Ka Kusaci Allah
Alƙali da Yake Yin Adalci Koyaushe
Farawa 18:22-32
ADALCI. Rashin son kai. Kana sha’awar irin wannan halin kuwa? Mutane suna son a yi musu adalci. Abin baƙin ciki kuwa shi ne, akwai rashin adalci sosai a duniya yau. Amma akwai alƙali da ya cancanta mu dogara da shi, wato, Jehobah Allah. Koyaushe yana kasancewa da adalci. An nuna hakan a wani tattaunawa da Jehobah ya yi da Ibrahim, da aka rubuta a Farawa 18:22-32.a
Sa’ad da Jehobah ya gaya wa Ibrahim abin da zai yi wa Saduma da Gwamarata, Ibrahim ya damu saboda mutane masu adalci da suke zama a wajen har da ɗan’uwansa Lutu. Ibrahim ya tambayi Jehobah: “Za ka hallaka mai-adilci tare da miyagu? Watakila ko da akwai masu-adilci guda hamsin a cikin birni: za ka . . . keɓewa sabili da masu-adilci hamsin da ke ciki?” (Ayoyi 23, 24) Allah ya ce ba zai halaka birnin ba idan akwai mutane 50 masu adalci a ciki. Ibrahim ya roƙi Jehobah har sau biyar, yana rage adadin mutanen har ya kai mutane goma. A kowane lokaci Allah yana cewa ba zai halaka birnin ba idan akwai mutane masu adalci a wajen.
Ibrahim yana gardama da Allah ne? A’a! Hakan zai nuna girman kai. Yadda Ibrahim ya yi magana ya nuna cewa shi mutum ne mai tawa’ilu. Ya kira kansa “turɓaya da toka.” Bugu da ƙari, kalaman Ibrahim sun nuna cewa ya tabbata Jehobah zai yi adalci. Sau biyu Ibrahim yana cewa, ra’ayin halaka mutane masu adalci tare da miyagu “ya yi nisa da kai [Allah].” Uban iyali ya kasance da tabbaci cewa “Mai-shari’an dukan duniya . . . za ya yi daidai.”—Aya 25.
Abin da Ibrahim ya ce gaskiya ne? Gaskiya ne kuma ba gaskiya ba ne. Ya yi kuskure da yake tunanin cewa akwai aƙalla mutane goma masu adalci a Saduma da Gwamarata. Amma ya yi gaskiya da ya ce Allah ba zai “hallaka mai-adilci tare da miyagu” ba. Daga baya sa’ad da Allah ya halaka waɗannan mugun birnin, Lutu mutum mai adalci tare da ’ya’yansa mata biyu sun tsira da taimakon mala’ika.—2 Bitrus 2:7-9.
Menene wannan labarin ya koya mana game da Jehobah? Ta wurin gaya wa Ibrahim abin da yake so ya yi a birnin, Jehobah yana son ya ji ra’ayin Ibrahim ne. Sai ya saurara sosai sa’ad da abokinsa Ibrahim yake furta damuwarsa. (Ishaya 41:8) Wannan ya koya mana cewa Jehobah Allah ne mai tawali’u, wanda yake daraja bayinsa na duniya! Hakika muna da dalilin mu dogara ga Jehobah, Alƙalin da yake yin adalci koyaushe.
[Hasiya]
a A wannan karon, mala’ika ne ya wakilta Jehobah ta wurin yin magana a madadinsa. Alal misali, dubi Farawa 16:7-11, 13.
[Hotunan da ke shafi na 20]
Ibrahim ya roƙi Jehobah game da Saduma da Gwamarata