Maganar Jehobah Rayayya Ce
Darussa Daga Littafin Ishaya na Ɗaya
“WA ZAN aika, kuma wanene za ya tafi domin mu?” Ishaya ɗan Amos ya amsa wannan gayya na Jehobah Allah yana cewa: “Ga ni; ka aike ni.” (Ishaya 1:1; 6:8) Sai aka ba shi aikin zama annabi. An rubuta ayyukan annabci na Ishaya a cikin littafi mai ɗauke da sunansa a cikin Littafi Mai Tsarki.
Annabin ne da kansa ya rubuta littafin, kuma littafin Ishaya ya ba da labarin aukuwa na shekara 46, wato, daga shekara ta 778 K.Z., zuwa shekara ta 732 K.Z. Ko da littafin na ɗauke da shelar hukunci a kan Yahuda, Isra’ila, da al’ummai da suka kewaye su, jigonsa na ainihi ba hukunci ba ne. Maimakon haka, ‘ceto na Jehobah Allah ne.’ (Ishaya 25:9) Sunan Ishaya na nufin “Ceto na Jehobah.” Wannan talifin zai tattauna darussa daga Ishaya 1:1 zuwa 35:10.
“WANI RINGI ZA SU KOMO”
(Ishaya 1:1–12:6)
Littafi Mai Tsarki bai faɗa ba ko an idar da saƙon annabci da ke rubuce a surori biyar na farko na littafin Ishaya kafin a naɗa Ishaya annabi ko kuma bayan haka. (Ishaya 6:6-9) Amma a bayyane yake cewa Yahuda da Urushalima suna ciwo ta ruhaniya daga “tāfin sawu har zuwa kai.” (Ishaya 1:6) Ana bautar gunki a ko’ina. Shugabannan suna cin hanci. Matan suna da girman kai. Mutane ba sa bauta wa Allah na gaskiya yadda yake so. An ba Ishaya aikin yin magana ‘a kai a kai’ ga waɗanda ba su da fahimi da kuma ilimi.
Rundunar Isra’ila da Suriya da suka haɗa kai sun kai wa Yahuda hari. Ta wajen yin amfani da Ishaya da yaransa su zama ‘alamu da al’ajabai,’ Jehobah ya ba Yahuda tabbaci cewa haɗa kai na Isra’ila da Suriya ba zai yi nasara ba. (Ishaya 8:18) Za a sami salama ta dindindin ta wurin sarauta na “Sarkin Salama.” (Ishaya 9:6, 7) Jehobah zai kuma yi wa Assuriya shari’a, al’umma da ya yi amfani da ita ta zama “sandar fushin[sa].” Yahuda za ta tafi bauta amma “wani ringi za su komo.” (Ishaya 10:5, 21, 22) Za a yi shari’a ta gaske a ƙarƙashin sarauta na “tsutsugen Jesse” na alama.—Ishaya 11:1.
Tambayoyin Nassi da Aka Amsa:
1:8, 9—Ta yaya za a bar ɗiyar Sihiyona kamar “bukka cikin gonar anab, kamar makanni cikin gonar kabewa”? Wannan yana nufin cewa a lokacin harin Assuriya, Urushalima za ta zama kamar ba mai kāre ta, kamar bukka cikin gonar anab ko kuma rumfa mai sauƙin rushewa a gonar kabewa. Amma Jehobah ya kāre ta kuma bai ƙyale ta ta zama kamar Saduma da Gwamrata ba.
1:18—Menene furcin nan: ‘Ku zo yanzu, mu yi bincike tare’ yake nufi? Wannan ba gayyata ba ne a zo a tattauna abubuwa kuma a kasance da ra’ayi ɗaya. Maimakon haka, ayar na nuna yanayi da aka tsara don yin shari’a inda Jehobah, Alƙali mai adalci ya ba Isra’ila zarafi ta canja kuma ta tsarkake kanta.
6:8a—Me ya sa aka yi amfani da wakilin suna “zan” da “mu” a nan? Wakilin suna “zan” na nuni ga Jehobah Allah. Jam’in wakilin suna “mu” na nuna cewa wani yana tare da Jehobah. Hakika, wannan Ɗansa ne “haifaffe kaɗai.”—Yohanna 1:14; 3:16.
6:11—Menene Ishaya yake nufi sa’ad da ya yi tambaya: “Har yaushe, ya Ubangiji?” Ishaya ba ya tambayar har yaushe zai ci gaba da idar da saƙon Jehobah ga mutane da ba sa saurarawa. Maimakon haka, yana son ya san har yaushe ciwo na ruhaniya na mutanen zai ci gaba da ɓata sunan Allah.
7:3, 4—Me ya sa Jehobah ya ceci mugun Sarki Ahaz? Sarakunan Suriya da Isra’ila sun yi shiri su kawar da Sarki Ahaz na Yahuda daga kursiyi kuma su naɗa wani ya ɗauki matsayinsa, ɗan Tabeel, mutumin da bai fito daga zuriyar Dauda ba. Wannan ƙullin zai shafi alkawari na Mulki da aka yi da Dauda. Jehobah ya ceci Ahaz domin zuriyar da aka yi alkawari cewa ta wurinsa ne “Sarkin Salama” zai zo ya ci gaba.—Ishaya 9:6.
7:8—Ta yaya aka “kakkarye” Ifraimu kafin shekara sittin da biyar? Korar mutane na mulkin ƙabilu goma daga ƙasar da kuma saka baƙi a ƙasar ya soma “a cikin kwanakin Pekah sarkin Isra’ila,” ba da daɗewa ba bayan Ishaya ya furta wannan annabcin. (2 Sarakuna 15:29) Ya ci gaba har zuwa kwanakin Sarkin Assuriya, Esar-haddon, ɗan Sennacherib da kuma magajinsa. (2 Sarakuna 17:6; Ezra 4:1, 2; Ishaya 37:37, 38) Da yake mutanen Assuriya sun ci gaba da kai mutane zuwa Samariya da kuma kawar da mutane daga wurin ya sa aka samu shekara sittin da biyar da aka ambata cikin Ishaya 7:8.
11:1, 10—Ta yaya Yesu Kristi ya fito daga “tsutsugen Jesse” da kuma “tushen Jesse”? (Romawa 15:12) Yesu ya fito daga “tsutsugen Jesse” ta zahiri. Shi zuriyar Jesse ne ta wurin Dauda ɗan Jesse. (Matta 1:1-6; Luka 3:23-32) Amma, karɓan ikon mulki ya shafi dangantakar Yesu da kakanninsa. Da yake an ba shi iko ya ba ’yan adam masu biyayya rai na har abada a duniya, Yesu ya zama “Uba madawwami.” (Ishaya 9:6) Saboda haka, shi ne “tushen” kakanninsa, har da Jesse.
Darussa Dominmu:
1:3. Ƙin bin abin da Mahaliccinmu ke bukata a gare mu yana nufin cewa sa da jaki sun fi mu hankali. A wata sassa kuma, nuna godiya don dukan abin da Jehobah ya yi mana zai hana mu aikatawa da rashin fahimi kuma ba za mu bar shi ba.
1:11-13. Bukukuwan riya na addinai da addu’o’i da ake yi kawai suna gajiyar da Jehobah. Ayyukanmu da addu’o’i ya kamata su fito daga zuciyar kirki.
1:25-27; 2:2; 4:2, 3. Zaman bauta da kango na Yahuda zai ƙare da dawowar raguwa da suka tuba zuwa Urushalima da kuma maido da bauta ta gaskiya. Jehobah mai jinƙai ne ga masu laifi da suka tuba.
2:2-4. Yin aikin wa’azin Mulki da almajirantarwa da himma na taimaka wa mutane daga al’ummai da yawa su koyi hanyoyin kasancewa da salama da juna.
4:4. Jehobah zai cire, ko kuma ya wanke, ƙazanta na ɗabi’a da alhakin jini.
5:11-13. Mutum ba ya aikatawa bisa sani idan ya ƙi kama kansa kuma ya kasance da kima a zaɓen nishaɗi.—Romawa 13:13.
5:21-23. Dole ne dattawa, ko masu kula su kauce wa “maida kansu masu-hikima.” Suna kuma bukatar su kasance da kima wajen shan “ruwan anab” kuma su guje wa nuna son kai.
11:3a. Misalin Yesu da koyarwarsa sun nuna cewa ana samun farin ciki ta wajen jin tsoron Jehobah.
“UBANGIJI ZA YA YI JUYAYIN YAKUB”
(Ishaya 13:1–35:10)
Surori 13 zuwa 23 sun yi shelar hukunci a kan al’ummai. Amma, “Ubangiji za ya yi juyayin Yakub” ta wajen barin dukan al’ummai na Isra’ila su koma gida. (Ishaya 14:1) Saƙon kango na Yahuda cikin surori 24 zuwa 27 ya haɗa da alkawarin maidowa. Jehobah ya nuna fushinsa ga “mashayan Ifraimu [Isra’ila]” don sun yi kawance da Suriya kuma ya yi fushi da ‘firist da annabi’ na Yahuda don neman yin kawance da Assuriya. (Ishaya 28:1, 7) An yi shelar kaito bisa “Ariel [Urushalima]” don suna “tafiya su gangara zuwa Masar” don kāriya. (Ishaya 29:1; 30:1, 2) Duk da haka, an annabta cewa za a ceci waɗanda suka ba da gaskiya ga Jehobah.
Kamar ‘yadda zaki ya kan yi ruri bisa kan ganimarsa’ Jehobah zai tsare “dutsen Sihiyona.” (Ishaya 31:4) An kuma yi alkawari: “DUBA, wata rana wani sarki za ya yi mulki cikin adalci.” (Ishaya 32:1) Ko da barazanan da Assuriya ta yi wa Yahuda yana sa “manzanni masu-neman amana” su yi kuka mai zafi, Jehobah ya yi alkawari cewa zai warkar da mutanensa kuma ya “gafarta musu zunubinsu.” (Ishaya 33:7, 22-24) “Ubangiji yana fushi da dukan al’ummai, yana hasala da dukan rundunassu.” (Ishaya 34:2) Yahuda ba za ta ci gaba da zama kango ba. “Jeji da ƙeƙasashiyar ƙasa za su yi farinciki; hamada kuma za ta yi murna, ta yi fure kamar [furanin] rose.”—Ishaya 35:1.
Tambayoyin Nassi da Aka Amsa:
13:17—Ta yaya ne ’yan Midiya ba za su kula da azurfa ba kuma ba sa damuwa da zinariya? ’Yan Midiya da ’yan Fasiya sun fi son darajar da ake samu daga cin yaƙi fiye da ganimar yaƙi. An ga gaskiyar wannan sa’ad da Cyrus ya ba ’yan bauta da suke komawa ƙasarsu zinariya da azurfa da Nebuchadnezzar ya kwashe daga haikalin Jehobah.
14:1, 2—Ta yaya mutanen Jehobah suka “bautadda waɗanda su ke bauta masu” kuma suka ‘mallaki waɗanda suka wulakanta su’? Wannan ya cika a kan mutane kamar Daniel, wanda yake da babban matsayi a Babila a ƙarƙashin ’yan Midiya da ’yan Fasiya; da Esther wadda ta zama sarauniya a Fasiya; da kuma Mordecai wanda aka naɗa firayim minista na Daular Fasiya.
20:2-5—Da gaske ne Ishaya ya yi tafiya tsirara shekara uku? Mai yiwuwa Ishaya ya tuɓe tufafinsa na waje yana tafiya da ’yar ciki.—1 Samuila 19:24.
21:1—Ina ne ake kira “jejin da ke wajen teku”? Ko da Babila ba ta yi kusa da kowane teku ba, an ce da ita hakan. Domin ruwan Yufiretis da Tigris suna cika wurin kowace shekara har ya zama “teku.”
24:13-16—Ta yaya Yahudawa za su zama “tsakiyar ƙasa a wurin al’ummai, kamar karkaɗan itacen zaitun, kamar kālan ’ya’yan anab bayanda an gama girbi”? Kamar yadda ake barin wasu ’ya’yan itace a kan itace ko kuma anab bayan girbi, mutane kaɗan ne kawai za su tsira wa halakar Urushalima da Yahuda. Duk inda aka kai waɗanda suka tsira, ko zuwa “[Babila] a gabas” ko kuma zuwa “cikin dukan gaɓan teku [Bahar Rum]” za su ɗaukaka Jehobah.
24:21—Su waye ne “rundunan maɗaukaka” da “sarakunan duniya”? “Rundunan maɗaukaka” na iya zama miyagun ruhohi. “Sarakunan duniya” masarautan duniya ne, da aljanu suke iko a kansu.—1 Yohanna 5:19.
25:7—Menene “fuskar labule, wanda ya rufe dukan dangogi, da luluɓi wanda an shimfiɗa a kan dukan al’ummai”? Wannan kwatanci ya jawo hankali ga manyan magabta biyu na ’yan adam, wato, zunubi da mutuwa.
Darussa Dominmu:
13:20-22; 14:22, 23; 21:1-9. Kalmomin annabci na Jehobah koyaushe na kasancewa gaskiya yadda yake a batun Babila.
17:7, 8. Ko da yawancin mutane a Isra’ila ba su saurara ba, wasu sun nemi Jehobah. Haka nan ma, wasu a Kiristendam sun saurari saƙon Mulki.
28:1-6. Isra’ila za ta faɗa wa Assuriya, amma Allah zai sa mutane masu aminci su tsira. Hukuncin Jehobah yana sa masu adalci su kasance da bege.
28:23-29. Jehobah yana yi wa mutane gyara bisa ga bukatunsu da yanayinsu na musamman.
30:15. Don Jehobah ya cece mu muna bukatar mu kasance da bangaskiya ta wurin “hutu,” ko kuma ƙin neman ceto ta wurin tsare-tsaren ’yan adam. Ta wurin “natsuwa” ko kuma kasancewa da gaba gaɗi, muna nuna mun dogara ga ikon Jehobah na kāre mu.
30:20, 21. Muna ‘ganin’ Jehobah da kuma ‘jin’ muryarsa na ceto ta wurin yin biyayya da abin da ya ce ta wurin Kalmarsa Littafi Mai Tsarki da aka hure, da kuma ta wurin “bawan nan mai-aminci, mai-hikima.”—Matta 24:45.
Annabcin Ishaya na Ƙarfafa Tabbacinmu ga Kalmar Allah
Muna godiya don saƙon Allah da ke cikin littafin Ishaya! Annabce-annabce da sun riga sun cika sun ƙarfafa tabbacinmu cewa ‘magana da ke fitowa daga bakin Jehobah ba za ta koma wurinsa wofi ba.’—Ishaya 55:11.
Annabce-annabcen Almasihu, kamar waɗanda suke cikin Ishaya 9:7 da 11:1-5, 10 kuma fa? Ba su ƙarfafa bangaskiyarmu ba ne ga tanadin Jehobah don cetonmu? Littafin na ɗauke da annabce-annabce da suke cikawa a zamaninmu ko kuma da za su cika nan gaba. (Ishaya 2:2-4; 11:6-9; 25:6-8; 32:1, 2) Hakika, littafin Ishaya ya daɗa ga tabbatar da cewa “maganar Allah mai-rai ce”!—Ibraniyawa 4:12.