Yaya Za Mu Yi Tsammanin Allah Ya Sa Hannu a Harkokin ’Yan Adam?
A ƘARNI na takwas K.Z., aka gaya wa Sarkin Yahuda, Hezekiya, ɗan shekara 39 cewa ciwonsa na ajali ne. Domin ya yi baƙin ciki da jin labarin, Hezekiya ya roƙi Allah a cikin addu’a ya warkar da shi. Allah ya amsa ta wurin annabinsa: “Na ji addu’arka, na ga hawayenka kuma: ga shi, zan ƙara maka kwanakinka har shekara goma sha biyar.”—Ishaya 38:1-5.
Me ya sa Allah ya sa hannu a wannan lokaci? Da farko cikin ƙarnuka, Allah ya yi wa Sarki Dauda adali, alkawari: “Gidanka fa da mulkinka za su tabbata har abada a gabanka: kursiyinka za ya tsaya har abada.” Allah kuma ya bayyana cewa za a haifi Almasihu a zuriyar Dauda. (2 Samu’ila 7:16; Zabura 89:20, 26-29; Ishaya 11:1) Lokacin da Hezekiya ya yi ciwo, bai haifi ɗa ba tukuna. Saboda haka, zuriyar sarauta ta wurin Dauda za ta yanke. Yadda Allah ya sa hannu a yanayin Hezekiya ya yi daidai da ainihin manufar adana zuriyar da Almasihu zai fito daga ciki.
Domin ya cika alkawuransa, Jehovah ya motsa ya sa hannu wa mutanensa a lokatai da yawa kafin zamanin Kiristoci. Musa ya sanar haka game da ceton Isra’ila daga bauta a Masar: “Domin Ubangiji yana ƙaunarku yana kuwa da nufin ya tsayadda rantsuwa wadda ya rantse ma ubanninku, domin wannan Ubangiji ya fishe ku da hannu mai-ƙarfi.”—Kubawar Shari’a 7:8.
A ƙarni na farko ma, sa hannu da Allah ya yi domin ƙudurinsa ne ya ci gaba. Alal misali, a kan hanyarsa zuwa Dimashƙa, Bayahudi mai suna Saul ya sami wahayi na mu’ujiza domin ya hana shi daga tsananta wa almajiran Kristi. Tuban wannan mutumin, da ya zama manzo Bulus yana da muhimmanci a yaɗa bishara a tsakanin al’ummai.—Ayukan Manzanni 9:1-16; Romawa 11:13.
Sa Hannu Ya Zama Abin da Aka Saba Yi Ne?
Sa hannu na Allah abin da aka saba yi ne ko kuma idan ya zama wajibi ne? Nassosi ya nuna cewa ba abin da aka saba yi ba ne. Ko da yake Allah ya sa hannu ya ceci matasa uku Ibraniyawa daga mutuwa cikin tanderu, annabi Daniel daga ramin zakuna, bai yi haka nan don ya kāre wasu annabawa daga mutuwa ba. (2 Labarbaru 24:20, 21; Daniel 3:21-27; 6:16-22; Ibraniyawa 11:37) An ceci Bitrus a hanya ta mu’ujiza daga kurkuku inda Hirudus Agaribas na I ya tsare shi. Amma wannan sarkin ne ya kashe manzo Yaƙub kuma Allah bai sa hannu ya hana laifin nan ba. (Ayukan Manzanni 12:1-11) Ko da yake Allah ya ba wa manzannin ikon su warkar da cuta har kuma su ta da matattu, bai yarda ya cire “ƙaya cikin jiki” da ke jikin manzo Bulus da yake masa azaba ba.—2 Korinthiyawa 12:7-9; Ayukan Manzanni 9:32-41; 1 Korinthiyawa 12:28.
Allah bai sa hannu ya hana tsanantawa da Daular Roma Nero ya yi wa almajiran Kristi ba. An gana wa Kiristoci azaba, a raye aka ƙone su a wuta, kuma an jefa su ga dabbobi masu kisa. Amma Kiristoci na farko ba su yi mamakin wannan hamayya ba, kuma bai raunana imaninsu cewa akwai Allah ba. Balle ma, Yesu ya gargaɗe almajiransa cewa za a kai su kotu, domin haka sun kasance a shirye don wahala har ma su mutu domin imaninsu.—Matta 10:17-22.
Yadda ya yi dā, a yau babu shakka Allah zai iya ceton bayinsa daga yanayi na haɗari, kuma kada a yi soki wa waɗanda suke jin sun amfana daga kāriyarsa. Ko da yake yana da wuya a kammala cewa Allah ya sa hannu ko kuma bai sa ba a irin yanayin. Fashewar wata nakiya a Toulouse ta ji rauni wa bayin Jehovah masu aminci da yawa kuma dubban Kiristoci masu aminci sun mutu a sansanin Nazi da kuma na Kwaminis ko kuma a cikin wasu yanayi na bala’i da Allah bai sa hannu ba ya hana. Me ya sa Allah ba ya bi ya kāre dukan waɗanda suke da tagomashinsa ba?—Daniel 3:17, 18.
‘Sa’a da Tsautsayi’
Sa’ad da bala’i ya auku, ba ya zaɓan mutanen da zai shafe su, ko kana da aminci ga Allah ko ba ka da shi. Sa’ad da nakiyar ta fashe a Toulouse, da Alain da Liliane suka tsira, mutane 30 suka mutu kuma ɗaruruwa suka ji rauni, duk da cewa ba laifinsu ba ne. A hanya mai girma kuma, mutane dubbai suna faɗāwa a hannun masu aika laifi, direbobi da ba sa kula, ko kuma yaƙe-yaƙe, amma ba za a ga laifin Allah ba domin masifar da ta same su. Littafi Mai Tsarki ya tunasar da mu cewa ‘sa’a da tsautsayi’ sukan same kowannenmu.—Mai-Wa’azi 9:11.
Ban da haka ma, ’yan Adam suna ciwo, suna tsufa, kuma suna mutuwa. Har waɗanda suke tunanin Allah ya ceci ransu ta mu’ujiza ko waɗanda suke yaba masa saboda sun samu sauƙi daga ciwon da suke yi sukan mutu su ma. Kawar da ciwo da mutuwa da kuma ‘share dukan hawaye’ daga idanun mutane yana nan gaba ne.—Ru’ya ta Yohanna 21:1-4.
Domin wannan ya faru, ana bukatar wani abu mafi girma maimakon sa hannu na lokaci lokaci kawai. Littafi Mai Tsarki ya yi magana game da wani aukuwa da aka kira “babbar ranar Ubangiji.” (Zephaniah 1:14) A lokacin sa hannu mai girman nan, Allah zai kawar da mugunta duka. Mutane za su sami zarafi na rayuwa har abada a yanayi kamiltacce, inda “ba za a tuna da al’amura na dā ba, ba kuwa za su shiga zuciya ba.” (Ishaya 65:17) Har ma za a dawo da matattu zuwa rai, juyar da bala’i mafi girma ke nan na ’yan Adam duka. (Yohanna 5:28, 29) Zai zamana cewa Allah cikin ƙaunarsa marar iyaka da kuma alherinsa ya magance matsalolin ’yan Adam ke nan sarai.
Yadda Allah Yake Sa Hannu a Yau
Amma, wannan ba ya nufin cewa a lokaci na jiran nan, Allah yana kallo ne ba ya damuwa da azabar halittu ba. A yau, Allah yana ba wa dukan mutane, zarafi su san shi kuma su yi dangantaka da shi ko da daga wace ƙasa ko yanayin zama suka fito. (1 Timothawus 2:3, 4) Yesu ya kwatanta matakin a waɗannan kalmomi: “Ba wanda ya iya zuwa wurina, sai dai Uba wanda ya aiko ni ya jawo shi.” (Yohanna 6:44) Allah yana jawo mutane masu zuciyar kirki wurinsa ta saƙon Mulkin da bayinsa suke yi a dukan duniya.
Ban da haka, Allah yana sarrafa rayuwar waɗanda suke son ya yi musu ja-gora. Ta wurin ruhunsa mai tsarki, Allah yana ‘buɗe zuciyarsu’ su fahimci nufinsa kuma aikata farillansa. (Ayukan Manzanni 16:14) Hakika, ta wurin ba da zarafin a sami saninsa, Kalmarsa, da kuma ƙudurinsa, Allah yana ba da tabbacin ƙaunarsa ga kowannenmu.—Yohanna 17:3.
A ƙarshe, Allah yana taimakon bayinsa a yau ba ta wurin yi musu ceto na mu’ujiza ba amma ta wurin ba su ruhu mai tsarki da kuma “mafificin girman iko” don su iya jimre da dukan yanayi da za su fuskanta. (2 Korinthiyawa 4:7) Manzo Bulus ya rubuta: “Na iya yin abu duka a cikin wannan [Jehovah Allah] da yake ƙarfafata.”—Filibbiyawa 4:13.
Saboda haka, muna da kowanne dalili na yin godiya ga Allah kowacce rana kuma domin bege da ya ba mu mu rayu har abada cikin duniya babu wahala. “Me zan bayar ga Ubangiji sabili da dukan alherinsa a gareni?” tambayar mai Zabura ke nan. “In karɓi ƙoƙon ceto, in kira bisa sunan Ubangiji.” (Zabura 116:12, 13) Idan kana karatun wannan jaridar a kai a kai za ka fahimci abin da Allah ya yi, da yake yi, da zai yi ya kawo maka farin ciki yanzu da kuma tabbataccen bege a nan gaba.—1 Timothawus 4:8.
[Bayanin da ke shafi na 6]
“Ba za a tuna da al’amura na dā ba, ba kuwa za su shiga zuciya ba.”—Ishaya 65:17
[Hotuna a shafi na 5]
Ko a lokatai na Littafi Mai Tsarki ma Jehovah bai hana a jejjefe Zechariah ba . . .
ko ya hana Hirudus kashe marasa laifi ba
[Hoto a shafi na 7]
Lokaci ya kusa da ba za a sha wahala ba kuma; har matattu za su sake rayuwa