Maganar Jehobah Rayayya Ce
Darussa Daga Littafin Ishaya na Biyu
ANNABI Ishaya yana aikinsa da aminci. Abin da ya faɗa game da ƙabila goma da ke masarautar Isra’ila ta kasance da gaske. Yana da wani saƙo yanzu game da abin da zai sami Urushalima a nan gaba.
Za a halaka birnin Urushalima, kuma za a kwashe mazaunanta zuwa bauta. Amma halakar ba zai kasance na dindindin ba. Bayan ɗan lokaci, za a dawo da bauta ta gaskiya. Wannan ne ainihin saƙon da ke cikin Ishaya 36:1–66:24.a Za mu amfana idan muka tattauna abin da ke cikin waɗannan surori, saboda yawancin waɗannan annabce-annabcen da aka ambata a wannan sashen suna cika a zamaninmu, ko kuma a nan gaba. Wannan sashe na littafin Ishaya yana ɗauke da annabce-annabce masu motsawa game da Almasihu.
“GA SHI, KWANAKI SUNA ZUWA”
(Ishaya 36:1–39:8)
A shekara ta goma sha huɗu ta sarautar Hezekiah (732 K.Z.), Assuriyawa sun kai wa Yahuda hari. Jehobah ya yi alkawari cewa zai kāre Urushalima. Wannan barazanar ta kai masu hari ta ƙare sa’ad da mala’ika guda ɗaya tak ya kashe sojojin Assuriya 185,000.
Sa’ad da Hezekiah ya yi rashin lafiya, Jehobah ya amsa addu’arsa ya warkar da shi, kuma ya ƙara masa shekaru 15 a rayuwarsa. Sa’ad da sarkin Babila ya aika bayinsa su taya shi murna, Hezekiah ya nuna masu duka dukiyoyinsa. Ishaya ya gaya wa Hezekiah saƙon Jehobah, yana cewa: “Ga shi, kwanaki suna zuwa, inda dukan abin da ke cikin gidanka; da dukan abin da ubaninka suka ajiye har wa yau, za a ɗauka a kai Babila.” (Ishaya 39:5, 6) Wannan annabcin ta cika bayan shekara 100.
Tambayoyin Nassi da Aka Amsa:
38:8 Waɗanne “matakai” ne suke sa inuwar ta koma da baya? Tun da yake ana yin amfani da na’urar sanin lokaci a ƙasar Masar da Babila a ƙarni na takwas K.Z., wataƙila waɗannan matakalai suna nuna yawan na’urar da mahaifin Hezekiah, Ahaz, yake da su. Ko kuwa a cikin fadar akwai matakalan bene. Wataƙila ana yin amfani da inuwar ginshiƙin da ke gefen matakalar don sanin lokaci.
Darussa Dominmu:
36:2, 3, 22. Ko da yake an sallame shi daga hidimar mai kula da gidan sarki, an ƙyale Shebna ya ci gaba da yin hidima a gidan sarki a matsayin sakataren wanda ya ɗauki matsayinsa. (Ishaya 22:15, 19) Idan aka saukar da mu daga wani matsayi a cikin ƙungiyar Jehobah saboda wani dalili, zai yi kyau mu ci gaba da bauta wa Allah a kowace hanya da ta dace.
37:1, 14, 15; 38:1, 2. A lokacin wahala, zai yi kyau mu yi addu’a ga Jehobah mu kuma dogara a gare shi.
37:15-20; 38:2, 3. Sa’ad da Assuriyawa suka yi wa Urushalima barazana, Hezekiah ya damu sosai saboda idan aka ci su a yaƙi, hakan zai ɓata sunan Jehobah. Sa’ad da ya ji cewa ciwonsa zai kai shi ga mutuwa, Hezekiah bai soma tunanin kansa kawai ba. Abin da ya fi damunsa shi ne, idan ya mutu ba shi da ɗa, hakan zai shafi zuriyar Dauda ta sarakuna. Ya kuma damu da wanda zai ja-goranci Isra’ilawa zuwa yaƙi da Assuriyawa. Kamar Hezekiah, ya kamata mu ɗauki tsarkake sunan Jehobah da muhimmanci da kuma yadda nufinsa zai cika fiye da yadda za mu tsira.
38:9-20. Wannan waƙar ta Hezekiah ta koya mana cewa babu abin da ya fi yabon Jehobah muhimmanci a rayuwa.
“ZA A GINA TA”
(Ishaya 40:1–59:21)
Nan da nan bayan ya annabta halakar Urushalima da kuma zuwa bauta a Babila, Ishaya ya annabta game da komowa. (Ishaya 40:1, 2) Ishaya 44:28 ta ce: “Za a gina [Urushalima].” Za a ɗauki allolin gumaka na mutanen Babila kamar “abin nawaiyawa.” (Ishaya 46:1) Za a halaka Babila. Waɗannan annabce-annabcen sun faru bayan ƙarni na biyu.
Bayin Jehobah za su “zama haske ga al’ummai.” (Ishaya 49:6) “Sammai” na Babila ko kuwa masu sarauta, za su “shuɗe kamar hayaƙi,” kuma mazaunanta “za su mutu hakanan,” amma ‘ɗiyar Sihiyona mai-shan bauta za ta kwance sarƙoƙin wuyanta.’ (Ishaya 51:6; 52:2) Jehobah ya ce wa waɗanda za su zo gare shi kuma su saurare shi cewa: ‘Zan yi madawwamin alkawari da ku, jiyejiyenƙai tabbatattu ke nan na Dauda.’ (Ishaya 55:3) Yin rayuwar da ta jitu da farillai masu aminci na Allah zai sa ka “faranta zuciyarka cikin Ubangiji.” (Ishaya 58:14) Amma laifofin mutanen sun ‘raba tsakaninsu da Allahnsu.’—Ishaya 59:2.
Tambayoyin Nassi da Aka Amsa:
40:27, 28—Me ya sa Isra’ila ta ce: “Tafarkina yana ɓoye ga Ubangiji, an ƙyale shari’ata a wurin Allahna”? Wasu Yahudawa a Babila sun ga kamar Jehobah ba ya ganin rashin adalcin da suke fuskanta. Amma an tuna masu cewa Babila ba ta fi ƙarfin Mahaliccin duniya ba, wanda ba ya gajiya.
43:18-21—Me ya sa aka ce wa waɗanda suka dawo daga zaman bauta ‘Kada su tuna da al’amura na dā’? Ba wai ana nufin su mance da yadda Jehobah ya cece su ba ne. Amma, Jehobah yana son su bauta masa ta ‘wani sabon al’amari’ da za su fahimta da kansu, kamar tafiyarsu zuwa Urushalima, wataƙila ta wata hanya mai hamada. “Taro mai-girma” waɗanda suka fito daga “cikin babban tsanani” za su samu sabon dalilin ɗaukaka Jehobah.—Ru’ya ta Yohanna 7:9, 14.
49:6—Ta yaya ne Almasihu ya zama “haske ga al’ummai,” ko da yake hidimarsa ga ’ya’yan Isra’ila ne kawai? Haka yake saboda abin da ya faru bayan mutuwar Yesu. Littafi Mai Tsarki ya yi amfani da Ishaya 49:6 ga almajiran Yesu. (Ayukan Manzanni 13:46, 47) A yau, shafaffun Kiristoci, tare da taro mai girma na masu bauta wa Allah, sun zama “haske ga al’ummai,” kuma suna koyar da mutane “har iyakacin duniya.”—Matta 24:14; 28:19, 20.
53:10—Ta yaya ne Jehobah ya yi farin cikin ƙuje Ɗansa? Jehobah Allah ne mai juyayi, kuma ya ji zafin ganin Ɗansa ƙaunatacce yana shan azaba. Duk da haka, ya yi farin cikin biyayyar da Yesu ya yi da kuma abin da wahala da mutuwarsa za su cim ma.—Misalai 27:11; Ishaya 63:9.
53:11—Da wane sani ne Almasihu zai “baratadda masu-yawa”? Wannan sani ne da Yesu ya samu sa’ad da ya zo duniya, ya zama mutum, kuma ya sha wahala ba gaira ba dalili har ya mutu. (Ibraniyawa 4:15) Ya yi hadayar fansa, wanda ake bukata don a taimaka wa shafaffun Kiristoci da taro mai girma domin su kasance da adalci a gaban Allah.—Romawa 5:19; Yaƙub 2:23, 25.
56:6—Su wanene “baƙi,” kuma ta wace hanya ce suke “riƙe da wa’adi” na Jehobah? “Waɗansu tumaki” na Yesu ne ‘baƙin.’ (Yohanna 10:16) Suna riƙe da sabon alkawari domin suna yin biyayya ga dokokin da suka jitu da ita, kuma suna ba da haɗin kai ga tsarin da aka yi daga cikinta, suna cin abinci na ruhaniya kamar yadda shafaffun Kiristoci suke ci, kuma suna taimakonsu a wa’azin Mulki da almajirantarwa.
Darussa Dominmu:
40:10-14, 26, 28. Jehobah yana da iko da haƙuri, shi mafi-iko ne, da kuma hikima fiye da yadda za mu iya fahimta.
40:17, 23; 41:29; 44:9; 59:4. Haɗa kai da ’yan siyasa da gumaka duka ‘banza’ ne. Saboda haka haɗa kai da su ba shi da amfani.
42:18, 19; 43:8. Idan muka yi watsi da Kalmar Allah kuma muka daina sauraron umurninta ta wurin “bawan nan mai-aminci, mai-hikima” za mu rasa ruhaniyarmu.—Matta 24:45.
43:25. Jehobah yana share laifuffukanmu domin kansa. Tsarkake sunan Allah ya fi ’yancin da muka samu daga zunubi da mutuwa da kuma rai na dindindin.
44:8. Muna samun taimako daga wurin Jehobah, wanda yake da ƙarfi kamar dutse. Kada mu ji tsoron shelar Allahntakarsa.—2 Samuila 22:31, 32.
44:18-20. Bautar gumaka alama ce mai nuna zuciyar da ta ɓace. Kada komi ya ɗauki matsayin Jehobah a zuciyarmu.
46:10, 11. Ingancinsa na ‘tabbatar da ƙudurinsa,’ wato, cika nufinsa, yana tabbatar da Allahntakan Jehobah.
48:17, 18; 57:19-21. Idan muka dogara da Jehobah don samun ceto, muka kusace shi, kuma muka bi dokokinsa, salamarmu za ta yi yawa kamar ruwan rafi mai zubowa kuma halayenmu masu kyau za su yi yawa kamar raƙuman teku. Waɗanda ba su lura da Kalmar Allah ba suna kama da “teku mai-hauka.” Ba su da salama.
52:5, 6. Babiloniyawa sun kammala cewa Allah na gaskiya ya raunana. Ba su fahimci cewa Jehobah ya yi fushi da mutanensa ne ba, shi ya sa Isra’ila ta je bauta a Babila. Idan matsala ta faɗa wa wasu, ba shi da kyau mu yi saurin kammala dalilin da ya sa hakan ya faru.
52:7-9; 55:12, 13. Muna da aƙalla dalilai uku da za su sa mu farin ciki a wa’azin Mulki da almajirantarwa. Mutane masu tawali’u da suke neman abinci na ruhaniya suna farin cikin ganin mu. Muna ganin Jehobah “ido da ido,” ko kuma muna da dangantaka na kud da kud da shi. Muna kuma jin daɗin ni’ima ta ruhaniya.
52:11, 12. Domin mu yi nasarar “ɗaukan kayan Ubangiji” kuma mu bauta masa, dole ne mu tsarkaka ruhaniyarmu da ɗabi’armu.
58:1-14. Idan muna nuna cewa mu masu ibada ne da kuma adalci da baki kawai, wannan duk banza ne. Ya kamata masu bauta ta gaskiya su zama masu ibada su kuma ƙaunaci ’yan’uwansu.—Yohanna 13:35; 2 Bitrus 3:11.
59:15b-19. Jehobah yana ganin harkokin ’yan Adam kuma zai sa hannu a lokacin da ya ga ya dace.
ZA TA ZAMA “ƘAMBIN JAMALI”
(Ishaya 60:1–66:24)
Game da komo da bauta ta gaskiya a zamanin dā da kuma a kwanakinmu, Ishaya 60:1 ta ce: “Tashi, ki bada haske; gama haskenki ya zo, darajar Ubangiji kuma ya hau bisa kanki.” Dole ne Sihiyona ta zama ‘ƙambin jamali a cikin hannun Ubangiji.’—Ishaya 62:3.
Ishaya ya yi addu’a ga Jehobah domin mutanen ƙasarsu waɗanda za su tuba a lokacin da suke zaman bauta a ƙasar Babila. (Ishaya 63:15–64:12) Bayan da ya kwatanta bambancin mabiyan gaskiya da ta ƙarya, annabin ya sanar da yadda Jehobah zai albarkaci waɗanda suke bauta masa.—Ishaya 65:1–66:24.
Tambayoyin Nassi da Aka Amsa:
61:8, 9—Menene “madawwamin alkawari,” kuma su wanene “zuriyar”? Wannan shi ne sabon alkawarin da Jehobah ya kammala da shafaffun Kiristoci. “Zuriyar” su ne “waɗansu tumaki,” wato mutane da yawa da suka bi saƙonsu.—Yohanna 10:16.
63:5—Ta yaya ne hasalar Allah take taimakonsa? Allah yana kame kansa idan ya yi fushi. Fushinsa na taimaka masa kuma yana motsa shi ya yi huƙunci cikin adalci.
Darrusa Dominmu:
64:6. Mutane ajizai ba za su iya ceton kansu ba. Idan ya zo ga neman gafara domin zunubansu, ayyukansu na adalci ba zai iya cetonsu ba.—Romawa 3:23, 24.
65:13, 14. Jehobah yana yi wa bayinsa masu aminci albarka, kuma yana ba su abinci na ruhaniya daidai bukatarsu.
66:3-5. Jehobah ya ƙi jinin munafunci.
“Ku Yi Murna”
Annabcin maidowa ya ƙarfafa Yahudawa masu aminci da suke zaman bauta a Babila! Jehobah ya ce: “Ku yi murna ku yi farinciki har abada da abin da ni ke halittawa; gama, ga shi, na halitta Urushalima abin murna, mutanenta kuma abin farinciki.”—Ishaya 65:18.
Mu ma muna zaune a lokacin da duhu ya rufe duniya, al’ummai kuma suna cikin duhu. (Ishaya 60:2) “Miyagun zamanu za su zo.” (2 Timothawus 3:1) Saboda haka, saƙon ceto na Jehobah da aka ba da a cikin Littafi Mai Tsarki na Ishaya yana ƙarfafa mu.—Ibraniyawa 4:12.
[Hasiya]
a Domin tattaunawar Ishaya 1:1-35:10, ka karanta “Maganar Jehobah Rayayya Ce—Darussa Daga Littafin Ishaya na Ɗaya” a Hasumiyar Tsaro ta 1 ga Disamba ta shekara ta 2006.