“Ƙaramin” Ya Zama “Dubu”
“Ƙaramin za ya zama dubu, ƙanƙanin kuma za ya zama al’umma mai-ƙarfi.”—ISHAYA 60:22.
1, 2. (a) Me ya sa duhu ya rufe duniya a yau? (b) Ta yaya hasken Jehovah ya haskaka mutanensa a hankali?
“DUHU za ya rufe duniya, baƙin duhu kuma za ya rufe al’ummai: amma Ubangiji za ya tashi a bisa kanki, za a ga darajassa kuma a bisa kanki.” (Ishaya 60:2) Waɗannan kalmomin sun kwatanta yanayin duniya tun daga 1919. Kiristendom sun ƙi alamar bayyanuwar sarauta ta Yesu Kristi “hasken duniya.” (Yohanna 8:12; Matta 24:3) Domin “hasala mai-girma” ta Shaitan, shugaban “mahukumtan wannan zamani mai-duhu,” ƙarni na 20 ya fi mugunta, ya fi hallaka mutane a duk tarihin bil Adam. (Ru’ya ta Yohanna 12:12; Afisawa 6:12) Yawancin mutane suna zama cikin duhu ta ruhaniya.
2 Duk da haka, haske ya haskaka a yau. Jehovah ‘ya haskaka’ bisa bayinsa, ringin shafaffun, waɗanda suna wakilta ‘macensa’ ta samaniya a nan duniya. (Ishaya 60:1) Musamman ma tun da aka sake su daga tsari na Babila a 1919, waɗannan sun nuna ɗaukakar Allah sun ‘bari haskensu ya haskaka a gaban mutane.’ (Matta 5:16) Daga 1919 zuwa 1931, hasken Mulki ya haskaka sosai sosai yayinda waɗannan suka kawar da mari na tunanin Babila. Adadinsu ya ƙaru zuwa dubbai yayinda Jehovah ya cika alkawarinsa: “Lallai zan tattara ringin Isra’ila; zan harhaɗa su kamar tumakin Bozrah; kamar garke cikin tsakiyar makiyayarsu, za su yi babban ɗumi sabada yawan taro.” (Mikah 2:12) A 1931, ɗaukakar Jehovah bisa mutanensa ta tabbata sosai lokacin da suka karɓi sunan nan Shaidun Jehovah.—Ishaya 43:10, 12.
3. Ta yaya ya tabbata cewa hasken Jehovah zai haskaka wasu ban da shafaffu?
3 Jehovah zai haskaka bisa ringin “ƙaramin garke” ne kawai? (Luka 12:32) A’a. Fitar Hasumiyar Tsaro ta 1 ga Satumba, 1931 (Turanci), ta nuna wani rukuni. A cikin bayani mai kyau na Ezekiel 9:1-11, ya nuna cewa mutum da ya rataye gafaka ta tawada da aka ambata a waɗannan ayoyin yana nufin ringin shafaffu ne. Su waye wancan “mutum” ya yi masu alama a goshinsu? “Waɗansu tumaki,” waɗanda suke da begen rayuwa har abada a aljanna a duniya. (Yohanna 10:16; Zabura 37:29) A 1935 aka gano cewa wannan rukuni na “waɗansu tumaki” shine ‘taro mai-girma . . . daga dukan al’ummai’ wanda manzo Yohanna ya gani a cikin wahayi. (Ru’ya ta Yohanna 7:9-14) Daga 1935 har wa yau, an mai da hankali sosai ga tattara taro mai-girma ɗin.
4. Su wanene “sarakuna” da kuma “al’ummai” da Ishaya 60:3 ya nuna?
4 Wannan aikin tattarawa ya yi nuni ne ga annabcin Ishaya lokacin da ya ce: “Al’ummai za su zo wurin haskenki, sarakuna kuma wurin hasken tāshinki.” (Ishaya 60:3) Su wanene ne “sarakuna” da ake nufi a nan? Ringin 144,000 waɗanda, tare da Yesu Kristi, suna tarayyar gadō na Mulkin sama kuma suke ja-gora a aikin wa’azi. (Romawa 8:17; Ru’ya ta Yohanna 12:17; 14:1) A yau, dubbai kalilan na ringin shafaffu da suka rage, “al’ummai” waɗanda suke da begen mallakar duniya da suka zo ga Jehovah don koyarwa kuma suka gayyace wasu su yi hakan sun fi su yawa sosai.—Ishaya 2:3.
Bayin Jehovah Masu Himma
5. (a) Wace gaskiya ce ta nuna cewa himmar Shaidun Jehovah ba ta ragu ba? (b) Waɗanne ƙasashe ne suke da ƙari mafi yawa a 1999? (Duba taswira da take shafofi 17-20.)
5 Shaidun Jehovah na zamani sun nuna himma ƙwarai duk cikin ƙarni na 20! Kuma duk da ƙarin matsa masu da ake yi, himmarsu ba ta ragu ba da shekara ta 2000 take dosowa. Har yanzu sun ɗauki umurnin Yesu da muhimmanci: “Ku almajirtadda dukan al’ummai.” (Matta 28:19, 20) Adadin masu shelar bishara masu ƙwazo a shekarar hidima ta ƙarshen ƙarni na 20 ya kai sabon ƙoli na 5,912,492. Sun ɓad da adadin sa’o’i 1,144,566,849 na musamman suna yi ma wasu magana game da Allah da kuma ƙudurinsa. Sun ziyarci mutane masu marmari 420,047,796 kuma sun yi nazarin 4,433,884 na Littafi Mai-Tsarki na kyauta a gidaje. Lallai rahoto ne na hidima da himma ƙwarai!
6. Wane sabon tsari ne aka yi wa majagaba, kuma yaya aka ɗauke wannan?
6 A Janairu na bara, Hukumar Mulki sun sanar da rage sa’o’i da ake bukata daga majagaba. Da yawa sun yi amfani da wannan zarafin wurin shiga aikin majagaba na kullum ko kuma na ɗan lokaci. Alal misali, cikin watanni huɗu na farko na 1999, reshen Netherlands sun sami ƙarin waɗanda suke so su shiga aikin majagaba na kullum ninki huɗu fiye da na daidai lokacin a waccan bara. Ghana ta bada rahoto: “Tun da sabon yawan sa’o’i da ake bukata daga majagaba ya fara aiki, yawan majagabanmu ya ci gaba da ƙaruwa.” A shekarar hidima ta 1999, adadin majagaba a dukan duniya ya kai 738,343—kyakkyawar misali na ‘himmar nagargarun ayyuka.’—Titus 2:14.
7. Ta yaya Jehovah ya albarkaci hidimar bayinsa da himma?
7 Jehovah ya albarkaci wannan himmar kuwa? I. Ta bakin Ishaya ya ce: “Tada idanunki ki duba ko’ina, ki gani: dukansu suna tattaruwa, suna zuwa wurinki: ’ya’yanki maza daga nesa za su tafo, ’ya’yanki mata kuma za a zo da su a goye.” (Ishaya 60:4) “ ’Ya’ya maza” da “mata” shafaffu waɗanda aka tattara su ciki har yanzu suna bauta wa Allah da himma. Kuma yanzu, waɗansu tumaki na Yesu ana tattara su zuwa gefen ’ya’ya maza da mata shafaffu na Jehovah a ƙasashe 234 da kuma tsibirai na teku.
“Kowane Managarcin Aiki”
8. A waɗanne ‘nagargarun ayyuka’ ne Shaidun Jehovah suke da ƙwazo?
8 Kiristoci suna da nawayar yin shelar bisharar Mulki da kuma su taimaki masu marmari su zama almajirai. Amma suna ‘shirye sarai domin kowane managarcin aiki.’ (2 Timothawus 3:17) Saboda haka, suna kula da iyalansu cikin ƙauna, suna nuna baƙonci, kuma suna ziyartan majiyyata. (1 Timothawus 5:8; Ibraniyawa 13:16) Kuma ayyukan gine-gine kamar na su Majami’ar Mulki ya ƙunshi masu bada kai—aiki da shi ma yake bada shaida. A Togo, bayan an gina wata majami’a, manyan ’yan cocin charismatic suna son su san dalilin da ya sa Shaidun Jehovah suke iya yin gine-gine da kansu yayinda kuma cocin sai ya yi hayar mutane don yin haka! Togo ya bada rahoton cewa gina Majami’ar Mulki masu kyau ya taimake waɗanda suke yankin har ya sa wasu mutane sun yi ƙoƙarin hayar gidaje ko kuma gina gidaje a inda ake so a gina majami’un.
9. Yaya Shaidun Jehovah suke yi lokacin da bala’i ya auku?
9 Wasu lokutta, ana bukatar wani irin nagarin aiki. Bala’i ya faɗā wa ƙasashe da yawa a cikin shekararhidima da ta shige, kuma sau da yawa Shaidun Jehovah ne suke zuwa da farko don su bada taimako. Alal misali, Hadari Mai-Ƙarfi ya hallaka wurare da yawa a Honduras. Da hanzari, reshen ya kafa kwamitin gaggawa su tsara kayan agaji. Shaidun na Honduras da kuma wasu ƙasashe da yawa suka bayar da sutura, abinci, magunguna, da wasu muhimman abubuwa. Kwamitin Gine-Gine na Yanki suka yi amfani da iyawarsu suka sake gina gidajen. Bada jimawa ba, yan’uwanmu waɗanda bala’i ya faɗa masu aka taimake su suka koma ayyukansu na kullum. A Ecuador, Shaidun Jehovah sun taimaki yan’uwansu lokacin da ambaliya ta hallaka wasu gidaje. Bayan da ya ga hanya mai kyau da suka yi amfani da ita wurin magance yanayin, wani ma’aikacin gwamnati ya ce: “Idan ina da wannan rukunin, zan yi abin mamaki! Ya kamata mutane irinku suna dukan ɓangarorin duniya.” Irin wannan nagarin aiki yana kawo yabo ga Jehovah Allah kuma tabbaci ne na ‘ibadarmu wadda tana da amfani ga dukan abu.’—1 Timothawus 4:8.
Sun Zo Suna “Tashi Kamar Cincirindo”
10. Duk da raguwan adadin shafaffu, me ya sa ake sanar da sunan Jehovah fiye da dā?
10 Sai Jehovah ya yi tambaya: “Su wanene waɗannan masu-tashi kamar cincirindo, kamar tantabaru kuma zuwa sakatansu? Babu shakka tsibirai za su saurara mani, jiragen Tarshish kuma su ne gaba, domin a ɗauki ’ya’yanki daga nesa . . . Baƙi kuma za su gina ganuwarki, sarakunansu kuma za su hidimce ki.” (Ishaya 60:8-10) Waɗanda suka fara juyawa ga ‘hasken’ Jehovah ‘ ’ya’yansa’ ne Kiristoci shafaffu. Sai kuma “baƙi,” taro mai-girma, waɗanda suka yi hidima da biyayya ga yan’uwansu shafaffu, suna bin ja-gorancinsu a yin wa’azin bisharar. Saboda haka, ko da yake adadin shafaffu yana raguwa, ana sanar da sunan Jehovah a duk faɗin duniya fiye da dā.
11. (a) Menene har yanzu yake ci gaba kuma da wane sakamako a 1999? (b) Waɗanne ƙasashe ne suke da waɗanda suka yi baftisma da suka fi yawa a 1999? (Duba taswira da take shafofi 17-20.)
11 Sakamakon haka, miliyoyin mutane suna tattaruwa “kamar tantabaru kuma zuwa sakatansu,” suna samun mafaka cikin ikklisiyar Kirista. Kowace shekara ana daɗa mutane dubbai ɗarurruwa, kuma hanyar tana buɗe har ila ga wasu da yawa. Ishaya ya ce: “Ƙofofinki kuma za su kasance a buɗe tuttur: ko da dare, ko da rana ba za a rufe su ba; domin mutane su kawo maki wadatar al’ummai.” (Ishaya 60:11) A bara an yi ma mutane 323,439 baftisma a alamar keɓe kansu ga Jehovah, kuma har yanzu bai rufe ƙofa ba tukuna. “Muraɗin dukan dangogi” waɗanda suke cikin taro mai-girma, har yanzu suna taruwa ta hannunsu. (Haggai 2:7) Ba wanda yake so ya bar duhu da aka kora. (Yohanna 12:46) Bari dukan waɗannan kada su bar ƙaunarsu ga haske!
Rashin Tsoro a Fuskar Hamayya
12. Ta yaya waɗanda suke ƙaunar duhu suka yi ƙoƙari su kashe haske?
12 Waɗanda suke ƙaunar duhu sun ƙi hasken Jehovah. (Yohanna 3:19) Wasu suna so ma su kashe wannan haske. Wannan ba abu ba ne da ba a tsammani. Har Yesu, “haske mai-gaskiya wanda yana haskaka kowane mutum,” an yi masa ba’a, an yi masa hamayya, a ƙarshe kuma mutanen ƙasarsa suka kashe shi. (Yohanna 1:9) Cikin dukan ƙarni na 20, Shaidun Jehovah ma an yi masu ba’a, tsare su a fursuna, hana su aiki, har ma an kashe su da suke nuna hasken Jehovah da aminci. A shekaru na baya bayan nan, ’yan hamayya sun juya ga yaɗa ƙarya ta hanyar labarai game da waɗanda suke nuna haske na Allah. Wasu suna so su sa mutane su yarda cewa Shaidun Jehovah mugaye ne kuma ya kamata a hana su aiki ko kuma a kawar da su. Waɗannan ’yan hamayya sun yi nasara ne?
13. Menene sakamakon gabatar da gaskiya da hikima na aikinmu ta hanyar yaɗa labarai?
13 A’a. A inda ya dace, Shaidun Jehovah sun je gidan yaɗa labarai su bayyana gaskiya. Sakamakon haka, an sanar da sunan Jehovah sosai a jaridu da yawa da mujallu da kuma a rediyo da telibijin. Wannan yana da sakamako mai kyau ga aikin wa’azi. Alal misali, a Denmark gidan TV na tarayya ya yi magana akan wannan batu “Me ya sa imanin mutanen Denmark, yake raguwa.” Tare da wakilan wasu addinai, an yi wa Shaidun Jehovah tambayoyi. Bayan haka, wata mace da ta kalli zancen ta faɗi albarkacin bakinta: “Waɗanda suke da ruhun Allah sun fita sarai.” Aka fara nazari da ita.
14. Ga wulakancinsu, menene ’yan hamayya bada jimawa ba za a tilasta masu su gane?
14 Shaidun Jehovah sun sani cewa da yawa cikin duniyar nan za su yi hamayya da su. (Yohanna 17:14) Amma, annabcin Ishaya yana ƙarfafa su: “ ’Ya’yan waɗanda suka wulakance ki za su zo wurinki a rusune; dukan waɗanda suka rena ki kuma za su rusuna a gaban tāfin sawunki; za su ce da ke, Birnin Ubangiji, Sihiyona ta Mai-tsarki na Isra’ila.” (Ishaya 60:14) Ga wulakancinsu, bada jimawa ba ’yan hamayya za su fahimci cewa, ashe su da Allah kansa suke yaƙi. Wa zai ci nasara a irin wannan yaƙin?
15. Ta yaya Shaidun Jehovah suka “sha nonon al’ummai,” kuma ta yaya wannan ta bayyana a aikinsu na koyarwa da kuma wa’azi?
15 Jehovah ya ci gaba da alkawari: “Ni sai in maishe ki abu mai-daraja har abada . . . Za ki sha nonon al’ummai, ki sha maman sarakuna kuma: za ki sani kuma ni Ubangiji mai-cetonki.” (Ishaya 60:15, 16) I, Jehovah shine Mai-Ceton mutanensa. Idan suka dogara gareshi za su rayu “har abada.” Kuma za su “sha nonon al’ummai,” suna yin amfani da wasu arziki da suke akwai wajen faɗaɗa sujada ta gaskiya. Alal misali, yin amfani da na’ura mai ƙwaƙwalwa da hikima da kuma wasu hanyoyin sadarwa na fasaha ya gaugauta buga Hasumiyar Tsaro a cikin harsuna 121 sau biyu a wata da kuma Awake! a cikin harsuna 62. An ƙirƙiro wata takamaiman hanyar wayar na’ura mai ƙwaƙwalwa don ta taimaka wajen juya New World Translation zuwa sabobin harsuna, kuma irin wannan juyin yana kawo farinciki sosai. Lokacin da aka fitar da Nassosin Hellenanci na Kirista a Croatiyanci a 1999, dubbai sun zub da hawayen murna. Wani ɗan’uwa tsoho ya ce: “Na jira wannan Littafi Mai-Tsarki na dogon lokaci. Yanzu zan iya mutuwa cikin salama!” New World Translation, a gabaɗayansa ko ɓarinsa ya fi miliyan 100 da aka bayar a cikin harsuna 34.
Mizanan Ɗabi’a Masu Girma
16, 17. (a) Ko da yake yana da wuya, me ya sa yake da muhimmanci mu riƙe mizanai masu girma na Jehovah? (b) Wane labari ne ya bada misalin cewa matasa za su iya ƙin gurɓatuwa da duniyar nan?
16 Yesu ya ce: “Kowanene wanda ya ke aika mugunta ƙin haske ya ke yi.” (Yohanna 3:20) A wata sassa, waɗanda suka manne ma haske suna ƙaunar mizanan ɗabi’u masu girma na Jehovah. Ta hannun Ishaya, Jehovah ya ce: “Mutanenki duka kuma za su zama masu adilci.” (Ishaya 60:21a) Kalubale ne a riƙe mizanai masu adilci a cikin duniya lalata ta jima’i, ƙarya, ƙwaɗayi, da fariya da take ko’ina. Alal misali, a wasu ƙasashe, arzikin ƙasa yana tashi kuma yana da sauƙi ya kwashe hankalin mutum zuwa biɗan arziki. Amma dai, Bulus ya yi kashedi: “Waɗanda suna so su zama mawadata su kan fāɗa cikin jaraba da tarko da sha’awoyi dayawa na wauta da ɓarna, irin da kan dulmaya mutane cikin hallaka da lalacewa.” (1 Timothawus 6:9) Lallai yana da muni idan wani ya duƙufa cikin hada hadar kasuwanci har ya sadakar da abubuwa masu muhimmanci, kamar su cuɗanyar Kiristoci, sujada, ƙa’idodin ɗabi’a, da nawayarsa na iyali!
17 Riƙe mizanai masu adilci za su yi wuya musamman ma ga matasa, yayinda da yawa cikin tsaransu suna shan miyagun ƙwayoyi da yin lalata. A Suriname, wani kyakkyawan yaro ya nemi wata yarinya ’yar shekara 14 a makaranta, ya gayyace ta ya yi jima’i da ita. Ta ƙi ta yarda, ta yi masa bayani cewa Littafi Mai-Tsarki ya hana hakan ga waɗanda ba su yi aure ba. Wasu ’yammata a makaranta suka yi mata ba’a kuma suka yi ƙoƙarin su matsa mata ta canja ra’ayinta, suka ce kowace yarinya tana so wannan yaro ya kwana da ita. Amma dai, ƙaramar yarinyar ta ƙi yarda. Makonni ƙaɗan bayan haka, aka auna yaron yana da HIV (ƙwayoyin cuta mai karya garkuwar jiki) kuma ya yi ciwo sosai. Yarinyar ta yi farinciki cewa ta yi biyayya ga umurnin Jehovah ‘ku hanu daga fasikanci.’ (Ayukan Manzanni 15:28, 29) Shaidun Jehovah suna alfahari da matasansu waɗanda suka dage bisa abin da yake nagari. Imaninsu, da kuma na iyayensu yana, ‘kyauwanta’—kawo daraja ga—sunan Jehovah Allah.—Ishaya 60:21b.
Jehovah Ya Bayar da Ƙari
18. (a) Wane abu ne mai girma Jehovah ya yi wa mutanensa? (b) Wane tabbaci ne da akwai cewa ƙarin zai ci gaba, kuma wane abu ne yake jiran waɗanda suka tsaya ga haske?
18 I, Jehovah ya bada haske akan mutanensa, ya albarkace su, ya ja-gorance su, ya kuma ƙarfafa su. A cikin ƙarni na 20, sun ga cikar kalmomin Ishaya: “Ƙaramin za ya zama dubu, ƙanƙanin kuma za ya zama al’umma mai-ƙarfi: ni, Ubangiji, zan hanzarta wannan a lotonsa.” (Ishaya 60:22) Da gaske, daga ɗan kaɗan a 1919, “ƙaramin” ya zama fiye da “dubu.” Kuma ƙarshen wannan girma bai ƙare ba tukuna! A shekara da ta gabata mutane 14,088,751 suka halarci bikin Abin Tuni na mutuwar Yesu. Da yawa cikin waɗannan ba Shaidu ba ne masu ƙwazo. Mun yi farinciki cewa sun halarci bikin nan mai muhimmanci, kuma mun gayyace su su ci gaba da matsowa ga haske. Har yanzu Jehovah yana bada haske ga mutanensa. Ƙofar ƙungiyarsa har yanzu tana buɗe. Bari kowa, ya ƙuduri aniyar tsayawa ga hasken Jehovah. Lallai wannan ya zama mana albarka yanzu! Kuma wannan zai kawo murna a nan gaba lokacin da dukan halitta za su yaba wa Jehovah kuma su yi murna cikin hasken ɗaukakarsa!—Ru’ya ta Yohanna 5:13, 14.
Za Ka Iya Bayyanawa?
• Su wanene suka nuna darajar Jehovah a waɗannan kwanakin ƙarshe?
• Menene ya nuna cewa himmar mutanen Jehovah bai ragu ba?
• A wane nagargarun ayyuka ne Shaidun Jehovah suke shagala?
• Duk da hamayya mai ƙarfi, ga me muke da tabbaci?
[Hotuna a shafi na 26]
Mutane har yanzu suna tattaruwa zuwa ƙungiyar Jehovah
[Hoto a shafi na 31]
Muna farincikin cewa Jehovah ya bar ƙofar a buɗe da faɗi ga waɗanda suke ƙaunar haske