.

    Nassosi 1 Tas. 5:3; R. Yar. 17:16

    Annabci Al’ummai sun yi shelar “zaman lafiya da salama,” kuma “ƙahoni goma” da “dabbar” sun kai wa ‘karuwar’ hari kuma sun hallaka ta. Bayan haka, za a hallaka al’umman.

    Yadda ya cika Al’ummai za su yi da’awar cewa sun kawo zaman lafiya da salama a duniya. Sa’an nan al’umman da ke goyon bayan Majalisar Ɗinkin Duniya za su hallaka ƙungiyoyin addinan ƙarya. Wannan zai zama somawar ƙunci mai girma. Za a daina ƙunci mai girma sa’ad da Yesu ya hallaka mugun zamanin Shaiɗan a yaƙin Armageddon.

  • Annabci na 12.

    Nassosi Ezek. 38:​11, 14-17; Mat. 24:31

    Annabci Gog zai kai wa mutanen Allah hari. Mala’iku za su tattara “waɗanda aka zaɓa.”

    Yadda ya cika Sarkin arewa da sauran sarakunan duniya za su kai wa mutanen Allah hari. Bayan sun soma kai wannan harin, za a tattara sauran shafaffu da suka rage zuwa sama.

  • Annabci na 13.

    Nassosi Ezek. 38:​18-23; Dan. 2:​34, 35, 44, 45; R. Yar. 6:2; 16:​14, 16; 17:14; 19:20

    Annabci Mahayin “farin doki” ya kammala “cin nasara” ta wajen hallaka Gog da sojojinsa. An jefa “dabbar” cikin “tafkin wuta mai ƙuna” kuma aka hallaka gunkin.

    Yadda ya cika Yesu wanda shi ne sarkin Mulkin Allah zai ceci bayin Allah. Yesu da mutane 144,000 da kuma mala’iku za su hallaka al’umman da suka kai wa mutanen Allah hari. Kuma hakan zai kawo ƙarshen mulkin Shaiɗan.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba