Ceto Ga Waɗanda Suka Zaɓi Haske
“Ubangiji ne haskena da cetona, ba zan ji tsoron kowa ba.”—ZABURA 27:1.
1. Wane tanadi ne Jehovah ya yi mai ba da rai?
JEHOVAH ne Tushen hasken rana da ya sa rayuwa ta yiwu a duniya. (Farawa 1:2, 14) Shi ne kuma har ila Mahaliccin haske na ruhaniya, wanda yake ƙorar duhu mai halakarwa na duniyar Shaiɗan. (Ishaya 60:2; 2 Korantiyawa 4:6; Afisawa 5:8-11; 6:12) Waɗanda suka zaɓi hasken za su faɗa tare da mai Zabura: “Ubangiji ne haskena da cetona, ba zan ji tsoron kowa ba.” (Zabura 27:1a) Duk da haka, kamar yadda ya faru a zamanin Yesu, waɗanda suka gwammace duhu za su yi tsammanin hukunci ne mai tsanani.—Yahaya 1:9-11; 3:19-21, 36.
2. A zamanin dā, menene ya faru da waɗanda suka ƙi hasken Jehovah da kuma waɗanda suka saurari kalmarsa?
2 A zamanin Ishaya, yawancin mutanen alkawari na Jehovah sun ƙi haske. Sakamakon haka, Ishaya ya ga halakar sarautar arewacin al’ummar Isra’ila. Kuma a 607 K.Z., Urushalima da haikalinta aka halaka su kuma mutanen Yahuza aka kwashe su zuwa hijira. Ko da yake, waɗanda suka saurari kalmar Jehovah an ƙarfafa su su tsayayya wa ridda ta zamanin. Game da 607 K.Z., Jehovah ya yi alkawarin cewa waɗanda suka saurare shi za su tsira. (Irmiya 21:8, 9) A yau, mu da muke ƙaunar haske za mu koyi abubuwa da yawa daga abin da ya faru a dā can.—Afisawa 5:5.
Farin Cikin Waɗanda Suke da Haske
3. A yau, wane tabbaci muke da shi, kuma wace “amintacciyar al’umma” muke ƙauna, kuma wane “birni ƙaƙƙarfa” wannan “al’umma” take da ita?
3 “Birni ƙaƙƙarfa ne, Allah kansa ke tsare garukansa! A buɗe ƙofofin birnin, a bar amintacciyar al’umma ta shiga, al’ummar da jama’arta ke aikata abin da ke daidai.” (Ishaya 26:1, 2) Waɗannan kalmomin ɗaukaka ne na mutane da suka dogara ga Jehovah. Amintattun Yahudawa a zamanin Ishaya sun saurari Jehovah, Tushen kwanciyar rai, ba allolin ƙarya ba na sauran mutanen ƙasar. A yau, muna da irin wannan tabbacin. Ƙari ga haka, muna ƙaunar “amintacciyar al’umma” na Jehovah—“Isra’ilan gaske na Allah.” (Galatiyawa 6:16; Matiyu 21:43) Jehovah ma yana ƙaunar wannan al’umma domin ɗabi’arta ta aminci. Da albarkarsa, Isra’ila ta Allah tana da “birni ƙaƙƙarfa,” ƙungiya mai kama da birni da take taimako kuma take kāre ta.
4. Wane hali ya kamata mu koya?
4 Waɗanda suke cikin wannan “birni” sun sani cewa “kai ke ba da cikakkiyar salama, ya [Jehovah], ga waɗanda ke riƙe da manufarsu da ƙarfi, waɗanda ke dogara gare ka [Jehovah].” Jehovah yana taimaka wa waɗanda suke dogara a gare shi kuma suke bin umurnansa na adalci. Saboda haka, masu aminci a Yahuza suka bi umurnin Ishaya: “Ku dogara ga Ubangiji har abada. Zai kiyaye mu kullayaumin.” (Ishaya 26:3, 4; Zabura 9:10; 37:3; Karin Magana 3:5) Waɗanda suke da wannan zuciyar suna zuba wa ‘Jah Jehovah’ idanu wanda zai kiyaye su kullayaumi. Suna morar “cikakkiyar salama” tare da shi.—Filibiyawa 1:2; 4:6, 7.
Wulaƙanci ga Abokan Gaba na Allah
5, 6. (a) Ta yaya aka wulaƙanta Babila ta dā? (b) A wace hanya ce aka wulaƙanta “Babila mai girma?”
5 To, yaya idan waɗanda suka dogara ga Jehovah suka sha tsanani? Ba sa bukatar su tsorata. Jehovah yana ƙyale irin waɗannan abubuwa na ɗan lokaci ne, amma daga baya yana sauƙaƙawa, kuma waɗanda suke tsananta musu za su fuskanci hukunci. (2 Tasalonikawa 1:4-7; 2 Timoti 1:8-10) Ka yi la’akari da batun wani “ƙaƙƙarfan birnin.” Ishaya ya ce: “[Jehovah] ya ƙasƙantar da masu girmankai, Ya hallaka ƙaƙƙarfan birnin da suke zaune ciki, ya rusa garunsa ƙasa. Waɗanda aka zalunta, a kansa suke tafiya yanzu, suna tattaka shi da ƙafafunsu.” (Ishaya 26:5, 6) Ƙaƙƙarfan birnin da aka ambata a nan mai yiwuwa Babila ce. Wannan birnin babu shakka ya tsananta wa mutanen Allah. Amma menene ya faru da Babila? A shekara ta 539 K.Z. Midiyawa da Fasiyawa suka ci ta a yaƙi. Ƙasƙanta ce ƙwarai!
6 A zamaninmu kalmomin annabci na Ishaya suna kwatanta abin da ya faru da “Babila mai girma” tun daga shekara ta 1919. Wannan ƙaƙƙarfan birnin ya yi faɗuwar wulaƙanci a shekarar da aka tilasta masa ya saki mutanen Jehovah daga hijira ta ruhaniya. (Wahayin Yahaya 14:8) Abin da ya faru daga baya ma ya fi wulaƙanci. Wannan ƙaramin rukunin ya juya yana ‘tattaka wanda ya kama shi dā da ƙafafu. A shekara ta 1922 suka fara sanar da zuwan ƙarshen Kiristendam, suna sanar da busa ƙaho na mala’iku huɗu na Wahayin Yahaya 8:7-12 da kuma kaito uku da aka annabta a Wahayin Yahaya 9:1–11:15.
“Hanyar Mutanen Kirki ta Yi Sumul”
7. Wace ja-gora ce waɗanda suke juya ga hasken Jehovah suke samu, kuma ga wanene suke da bege, kuma menene suke ƙauna?
7 Jehovah yana ceton waɗanda suke juyawa ga haskensa, kuma yana ja-gorar hanyarsu kamar yadda Ishaya ya nuna a gaba: “Ka sa hanyar mutanen kirki ta yi sumul, hanyar da suke bi ta yi bai ɗaya, Muna bin nufinka, muna sa zuciya gare ka. Kai kaɗai ne bukatarmu.” (Ishaya 26:7, 8) Jehovah Allah ne mai adalci, kuma waɗanda suke bauta masa dole ne su kiyaye umurnansa na adalci. Idan suka yi haka, Jehovah yana ja-gorarsu, yana sumulmula hanyarsu. Ta wajen bin ja-gorarsa, waɗannan masu tawali’u suke nuna cewa suna da bege ga Jehovah kuma da zuciya ɗaya suna ƙaunar sunansa—‘abin tunawa’ da shi.—Fitowa 3:15.
8. Wane hali ne mai kyau Ishaya ya nuna?
8 Ishaya ya ƙaunaci sunan Jehovah. Wannan ya bayyana a nasa kalmomi na gaba: “Da dare ina zuba ido gare ka da zuciya ɗaya. Sa’ad da kake yi wa duniya da jama’arta shari’a dukansu za su san yadda adalci yake.” (Ishaya 26:9) Ishaya ya zuba wa Jehovah ido da ‘zuciya ɗaya’—da dukan ransa. Ka yi tunani annabin yana addu’a ga Jehovah a lokacin da kome ya yi tsit, yana furta tunanin zuciyarsa kuma yana neman ja-gorar Jehovah. Misali ne mai kyau! Ƙari ga haka, Ishaya ya koyi adalci daga ayyukan hukunci na Jehovah. A wannan, ya tunasar da mu bukatar kasance wa a farke ko da yaushe, zama cikin hankalinmu domin mu fahimci nufin Jehovah.
Wasu Sun Zaɓi Duhu
9, 10. Wane kirki Jehovah ya yi wa al’ummarsa marar aminci, amma kuma yaya suka amsa?
9 Jehovah ya nuna ƙauna ƙwarai ga Yahuza, amma abin baƙin ciki ba duka ba ne suka karɓa. A kai a kai, yawanci suka zaɓi su yi tawaye da kuma ridda maimakon hasken gaskiya na Jehovah. Ishaya ya ce: “Ko da ya ke kana yi wa mugaye alheri, duk da haka ba su taɓa koyon abin da yake na kirki ba. Har a nan ma, a ƙasar adalai, suna ta aikata kuskure, sun ƙi ganin girmanka.”—Ishaya 26:10.
10 A zamanin Ishaya, lokacin da Jehovah ya kāre Yahuza daga abokan gabanta, yawancin suka ƙi su fahimci hakan. Lokacin da ya albarkace su da salamarsa, al’ummar ba ta yi godiya ba. Saboda haka, Jehovah ya ƙyale su su yi wa wasu “bauta,” a ƙarshe ya ƙyale aka kwashe Yahudawa zuwa hijira a Babila a shekara ta 607 K.Z. (Ishaya 26:11-13) Daga baya, raguwarsu suka komo, a hore suka koma ƙasarsu.
11, 12. (a) Menene waɗanda suka kama Yahuza suke da shi a nan gaba? (b) A shekara ta 1919 menene waɗanda suka kama bayin Allah shafaffu suke da shi a nan gaba?
11 Waɗanda suka kama Yahuza fa? Ishaya ya amsa cikin annabci: “Yanzu kuwa sun mutu, ba za su ƙara rayuwa ba, kurwarsu ba za ta tashi ba, domin ka hukunta su, ka hallaka su. Ba wanda zai ƙara tunawa da su.” (Ishaya 26:14) Hakika, bayan faɗuwarta a shekara ta 539 K.Z. Babila ba ta da saurar rayuwa a nan gaba. Da shigewar lokaci, birnin ba za ta kasance ba. Ba za ta “ƙara rayuwa ba,” kuma daularta mai girma ta zama dutsen gina tarihi. Gargaɗi ne ga waɗanda suke bege da masu ƙarfi na wannan duniyar!
12 Ɓangaren wannan annabci ya cika lokacin da Allah ya ƙyale bayinsa shafaffu suka je hijira ta ruhaniya a shekara ta 1918 kuma ya ’yantar da su a shekara ta 1919. Daga wannan lokacin zuwa gaba, waɗanda suka kama su dā, musamman Kiristendam ba su da saurar rayuwa a nan gaba. Amma albarkar da take ajiye wa mutanen Jehovah suna da kyau ƙwarai.
“Ka Sa Al’ummarmu ta Yi Ƙarfi”
13, 14. Wace albarka ce mai girma bayin Jehovah shafaffu suka more tun daga shekara ta 1919?
13 Allah ya albarkaci halin tuba na bayinsa shafaffu a shekara ta 1919 ya ba su ƙari. Da farko aka mai da hankali wajen tara saura na Isra’ila ta Allah, sai kuma aka tattara “taro mai girma” na “waɗansu tumaki.” (Wahayin Yahaya 7:9; Yahaya 10:16) Waɗannan albarka an faɗe su a cikin annabcin Ishaya: “Ya Ubangiji, ka sa al’ummarmu ta yi ƙarfi, ka faɗaɗa karkararta a kowane gefe, wannan kuwa ya sa ana girmama ka. Ka hukunta jama’arka, ya Ubangiji, a cikin azaba sun yi addu’a gare ka.”—Ishaya 26:15, 16.
14 A yau, iyaka ta Isra’ila ta Allah ya bazu a cikin duniya, kuma taro mai girma da aka daɗa yanzu ya kai miliyan shida na masu yin wa’azin bishara da ƙwazo. (Matiyu 24:14) Albarka ce daga wurin Jehovah! Kuma wannan yana kawo ɗaukaka ga sunansa! Wannan sunan ana jinsa a ƙasashe 235—cikar alkawarinsa na ban mamaki.
15. Wane tashin matattu ne na alama ya faru a shekara ta 1919?
15 Yahuza tana bukatar taimakon Jehovah ta tsira daga hijira a Babila. Da ba su yi nasara ba in don kansu ne. (Ishaya 26:17, 18) Hakanan, ’yantar da Isra’ila ta Allah a 1919 tabbaci ne na taimakon Jehovah. Da bai faru ba idan babu shi. Canjin yanayinsu abin mamaki ne ƙwarai shi ya sa Ishaya ya kwatanta shi da tashin matattu: “Mutanenmu da suka mutu za su sāke rayuwa! Jikunansu za su sāke rayuwa! Dukan waɗanda ke kwance cikin kaburburansu za su farka, su yi waƙa don farin ciki! Kamar laimar raɓa wanda ke wartsakar da duniya, haka Ubangiji zai rayar da waɗanda suka daɗe da mutuwa.” (Ishaya 26:19; Wahayin Yahaya 11:7-11) Hakika, waɗanda suke zaune cikin turɓaya, za su tashi, kamar yadda yake, ga sabonta ayyuka!
Kāriya a Miyagun Lokatai
16, 17. (a) A shekara ta 539 K.Z., menene Yahudawa suke bukatar yi domin su tsira daga faɗuwar Babila? (b) Wataƙila, menene ne ‘gidaje’ a yau, kuma ta yaya suke mana amfani?
16 Bayin Jehovah kullayaumi suna bukatar kāriyarsa. Ba da jimawa ba, zai miƙa hannunsa na ƙarshe bisa duniyar Shaiɗan, kuma masu bauta masu za su bukaci taimakonsa fiye da dā. (1 Yahaya 5:19) Game da wannan mugun lokacin, Jehovah ya yi mana kashedi: “Jama’ata, ku shiga gidajenku, ku kukkulle ƙofofi, ku ɓoye kanku ɗan lokaci, kafin Allah ya huce daga fushinsa. Ubangiji yana zuwa ya hukunta jama’arsa a duniya saboda zunubansu. Kashe-kashen da aka yi a duniya a ɓoye, za a bayyana su, ƙasa ba za ta ƙara ɓoye waɗanda aka kashe ba.” (Ishaya 26:20, 21; Zafaniya 1:14) Wannan gargaɗin ya nuna wa Yahudawa yadda za su tsira daga faɗuwar Babila a 539 K.Z. Waɗanda suka yi biyayya da za su zauna a cikin gidajensu, a tsare daga sojoji da suka yi nasara na kan tituna.
17 A yau, ‘gidaje’ na annabcin wataƙila ikilisiyoyi dubbai ne na mutanen Jehovah a dukan duniya. Ikilisiyoyin nan wajen kāriya ne har a yanzu ma, waje ne inda Kiristoci sukan samu kwanciyar hankali tsakanin ’yan’uwansu, cikin kula ta ƙauna na dattawa. (Ishaya 32:1, 2; Ibraniyawa 10:24, 25) Wannan haka yake musamman ma saboda kusatowar ƙarshen wannan tsarin abubuwa lokacin da tsira za ta dangana bisa biyayya.—Zafaniya 2:3.
18. Ta yaya Jehovah zai kashe “dodon da ke cikin teku” ba da daɗewa ba?
18 Game da wannan lokacin, Ishaya ya yi annabci: “A wannan rana Ubangiji zai yi amfani da takobinsa mai ƙarfi, mai muguwar ɓarna, don ya hukunta dodon ruwan nan mai kanannaɗewa, mai murɗewa, ya kashe dodon da ke cikin teku.” (Ishaya 27:1) Menene ne “dodon ruwa” na zamani? A bayyane yake, “macijin nan ne na tun dā dā,” Shaiɗan kansa, tare da mugun tsarin abubuwansa, wanda yake amfani da shi wajen yaƙi da Isra’ila ta Allah. (Wahayin Yahaya 12:9, 10, 17; 13:14, 16, 17) A shekara ta 1919, “dodon ruwan” ya ƙyale mutanen Allah. Nan gaba, zai ɓace ma gabaki ɗaya. (Wahayin Yahaya 19:19-21; 20:1-3, 10) Saboda haka, Jehovah zai “kashe dodon da ke cikin teku.” A yanzu, babu abin da Dodon Ruwan zai yi ƙoƙarin yi wa mutanen Jehovah da zai yi nasara har abada. (Ishaya 54:17) Abin ƙarfafa ne a tabbatar mana da wannan!
“Kyakkyawar Gonar Inabinsa”
19. Menene yanayin raguwar a yau?
19 Bisa ga dukan wannan hasken daga Jehovah, ba muna da dalilin murna ba ne? Hakika, muna da shi! Ishaya ya kwatanta da kyau farin cikin mutanen Jehovah lokacin da ya rubuta: “A wannan rana Ubangiji zai yi magana a kan kyakkyawar gonar inabinsa, ya ce, ‘Ina tsaronta ina yi mata banruwa kowane lokaci, ina tsaronta dare da rana, don kada a yi mata ɓarna.” (Ishaya 27:2, 3) Jehovah ya kula da “gonar inabinsa,” raguwar Isra’ila ta Allah, da kuma abokan tarayyarsu masu ƙwazo. (Yahaya 15:1-8) Sakamakon haka ’ya’ya ne da suke ɗaukaka sunansa kuma yana kawo farin ciki tsakanin bayinsa a duniya.
20. Ta yaya Jehovah ya kāre ikilisiyar Kirista?
20 Za mu yi farin ciki cewa fushin Jehovah na farko da bayinsa shafaffu—da ya sa ya ƙyale su suka je hijira na ruhaniya a 1918—ya huce. Jehovah kansa ya ce: “Ba zan ƙara yin fushi da gonar inabin ba. Da ma a ce akwai ƙayayuwa da sarƙaƙƙiya in yi faɗa da su, da na ƙone su ƙurmus. Amma idan maƙiyan jama’ata suna so in cece su, sai su yi sulhu da ni, i, bari su yi sulhu da ni.” (Ishaya 27:4, 5) Don ya tabbata cewa gonar inabinsa ta ci gaba da ba da ’ya’ya da yawa na “inabi,” Jehovah yana ragargaza kuma ya ƙona ƙurmus na wani rinjaya da ke kama da ƙayayuwa da zai iya lalata su. Saboda haka, kada wani ya saka lafiyar ikilisiyar Kirista cikin haɗari! Bari duka su samu ‘mafaka wurin Jehovah,’ suna biɗan albarkarsa da kuma kāriya. Yin haka, muna yin salama da Allah—aba da take da muhimmanci ƙwarai da Ishaya ya ambata har sau biyu.—Zabura 85:1, 2, 8; Romawa 5:1.
21. A wace hanya ce aka cika ƙasa mai hayayyafa da “ ’ya’ya”?
21 Albarkar ta ci gaba: “A wannan rana jama’ar Isra’ila, zuriyar Yakubu, za su yi saiwa kamar itace, za su yi toho, su yi fure. ’Ya’yan da suka yi za su cika duniya.” (Ishaya 27:6) Wannan ayar ta cika tun shekara ta 1919, tana ba da tabbaci na ban mamaki na ikon Jehovah. Shafaffun Kiristoci suna cika duniya da “ ’ya’ya,” da abinci mai kyau na ruhaniya. A tsakanin duniya mai lalata, suna adana mizanan Allah mai girma da farin ciki. Kuma Jehovah ya ci gaba da yi musu albarka da ƙari. Sakamakon haka, miliyoyin abokanan tarayyarsu, waɗansu tumaki, “suna bauta masa [Allah] dare da rana.” (Wahayin Yahaya 7:15) Kada mu yi banza da gatarmu ta cin “ ’ya’ya” da kuma rabawa da wasu!
22. Wace albarka ce waɗanda suka karɓi haske suke samu?
22 A wannan mawuyacin lokaci, da duhu ya rufe duniya da kuma baƙin duhu dukan al’ummai, ba ma godiya cewa Jehovah yana ba da haske na ruhaniya bisa mutanensa? (Ishaya 60:2; Romawa 2:19; 13:12) Ga dukan waɗanda suka karɓe shi, irin wannan hasken yana nufin kwanciyar rai da kuma farin ciki da kuma rai madawwami a nan gaba. Da kyakkyawan dalili, mu da muke ƙaunar haske mu ɗaga zukatanmu ga ɗaukaka Jehovah kuma mu ce tare da mai Zabura: “Ubangiji yana kiyaye ni daga dukan hatsari, ba zan ji tsoro ba. Ka dogara ga Ubangiji! Ka yi imani, kada ka karai. Ka dogara ga Ubangiji!”—Zabura 27:1b, 14.
Ka Tuna?
• Wane abu waɗanda suke tsanantawa mutanen Jehovah suke da shi a nan gaba?
• Wane ƙari aka annabta a Ishaya?
• Cikin waɗanne ‘gidaje’ ya kamata mu zauna, kuma me ya sa?
• Me ya sa yanayin mutanen Jehovah yake kawo masa ɗaukaka?
[Akwati a shafi na 32]
SABON LITTAFI
Yawancin abin da aka tattauna a cikin waɗannan talifai biyu an gabatar da su a cikin jawabi a taron gunduma na 2000/2001. A ƙarshen jawabin, an fito da sabuwar littafi, mai suna Isaiah’s Prophecy—Light for All Mankind I. Wannan littafin mai shafuffuka 416 ya tattauna surori 40 na littafin Ishaya aya zuwa aya.
[Hoto a shafi na 28]
Adalai ne kawai za a ƙyale a cikin “birni ƙaƙƙarfa,” ƙungiyar Jehovah
[Hoto a shafi na 29]
Ishaya ya zuba wa Jehovah ido cikin “dare”
[Hoto a shafi na 31]
Jehovah ya tsare “gonarsa ta inabi” kuma ya mai da ita mai ba da ’ya’ya