Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w02 7/1 pp. 26-31
  • Ɗaukakar Jehovah Ta Haskaka Mutanensa

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ɗaukakar Jehovah Ta Haskaka Mutanensa
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2002
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • An Albarkace ta Fiye da Yadda Ake Tsammani
  • Ci Gaba ta Ƙungiya da Aka Tsara
  • Hasken Jehovah Zai Ci Gaba da Haskakawa
  • Ƙaruwar ta Ci Gaba
  • Jehovah Yana Kyawanta Mutanensa Da Haske
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2002
  • “Ƙaramin” Ya Zama “Dubu”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2000
  • Ceto Ga Waɗanda Suka Zaɓi Haske
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2001
  • Amsoshin Tambayoyin Masu Karatu
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2024
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2002
w02 7/1 pp. 26-31

Ɗaukakar Jehovah Ta Haskaka Mutanensa

“Ubangiji za ya zama madawwamin haskenki.”—ISHAYA 60:20.

1. Ta yaya Jehovah ya albarkaci mutanensa masu aminci?

“UBANGIJI ya kan ji daɗin mutanensa: Za ya sa ma masu-tawali’u jamali da ceto.” (Zabura 149:4) Haka mai Zabura na dā ya ce, kuma tarihi ya nuna gaskiyar kalmominsa. Sa’ad da mutanen Jehovah suke da aminci yana kula da su, ya sa su bunƙasa, kuma ya kāre su. A zamanin dā, ya ba su nasara a kan abokan gabansu. A yau, yana ƙarfafa su a ruhaniya kuma ya tabbatar da ceto bisa hadaya ta Yesu. (Romawa 5:9) Ya yi haka domin suna da kyau a idanunsa.

2. Ko da yake ana hamayya da su, wane tabbaci ne mutanen Jehovah suke da shi?

2 Hakika, a duniya da take cikin duhu, waɗanda “su ke so su yi rai mai-ibada” za su sha hamayya. (2 Timothawus 3:12) Duk da haka, Jehovah ya lura da ’yan hamayya, kuma ya yi musu gargaɗi: “Al’umma ko sarauta da ba za ta bauta miki ba, za ta lalace, i waɗannan al’ummai za su risɓe sarai.” (Ishaya 60:12) A yau, hamayya ana yin ta a hanyoyi da yawa. A wasu ƙasashe, ’yan hamayya suna ƙoƙari su rage ko kuma su hana bauta da Kiristoci na gaskiya suke yi wa Jehovah. A wasu, masu zafin kai na addini suna kai wa masu bauta wa Jehovah hari na zahiri kuma suna ƙone kayayyakinsu. Ka tuna, cewa Jehovah ya riga ya ƙaddara sakamakon kowacce hamayya ta cika nufinsa. ’Yan hamayya za su kasa. Waɗanda suke yin yaƙi da Sihiyona, da ’ya’yanta a duniya suke wakiltarta ba za su yi nasara ba. Wannan ba tabbaci ba ne mai ban ƙarfafa daga wajen Allahnmu mai girma, Jehovah?

An Albarkace ta Fiye da Yadda Ake Tsammani

3. Ta yaya aka kwatanta kyau da kuma albarka ta masu bauta wa Jehovah?

3 Hakika a wannan kwanaki na ƙarshe na wannan zamani, Jehovah ya albarkaci mutanensa fiye da yadda suke tsammani. Musamman ya kyawanta wajen bautarsa a hankali da kuma waɗanda suke ciki suke amsa sunansa. In ji annabcin Ishaya, ya ce wa Sihiyona: “Darajar Lebanon za ta zo wurinki, da itacen fir, da pine, da box tare, domin a jamalatarda wurina mai-tsarki; wurin takawar ƙafafuwana kuma zan maishe shi mai-daraja.” (Ishaya 60:13) Duwatsu da itatuwa suka lulluɓe su abin sha’awa ne. Saboda haka, itatuwa alama ne na kyau da kuma albarka na masu bauta wa Jehovah.—Ishaya 41:19; 55:13.

4. Menene “wuri mai-tsarki” da kuma “wurin takawar ƙafafuwan [Jehovah],” kuma ta yaya aka kyawanta waɗannan?

4 Menene “wurina mai-tsarki” da kuma “wurin takawar ƙafafuwan [Jehovah]” da aka ambato a Ishaya 60:13? Waɗannan kalmomin suna nufin farfajiyar haikali na ruhaniya mai girma na Jehovah, wanda tsari ne na zuwa wurin Jehovah cikin bauta ta wajen Yesu Kristi. (Ibraniyawa 8:1-5; 9:2-10, 23) Jehovah ya faɗi nufinsa na ɗaukaka wannan haikali na ruhaniya ta wajen kawo mutane daga dukan al’ummai su zo su yi bauta a ciki. (Haggai 2:7) Da farko, Ishaya kansa ya ga taron mutane daga dukan al’ummai suna rugawa zuwa dutse da aka ɗaukaka na bauta ta Jehovah. (Ishaya 2:1-4) Shekaru da yawa daga baya, manzo Yohanna ya ga a wahayi “taro mai-girma, wanda ba mai-ƙirgawa, daga cikin kowane iri, da dukan ƙabilai da al’ummai da harsuna.” Waɗannan “suna gaban kursiyin Allah; suna yi masa bauta . . . dare da rana cikin haikalinsa.” (Ru’ya ta Yohanna 7:9, 15) Dukan waɗannan annabce-annabce suna cika a zamaninmu, an kyawanta gidan Jehovah a idanunmu.

5. Wace kyautatawa ce ’ya’yan Sihiyona za su fuskanta?

5 Wannan lallai an kyautata wa Sihiyona! Jehovah ya ce: “Inda shi ke a dā an yashe ki, an ƙi, har da babu mutum da ya ratsa ta wurinki, ni sai in maishe ki abu mai-daraja har abada, abin murna ne ga tsararaki dayawa.” (Ishaya 60:15) A wajen ƙarshen yaƙin duniya na farko, hakika “Isra’ila na Allah” ta fuskanci halaka. (Galatiyawa 6:16) Ta ji an “yashe” ta gabaki ɗaya, domin ’ya’yanta a duniya ba su fahimci menene nufin Allah a gare su ba. Sai kuma a shekara ta 1919, Jehovah ya farfaɗo da bayinsa shafaffu, kuma tun daga lokacin ya albarkace su da ci gaba na ban mamaki a ruhaniya. Bugu da ƙari, shin alkawarin da yake cikin wannan ayar ba abin farin ciki ba ne? Jehovah zai ɗauki Sihiyona “abu mai-daraja.” Hakika, ’ya’yan Sihiyona, da kuma Jehovah kansa, za su yi alfahari da Sihiyona. Za ta zama “abin murna” dalilin farin ciki mai yawa. Kuma wannan ba zai kasance kawai na ɗan lokaci ba. Yanayin tagomashi na Sihiyona, kamar yadda ’ya’yanta na duniya suke wakilta, ya kai har zuwa “tsararaki dayawa.” Ba zai taɓa ƙarewa ba.

6. Ta yaya Kiristoci na gaskiya suke amfani da arziki daga al’ummai?

6 Ka saurara yanzu ga wani alkawari na Allah. Da yake magana da Sihiyona, Jehovah ya ce: “Za ki sha nonon al’ummai, ki sha maman sarakuna kuma: za ki sani kuma ni Ubangiji mai-cetonki, mai-fansarki ne, Mai-iko na Yakubu.” (Ishaya 60:16) Ta yaya Sihiyona ta sha “nonon al’ummai” kuma ta tsotsi “maman sarakuna”? Wajen amfani da arzikin al’ummai da Kiristoci shafaffu da kuma abokanansu “waɗansu tumaki” suka yi wajen yaɗa bauta mai tsarki. (Yohanna 10:16) Ba da kyauta ta kuɗi ya sa aikin wa’azi da kuma koyarwa ya yiwu a dukan duniya. Ta wajen amfani da kayayyakin fasaha na zamani an gaggauta buga Littafi Mai Tsarki da kuma littattafai na Littafi Mai Tsarki zuwa harsuna da yawa. A yau, gaskiyar Littafi Mai Tsarki ta kai ga mutane fiye da kowane lokaci a dukan tarihi. Talakawan al’ummai da yawa suna koyon cewa Jehovah, wanda ya fanshi bayinsa shafaffu daga bauta ta ruhaniya, hakika shi ne Mai Ceto.

Ci Gaba ta Ƙungiya da Aka Tsara

7. Wane ci gaba na ban mamaki ne ’ya’yan Sihiyona suka yi?

7 Jehovah ya kyawanta mutanensa a wata hanya. Ya albarkace su da ci gaba ta tsarin ƙungiya. Mun karanta a Ishaya 60:17: “Maimakon janganci zan kawo zinariya, maimakon baƙin ƙarfe kuma in kawo azurfa, maimakon itace kuma janganci, maimakon duwatsu kuma baƙin ƙarfe: zan sa salama ta zama mulkinki, adalci kuma ya zama mahukuncinki.” Sake janganci da zinariya lallai ci gaba ne, kuma haka yake da wasu abubuwa da aka ambata. Cikin jituwa da wannan, Isra’ila ta Allah ta fuskanci wasu tsare-tsare da yake ci gaba a ƙungiya a cikin waɗannan kwanaki na ƙarshe. Ga wasu misalai cikinsu.

8-10. Ka kwatanta wasu ci gaba na tsarin ƙungiya da aka samu tun daga shekara ta 1919.

8 Kafin shekara ta 1919, ikilisiyar mutanen Allah dattawa ne da dikonawa suke shugabancinta, dukansu kuma mutanen ikilisiya ne suke zaɓansu ta hanya ta dimokuraɗiyya. Farawa daga wannan shekarar, “bawan nan mai-aminci mai-hikima” ne yake naɗa mai gudanar da hidima a kowacce ikilisiya ya kula da ayyukan wa’azi na fage. (Matta 24:45-47) Ko da yake, a ikilisiyoyi da yawa wannan tsarin bai yi aiki ba sosai domin wasu dattawa da aka zaɓa ba su ba wa aikin wa’azi cikakken goyon baya ba. Saboda haka, a shekara ta 1932, aka ba da umurni ga ikilisiyoyi su daina zaɓan dattawa da dikonawa. Maimakon haka, su zaɓi mutane da za su yi hidimar kwamitin hidima tare da mai gudanar da hidima. Wannan yana kama ne da “janganci” maimakon “itace”—ci gaba ne sosai!

9 A shekara ta 1938, ikilisiyoyi a dukan duniya suka yarda su karɓi tsari da aka kyautata, wanda ya fi jituwa da tsarin Nassosi. Aka ba da amanar ja-gorar ikilisiya ga bawan rukuni da kuma wasu bayi, dukansu an naɗa su ne a ƙarƙashin ja-gorar bawa mai aminci mai hikima. Babu yin zaɓe kuma! Saboda haka naɗi na ikilisiya ana yinsa ne ta bin tsarin Allah. Wannan kamar “ƙarfe” ne maimakon “duwatsu” ko kuma “zinariya” maimakon “janganci.”

10 Tun daga wannan lokacin ci gaba ta ci gaba. Alal misali, a shekara ta 1972 an ga cewa ikilisiya da rukunin dattawa da aka naɗa su ta wajen tsarin ne ke ja-gorarta, ba tare da wani dattijo da yake da iko bisa wasu ba, ya fi kusa da yadda aka ja-goranci ikilisiya ta ƙarni na farko. Bugu da ƙari, shekara biyu da ta shige, an sake samun wani ci gaba. An yi gyara a tsarin hukumarmu, da ya sa ya yiwu Hukumar Mulki ta mai da hankali sosai bisa ayyukan ruhaniya na mutanen Allah maimakon ayyukan yau da kullum na hukumar ya ɗauke musu hankali.

11. Waye ya kawo canji na tsarin ƙungiya da yake tsakanin mutanen Jehovah, kuma menene waɗannan canje-canje suka kawo?

11 Wanene ya kawo wannan canji mai ci gaba? Babu wani, Jehovah Allah ne. Shi ne ya ce: “Zan kawo zinariya.” (Tafiyar tsutsa tamu ce) Shi ne kuma ya ci gaba da cewa: “Zan sa salama ta zama mulkinki, adalci kuma ya zama mahukuncinki.” (Tafiyar tsutsa tamu ce) Hakika, Jehovah ne yake da hakkin kula da mutanensa. Ya annabta ci gaba na tsarin ƙungiya a wata hanya kuma da yake kyawanta mutanensa. Kuma an albarkaci Shaidun Jehovah a hanyoyi da yawa domin wannan. Mun karanta a Ishaya 60:18: “Ba za a ƙara jin labarin ƙwace a ƙasarki ba, ko risɓewa ko halaka a cikin kan iyakanki: amma za ki kira ganuwarki Ceto, ƙofofinki kuma Yabo.” Lallai waɗannan kalmomi suna da daɗi! Amma ta yaya suka cika?

12. Ta yaya salama ta zo ta yi sarauta a tsakanin Kiristoci na gaskiya?

12 Kiristoci na gaskiya suna zuba wa Jehovah ne ido domin umurni da kuma ja-gora, kuma Ishaya ya faɗi sakamakon haka: “Dukan ’ya’yanki kuma za su zama masu-koyi na Ubangiji: lafiyar ’ya’yanki kuma mai-girma ce.” (Ishaya 54:13) Bugu da ƙari, ruhun Jehovah yana aiki a kan mutanensa, kuma ɓangaren ’ya’yan ruhun shi ne salama. (Galatiyawa 5:22, 23) Salamar mutanen Jehovah ya mai da su wurin wartsakewa daga wannan muguwar duniya. Yanayin salama, da ya kasance domin ƙauna da Kiristoci na gaskiya suke da shi ga junansu, alama ce ta rayuwar sabuwar duniya. (Yohanna 15:17; Kolossiyawa 3:14) Babu shakka kowannenmu yana sha’awar more wannan kuma yana ƙara ga wannan salama, wadda take kawo yabo da daraja ga Allahnmu wadda ɓangare na musamman ne na aljannarmu ta ruhaniya!—Ishaya 11:9.

Hasken Jehovah Zai Ci Gaba da Haskakawa

13. Me ya sa za mu tabbata cewa hasken Jehovah ba zai taɓa daina haskakawa a kan mutanensa ba?

13 Hasken Jehovah zai ci gaba da haskakawa kuma a kan mutanensa? E! Mun karanta a Ishaya 60:19, 20: “Rana ba za ta ƙara zama haskenki a yini ba: don annuri kuma wata ba za ya ƙara ba ki haske ba: amma Ubangiji za ya zama madawwamin haskenki, Allahnki kuma darajarki. Ranarki ba za ta sāke fāɗuwa ba, watanki kuma ba za ya shuɗe ba: gama Ubangiji za ya zama madawwamin haskenki, kwanakin makokinki kuma za su ƙare.” Da zarar “makokin” waɗanda suke bauta ta ruhaniya ya ƙare a shekara ta 1919, hasken Jehovah ya fara haskaka su. Fiye da shekara 80 daga baya, suna more tagomashin Jehovah da hasken ya ci gaba da haskakawa. Kuma ba zai tsaya ba. Game da masu bauta masa, Allahnmu ba zai ‘faɗi ba’ kamar rana ko kuma “shuɗe” kamar wata. Maimakon haka, zai haskaka su har abada abadin. Hakika wannan tabbaci ne mai ban sha’awa dominmu da muke rayuwa a kwanaki na ƙarshe na wannan duniya mai duhu!

14, 15. (a) A wace hanya ce dukan mutanen Allah “masu-adalci” ne? (b) Bisa ga Ishaya 60:21, wace cika ce mai muhimmanci waɗansu tumaki suke sauraro?

14 Ka saurara yanzu ga wani alkawari da Jehovah ya yi game da wakilan Sihiyona na duniya, Isra’ila ta Allah. Ishaya 60:21 ta ce: “Mutanenki duka kuma za su zama masu-adalci; za su gāji ƙasar har abada; reshen da ni na dasa ke nan, aikin hannuwana, domin in ɗaukaka.” A shekara ta 1919 sa’ad da aka mai da Kiristoci shafaffu bakin aikinsu, sun kasance rukunin mutane ne da suka bambanta. A cikin duniya da yake cike da zunubi, an ce da su “masu-adalci” domin bangaskiyarsu marar jijjiga a kan hadayar fansa na Kristi Yesu. (Romawa 3:24; 5:1) Kamar waɗannan Isra’ilawa da aka sake daga bauta a Babila, suka mallaki “ƙasar,” ƙasa ta ruhaniya, ko kuma duniya ta ayyuka, wadda a cikinta suka more aljanna ta ruhaniya. (Ishaya 66:8) Kyau na wannan Aljanna ba zai taɓa ƙarewa ba domin ba kamar Isra’ila ta dā ba, Isra’ila ta Allah al’umma ce da ba za ta yi rashin aminci ba. Bangaskiyarsu, da jimirinsu, da kuma himmarsu ba za su taɓa ƙarewa ba wajen daraja sunan Allah.

15 Dukan waɗanda suke cikin wannan al’umma ta ruhaniya sun shiga cikin sabon alkawari. Dukansu suna da dokokin Jehovah da suke rubuce cikin zukatansu, kuma Jehovah, a kan hadayar fansa ta Yesu, ya gafarta musu zunubansu. (Irmiya 31:31-34) Ya ce da su masu adalci “ ’ya’ya,” kuma yana sha’ani da su kamar dai kamiltattu ne. (Romawa 8:15, 16, 29, 30) Kuma abokanansu waɗansu tumaki su ma an gafarta musu zunubansu a kan hadayar fansa ta Yesu, kamar Ibrahim, an ce da su masu adalci abokanan Allah domin bangaskiya. “Suka wanke rigunansu, suka faranta su cikin jinin Ɗan ragon kuma.” Waɗannan waɗansu tumaki suna sauraron wata albarka kuma ta musamman. Bayan sun tsira daga “ƙunci mai-girma” ko kuma bayan an ta da su daga matattu, za su ga cika ta zahiri na kalmomin Ishaya 60:21 sa’ad da dukan duniya za ta zama aljanna. (Ru’ya ta Yohanna 7:14; Romawa 4:1-3) A wannan lokacin, “masu-tawali’u za su gāji ƙasan; za su faranta zuciyarsu kuma cikin yalwar salama.”—Zabura 37:11, 29.

Ƙaruwar ta Ci Gaba

16. Wane alkawari mai ban sha’awa Jehovah ya yi, kuma ta yaya wannan ya cika?

16 A aya ta ƙarshe ta Ishaya 60, mun karanta alkawarin Jehovah na ƙarshe a wannan surar. Ya ce wa Sihiyona: “Ƙaramin za ya zama dubu, ƙanƙanin kuma za ya zama al’umma mai-ƙarfi: ni, Ubangiji, zan hanzarta wannan a lotonsa.” (Ishaya 60:22) A zamaninmu, Jehovah ya cika alkawarinsa. Sa’ad da aka maido da Kiristoci a kan aikinsu a shekara ta 1919, adadinsu kaɗan ne—hakika, “ƙarami” ne. Adadinsu ya ƙaru sa’ad da aka ƙaro Isra’ilawa ta ruhaniya. Sai kuma waɗansu tumaki suka fara rugowa wurinsu sai adadin ya ƙaru. Yanayin salama na mutanen Allah, da aljanna ta ruhaniya da ta wanzu a “ƙasa” tasu, ta jawo mutane masu zukatan kirki kuma “ƙanƙanin” hakika ya zama “al’umma mai-ƙarfi.” A yanzu wannan “al’ummar”—Isra’ila ta Allah da kuma “baƙi” da suka keɓe kai waɗanda suka fi miliyan shida—sun fi ƙasashe da yawa na duniya yawa. (Ishaya 60:10) Dukan talakawanta suna saka hannu wajen haskaka hasken Jehovah, kuma wannan yana kyawanta su duka a idanunsa.

17. Ta yaya tattauna wannan sura ta 60 ta Ishaya ta shafe ka?

17 Hakika, yana ba da ƙarfafa a bincika ainihin darussa na Ishaya sura 60. Yana ƙarfafa mu mu gani cewa Jehovah ya sani tun da farko cewa mutanensa za su je bauta ta ruhaniya kuma zai maido su. Yana ba mu mamaki mu ga cewa Jehovah ya riga ya ga cewa za ya samu ƙaruwa na masu bauta ta gaskiya a kwanaki na ƙarshe. Bugu da ƙari, yana da ban ƙarfafa mu tuna cewa Jehovah ba zai yashe mu ba! Lallai tabbaci ne na ƙauna cewa ƙofofin “birnin” za su kasance a buɗe ko da yaushe su marabci waɗanda “aka ƙaddara su ga rai na har abada”! (Ayukan Manzanni 13:48) Jehovah zai ci gaba da haskakawa a kan mutanensa. Sihiyona za ta ci gaba da kasancewa abin alfahari sa’ad da ’ya’yanta suka ci gaba da haskaka haske. (Matta 5:16) Hakika mun ƙudiri aniya fiye da dā mu kusaci Isra’ila ta Allah kuma mu ɗaukaka gatar da muke da ita na haskaka hasken Jehovah!

Za Ka Iya Bayyanawa?

• Game da hamayya, tabbacin me muke da shi?

• Ta yaya ’ya’yan Sihiyona suka ‘sha nonon al’ummai’?

• A waɗanne hanyoyi ne Jehovah ya kawo “janganci” maimakon “duwatsu”?

• Waɗanne halaye biyu ne aka nanata a Ishaya 60:17, 21?

• Ta yaya “ƙanƙanin” ya zama “al’umma mai-ƙarfi”?

[Box/Hotuna a shafi na 30]

ANNABCIN ISHAYA—Haske ga Dukan ’Yan Adam

Darussan waɗannan talifofi an gabatar da su a wani tattaunawa a lokacin Taron Gunduma na “Masu Koyar da Kalmar Allah” na shekara ta 2001/2002. A ƙarshen jawabin, a yawancin wurare mai jawabin ya fito da sabon littafi mai suna Isaiah’s Prophecy—Light for All Mankind, Littafi na Biyu. A shekarar da ta gabata an riga an fito da Isaiah’s Prophecy—Light for All Mankind, Littafi na Ɗaya. Da fitowar wannan sabon littafi, yanzu akwai bayani a kan kusan kowacce aya da take cikin littafin Ishaya. Waɗannan Littattafai sun kasance da taimako wajen zurfafa fahimtarmu da kuma godiyarmu ga annabci mai ƙarfafawa na littafin Ishaya.

[Hotuna a shafi na 27]

A lokacin hamayya mai tsanani, ‘Jehovah ya kyawanta mutanensa da ceto’

[Hotuna a shafi na 28]

Mutanen Allah suna amfani da arziki daga al’ummai wajen yaɗa tsarkakar bauta

[Hoto a shafi na 29]

Jehovah ya albarkaci mutanensa da bunƙasa ta tsarin ƙungiya da kuma salama

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba