Murna Ga Waɗanda Suke Tafiya Cikin Haske
“Bari mu yi tafiya a cikin hasken da Ubangiji ya ba mu!”—ISHAYA 2:5.
1, 2. (a) Yaya muhimmancin haske yake? (b) Me ya sa gargaɗin cewa duhu zai rufe duniya yake da tsanani ƙwarai?
JEHOVAH ne Tushen haske. Littafi Mai Tsarki ya kira shi “wanda ya ba da rana ta haskaka yini, Ya sa wata da taurari su ba da haske da dare.” (Irmiya 31:35; Zabura 8:3) Shi ne ya halicci rana tamu, wadda tanderu ce ta nukiliya wadda take fid da zafi ƙwarai, wasu haske ne wasu kuma zafi. Kaɗan daga cikin zafinta yake isa wurin mu yayin da hasken rana yake raya rai a duniya. Idan ba tare da hasken rana ba, ba za mu rayu ba. Duniya za ta kasance babu rai cikinta.
2 Da wannan a zuci, za mu fahimci muhimmancin yanayi da annabi Ishaya ya kwatanta. Ya ce: “Duhu zai rufe sauran al’umma.” (Ishaya 60:2) Hakika, wannan ba ya nufin duhu na zahiri. Ishaya bai nufa cewa wata rana, rana, wata, da taurari za su daina haskakawa ba. (Zabura 89:36, 37; 136:7-9) Maimako, yana magana ne game da duhu na ruhaniya. Amma duhu na ruhaniya yana da haɗari ƙwarai. A ƙarshe, ba za mu iya rayuwa ba ba tare da haske na ruhaniya ba kamar yadda ba za mu iya rayuwa ba tare da haske na zahiri ba.—Luka 1:79.
3. Saboda maganar Ishaya, menene ya kamata Kiristoci su yi?
3 Saboda wannan, abin da za a damu da shi shi ne a kula da kalmomin Ishaya, ko da yake ya cika a kan Yahuza ta dā, suna samun cika mafi girma a yau. Hakika, a lokacinmu duniya tana lulluɓe cikin duhu na ruhaniya. A cikin irin wannan mummunan yanayi, haske na ruhaniya yana da muhimmanci sosai da sosai. Saboda wannan ne Kiristoci ya kamata su yi ƙoƙari su bi gargaɗin Yesu: “Haskenku ya riƙa haskakawa haka a gaban mutane.” (Matiyu 5:16) Amintattu Kiristoci za su iya su haskaka cikin duhu domin masu tawali’u, ta haka suna ba su damar samun rai.—Yahaya 8:12.
Lokatai Masu Duhu a Isra’ila
4. Yaushe ne cikar farko na kalmomin annabci na Ishaya, amma wane yanayi ya kasance a nasa zamanin?
4 Kalmomin Ishaya game da duhu da zai rufe duniya sun cika da farko lokacin da Yahuza ta halaka kuma aka kwashi mutanenta zuwa hijira a Babila. Kafin wannan lokacin ma, a zamanin Ishaya da yawa cikin al’ummar suna lulluɓe cikin duhu, abin da ya sa ya aririci mutanen ƙasarsa: “Yanzu fa, zuriyar Yakubu, bari mu yi tafiya a cikin hasken da Ubangiji ya ba mu!”—Ishaya 2:5; 5:20.
5, 6. Waɗanne abubuwa ne suka ƙara ga duhun zamanin Ishaya?
5 Ishaya ya yi annabcinsa a Yahuza “a zamanin da Azariya, da Yotam, da Ahaz, da Hezekiya, suka yi sarautar Yahuza.” (Ishaya 1:1) Lokaci ne na hargitsin siyasa, da riyya ta addini, da rashawa wajen hukunci, da kuma zaluntar matalauta. Har a lokacin sarautar sarakuna masu aminci ma, kamar su Yotam, ana ganin bagadodin allolin ƙarya a kan tuddai. A ƙarƙashin sarakuna marasa aminci, yanayi sai ya ƙara muni. Mugun Sarki Ahaz, alal misali, har ya kai ga ba da hadayar ɗansa ga allahn Molek. Wannan duhu ne ƙwarai!—2 Sarakuna 15:32-34; 16:2-4.
6 Yanayin duniya duka a duhunce yake. Mowab, Edom, da kuma Filistiya suna nan a kan iyakar Yahuza abin tsoro. Sarautar arewa ta Isra’ila ko da yake jini ya haɗa su ta zama abokiyar gaba. Can nesa daga arewa, Suriya tana yi wa salama ta Yahuza burga. Wanda ma ta fi muni ita ce muguwa Assuriya, kullayaumi tana neman zarafi ta yaɗa ikonta. A lokacin annabcin Ishaya, Assuriya ta ci Isra’ila har ma ta yi kusa ta halaka Yahuza. A wani lokaci, Assuriya ta ci dukan biranen Yahuza, Urushalima ce kaɗai ta gagara.—Ishaya 1:7, 8; 36:1.
7. Wane tafarki Isra’ila da Yahuza suka zaɓa, kuma me Jehovah ya yi?
7 Mutanen alkawari na Allah sun fuskanci irin wannan bala’i domin Isra’ila da Yahuza sun yi rashin aminci gare shi. Kamar waɗanda aka ambata a littafin Karin Magana suka bar “zaman adalci don su zauna cikin duhun.” (Karin Magana 2:13) Duk da haka, ko da yake Jehovah yana fushi da mutanensa bai yasar da su ba gabaki ɗaya. Maimakon haka ya ta da Ishaya da wasu annabawa domin su ba da haske na ruhaniya ga dukan wanda zai nemi ya bauta wa Jehovah da aminci a cikin al’ummar. Haske da aka yi tanadinsa ta wajen waɗannan annabawa yana da muhimmanci ƙwarai. Yana ba da rai.
Lokatai na Masu Duhu a Yau
8, 9. Waɗanne abubuwa ne suka ƙara ga duhun duniya a yau?
8 Yanayi na lokacin Ishaya, ya yi daidai da yanayin yau. A zamaninmu, shugabanni sun juya baya wa Jehovah da kuma Yesu Kristi da ya naɗa sarki. (Zabura 2:2, 3) Shugabannin addini na Kiristendam sun yaudari tumakinsu. Waɗannan shugabannin suna da’awar suna bauta wa Allah, amma da gaske yawancinsu suna ɗaukaka allolin wannan duniya—wariya, dakarun soja, dukiya, da kuma wasu mutane da suka yi suna—ban da koyarwar arna da suke yi.
9 Daga wuri zuwa wuri, addinan Kiristendam suna saka hannu a yaƙe-yaƙe da tarzoma na ƙare dangi da kuma wasu munanan abubuwa. Bugu da ƙari, maimakon su dage a kan ɗabi’a ta Littafi Mai Tsarki, coci da yawa ko suna ƙyale ko kuma suna tallafa wa ayyukan fajirci kamar su fasikanci da kuma luwaɗi. Domin wannan yasar da mizanan Littafi Mai Tsarki, tumakin Kiristendam suna kama da waɗannan mutane da mai Zabura na dā ya yi maganarsu: “Waɗanne irin jahilai ne ku, wawaye! Kuna zaune cikin duhu.” (Zabura 82:5) Hakika, Kiristendam kamar Yahuza ta dā yake, yana cikin baƙin duhu.—Wahayin Yahaya 8:12.
10. Yaya haske yake haskaka a cikin duhu a yau, kuma ta yaya masu tawali’u suke amfana?
10 A cikin wannan duhu, Jehovah yana sa haske ya haskaka domin masu tawali’u. Domin haka yake amfani da bayinsa shafaffu na duniya, “amintaccen bawan nan mai hikima,” kuma waɗannan suna “haskakawa a cikinsu kamar fitilu a duniya.” (Matiyu 24:45; Filibiyawa 2:15) Ajin bawa, da kuma miliyoyin “waɗansu tumaki” abokanan tarayyarsu da su suke tallafa musu, suna haskaka haske na ruhaniya bisa Kalmar Allah, Littafi Mai Tsarki. (Yahaya 10:16) A cikin wannan duniya da take cikin duhu, wannan hasken yana ba masu tawali’u bege, yana taimakonsu su sami dangantaka mai kyau da Allah, yana taimaka musu su guje wa faɗawa ta ruhaniya. Yana da tamani, yana ba da rai.
“Zan Ɗaukaka Sunanka”
11. Menene Jehovah ya sanar a zamanin Ishaya?
11 A zamani mai duhu da Ishaya ya rayu da kuma zamani mafi duhu da ya zo daga baya lokacin da Babiloniya suka kwashi al’ummar Jehovah zuwa hijira, wane irin ja-gora Jehovah ya bayar? Ban da ba su ja-gora na ɗabi’a, ya zana abin da zai faru a gaba sarai, yadda zai cika nufe-nufensa game da mutanensa. Ka yi la’akari da, alal misali, annabce-annabce na ban mamaki da suke cikin surori 25 da kuma 27 na Ishaya. Kalmomi cikin waɗannan surori sun nuna yadda Jehovah ya bi da al’amura a dā can da kuma yadda yake bi da su a yau.
12. Wane furci ne Ishaya ya furta daga zuciyarsa?
12 Da farko, Ishaya ya furta: “Ya Ubangiji, kai ne Allahna, Zan ɗaukaka ka, in yabi sunanka.” Wannan yabo ne da ya fito daga zuci! Me ya motsa annabin ya furta irin wannan addu’ar? Babban dalili ya bayyana a cikin saurar ayar, in da muka karanta: “[Jehovah] ka aikata al’amura masu banmamaki, Ka tafiyar da su da aminci, Wato bisa ga shirin da ka yi tuntuni.”—Ishaya 25:1.
13. (a) Wane sani ne ya ƙarfafa godiyar Ishaya ga Jehovah? (b) Ta yaya za mu koya daga misalin Ishaya?
13 A zamanin Ishaya, Jehovah ya yi ayyuka da yawa na ban mamaki ga Isra’ila, kuma an rubuta waɗannan abubuwa. Kuma da alamu cewa Ishaya ya san da waɗannan rubuce-rubucen. Alal misali, ya san cewa Jehovah ya fito da mutanensa daga bauta a Masar kuma ya cece su daga fushin dakarun Fir’auna a Jar Teku. Ya san cewa Jehovah ya ja-goranci mutanensa a hamada zuwa Ƙasar Alkawari. (Zabura 136:1, 10-26) Irin waɗannan labaran tarihi sun nuna cewa Jehovah Allah ne mai aminci kuma abin dogara. ‘Shawararsa’—dukan abin da ya nufa—sun tabbata. Cikakken sani da Allah ya yi tanadinsa ya ƙarfafa Ishaya ya ci gaba da tafiya cikin haske. Saboda haka, misali ne mai kyau domin mu. Idan muka yi nazarin rubucacciyar Kalmar Allah sosai kuma muka yi amfani da ita a rayuwarmu, mu ma za mu kasance cikin haske.—Zabura 119:105; 2 Korantiyawa 4:6.
An Halaka Birni
14. Menene aka annabta game da birni, kuma wataƙila, wane birni ne wannan?
14 Misalin gargaɗi na Allah an samu a cikin Ishaya 25:2, inda muka karanta: “Ka mai da birane kufai ka lalatar da kagaransu, Wuraren da maƙiya suka gina kuwa, An shafe su har abada.” Menene wannan birnin? Wataƙila Ishaya ya yi magana ne cikin annabci game da Babila. Hakika, lokaci ya zo da Babila ta zama tarin duwatsu.
15. Wane “babban birni” ne yake wanzuwa a yau, kuma menene zai faru da shi?
15 Birni da Ishaya ya yi maganarsa yana da na biyunsa ne a yau? I. Littafin Wahayin Yahaya ya yi magana game da “babban birnin da ke mulkin sarakunan duniya.” (Wahayin Yahaya 17:18) Babban birnin “Babila mai girma” ce, daular addinin ƙarya ta duniya. (Wahayin Yahaya 17:5) A yau, Kiristendam shi ne ɓangare mafi muhimmanci na Babila Babba, wanda limamansa suke ja-gora wajen hamayya da aikin wa’azin Mulki na mutanen Jehovah. (Matiyu 24:14) Kamar Babila ta dā, Babila Mai Girma ba da daɗewa ba za a halaka ta, ba za ta kuwa sake tashi ba.
16, 17. Ta yaya abokan gaban Jehovah suka ɗaukaka shi a zamanin dā da kuma na yau?
16 Menene kuma Ishaya ya annabta game da “birane musu ganuwa”? Da yake magana da Jehovah, Ishaya ya ce: “Jama’ar al’ummai masu iko za su yabe ka, Za a ji tsoronka a biranen mugayen al’ummai.” (Ishaya 25:3) Ta yaya wannan birnin da abokin gaba ne, “biranen mugayen al’ummai,” za su ɗaukaka Jehovah? To, ka tuna da abin da ya sami sarkin Babila mafi girma, Nebuchadnezzar. Bayan ya fuskanci yanayi na ladabtarwa da ya nuna ajizancinsa, aka tilasta masa ya furta ɗaukakar Jehovah da kuma girman ikonsa. (Daniyel 4:34, 35) Idan Jehovah ya yi amfani da ikonsa, har abokan gabansa suna yaba masa, ko da ba da son rai ba, ayyukansa na ban mamaki.
17 An taɓa tilasta wa Babila Mai Girma ta fahimci ayyuka masu ban mamaki na Jehovah ne? I. A lokacin yaƙin duniya na farko, bayin Jehovah shafaffu sun yi wa’azi cikin tsanani. A shekara ta 1918 an kwashe su hijira a ruhaniya lokacin da aka ɗaure majagaban ma’aikata na Watch Tower Society a fursuna. Wa’azi da aka tsara ta kusan dainawa. Sai a 1919, lokacin Jehovah ya mai da su ya sake ƙarfafa su da ruhunsa, daga nan suka sha ɗamarar cika umurnin su yi wa’azin bisharar a dukan mazaunan duniya. (Markus 13:10) An annabta duka wannan a littafin Wahayin Yahaya, har da yadda wannan zai shafi abokan adawarsu. Waɗannan “suka tsorata, suka ɗaukaka Allah Mai Sama.” (Wahayin Yahaya 11:3, 7, 11-13) Ba dukansu ba ne suka tuba, amma an tilasta musu su fahimci ayyuka mai ban mamaki na Jehovah a wannan lokacin, kamar yadda Ishaya ya riga ya annabta.
‘Kagara ga Matalauta’
18, 19. (a) Me ya sa ’yan adawa sun kasa karya amincin mutanen Jehovah? (b) Ta yaya ‘hayaniyar mugaye za ta yi tsit’?
18 Da ya mai da hankalinsa ga hanya ta kirki da Jehovah ya bi da waɗanda suke tafiya cikin haske, Ishaya ya ce game da Jehovah: “Matalauta da ’yan ƙaƙa naka yi sun sheƙa zuwa wurinka, Sun sami zaman lafiya a lokatan wahala. Ka ba su mafaka daga hadura, Ka ainuwantar da su daga matsanancin zafi. Mugaye sukan tasar musu kamar hadirin ƙanƙara, Kamar fari a ƙeƙasasshiyar ƙasa. Amma kai, ya Ubangiji, ka rufe bakin abokan gābanmu, Ka sa hayaniyar mugaye ta yi tsit, Kamar yadda girgije ke sanyaya zafin rana.”—Ishaya 25:4, 5.
19 Tun daga shekara ta 1919, mugaye sun yi ƙoƙari su karya amincin masu bautar gaskiya, amma sun kasa. Me ya sa? Domin Jehovah shi ne kagara da kuma mafakar mutanensa. Ya yi tanadin inuwa mai sanyi daga matsanancin zafi na tsanantawa kuma yana tsaye kamar garu ga hadarin ƙanƙara na hamayya. Mu da muke tafiya cikin hasken Allah da gaba gaɗi muna sauraron lokacin da ‘hayaniyar mugaye za ta yi tsit.’ Hakika, muna ɗokin jiran ranar da abokan gaban Jehovah za su kare.
20, 21. Wane biki ne Jehovah ya yi tanadi, kuma menene wannan bikin zai ƙunsa a sabuwar duniya?
20 Jehovah yana yi fiye da kāre bayinsa. Uba ne mai ƙauna da yake yi masu tanadi. Bayan ya ceci mutanensa daga Babila Mai Girma a shekarar 1919, ya yi musu bikin nasara, ya ba su abinci isashe na ruhaniya. An faɗi wannan a Ishaya 25:6, inda muka karanta: “A kan Dutsen Sihiyona Ubangiji Mai Runduna zai shirya wa dukan sauran al’umman duniya biki da abinci irin na adaras da ruwan inabi mafi kyau.” Lalle masu albarka ne mu da muka sami rabonmu cikin wannan dina! (Matiyu 4:4) ‘Teburin Jehovah’ da gaske yana ɗauke da abubuwa masu kyau na ci. (1 Korantiyawa 10:21) Ta hannun “amintaccen bawan nan mai hikima,” ana ba mu dukan abubuwa da muke bukata a ruhaniya.
21 Da akwai ƙari ga wannan biki da Allah ya yi. Biki na ruhaniya da muke morewa a yau yana tunasar da mu abinci na zahiri mai yawa da za a samu a sabuwar duniya da Allah ya yi alkawarinta. A lokacin, “abinci irin na adaras” zai haɗa da abinci na zahiri a yalwace. Babu wanda zai ce yana yunwa a zahiri ko kuma a ruhaniya. Wannan zai sauƙaƙa wahala da ’yan’uwanmu masu bi ƙaunatattu suke sha saboda ‘karancin abinci’ da aka annabta, waɗanda ‘alamu’ ne na bayyanuwar Yesu! (Matiyu 24:3, 7) A gare su kalmomin mai Zabura suna da ban ƙarfafawa da gaske. Ya ce: “Da ma a sami hatsi mai yawa a ƙasar, da ma amfanin gona ya cika tuddan.”—Zabura 72:16.
22, 23. (a) Wane ‘saƙa’ ne ko kuma ‘lulluɓi,’ za a cire, kuma ta yaya? (b) Ta yaya za a kawar da ‘zargi na mutanen Allah?’
22 Ka saurara yanzu ga alkawari mafi ban al’ajabi. A kwatanta zunubi da mutuwa da ‘saƙa,’ ko kuma ‘luluɓi,’ Ishaya ya ce: “A can ne zai kawar da baƙin cikin da ya lulluɓe dukan sauran al’umma.” (Ishaya 25:7) Ka yi tunani! Zunubi da mutuwa, da suka yi nauyi a kan mutane kamar bargon mutuwa, ba za su kasance ba kuma. Muna sauraron ranar da za a aikata amfanin hadayar fansa ta Yesu a kan mutane masu aminci kuma masu biyayya!—Wahayin Yahaya 21:3, 4.
23 Da yake magana game da wannan lokacin ɗaukaka, annabi da aka hure ya tabbatar mana: “[Allah] zai hallaka mutuwa har abada! Zai share hawaye daga idanun kowane mutum, ya kawar da kunyar da jama’arsa suke sha a duniya duka. Ubangiji ne da kansa ya faɗa!” (Ishaya 25:8) Babu wanda zai mutu daga wani sanadi ko kuma a yi kuka domin an yi rashin wanda ake ƙauna. Canji mai albarka kuwa! Bugu da ƙari, babu wani wuri a duniya da za a ji zargin ƙarya da ake yaɗa wanda Allah da bayinsa suka jure na dogon lokaci. Me ya sa? Domin Jehovah zai kawar da tushensu—uban ƙarya, Shaiɗan Iblis, tare da zuriyarsa.—Yahaya 8:44.
24. Ta yaya waɗanda suka yi tafiya cikin hasken za su amsa game da ayyukan ban mamaki dominsu?
24 Bayan sun yi tunani a kan irin wannan nuna iko na Jehovah, waɗanda suke tafiya cikin haske za su motsu su ce: “Shi Allahnmu ne! Mun dogara gare shi, ya kuwa cece mu. Shi ne Ubangiji. Mun dogara gare shi, yanzu kuwa muna da farin ciki domin ya cece mu!” (Ishaya 25:9) Ba da daɗewa ba, mutane masu adalci za su samu dalilin yin murna. Duhu zai ƙare kwata kwata, kuma amintattu za su wanku cikin hasken Jehovah har abada abadin. Da wani bege da zai fi wannan ɗaukaka? Babu!
Za Ka Iya Bayyanawa?
• Me ya sa yake da muhimmanci mu yi tafiya cikin haske a yau?
• Me ya sa Ishaya ya ɗaukaka sunan Jehovah?
• Me ya sa abokan gaba suka kasa karya amincin mutanen Allah?
• Wace babbar albarka ce take jiran waɗanda suke tafiya cikin haske?
[Hoto a shafi nas 22, 23]
Mazaunan Yahuza suna yin hadayar yara ga Molek
[Hotuna a shafi na 25]
Sanin ayyukan ban mamaki na Jehovah ya motsa Ishaya ya ɗaukaka sunan Jehovah
[Hoto a shafi na 26]
Amintattu za su wanku cikin hasken Jehovah har abada abadin