Sashe 4
Allah Ya Ɗauki Alkawari da Ibrahim
Ibrahim ya yi biyayya ga Allah cike da bangaskiya, kuma Jehobah ya yi alkawari cewa zai albarkace shi kuma zai ƙara yawan zuriyoyinsa
SHEKARU wajen 350 sun riga sun wuce da aukuwar Rigyawa ta zamanin Nuhu. Ibrahim uban iyali yana zaune a birni mai arziki a Ur, wato, inda ƙasar Iraƙi ta zamani ta ke. Ibrahim mutumi ne mai bangaskiya sosai. Amma a yanzu ana son a jarraba bangaskiyarsa.
Jehobah ya gaya wa Ibrahim ya bar ƙasar da aka haife shi kuma ya koma wata ƙasa, wato, Ka’anan. Ibrahim ya yi biyayya ba tare da yin ja-in-ja ba. Ya tafi da iyalinsa, har da matarsa, Saratu, da ɗan’uwansa Lutu, kuma bayan wannan tafiyar mai nisa, ya zama mai zama a cikin tanti a Ka’anan. A cikin alkawarin da Ya yi da Ibrahim, Jehobah ya yi alkawarin cewa zai fito da wata al’umma mai girma daga cikinsa, za a yi wa dukan iyalan da ke duniya albarka ta hanyarsa, kuma ’ya’yansa za su gaji ƙasar Ka’anan.
Ibrahim da Lutu sun yi arziki, sun tara garken tumaki da shanu masu yawa. Ba tare da nuna son kai ba, Ibrahim ya ƙyale Lutu ya zaɓi yankin da yake so. Lutu ya zaɓi ƙasar da ke da ni’ima da ke yankin Kogin Urdun kuma ya zauna a birnin Saduma. Mutanen Saduma ’yan iska ne, suna mugun zunubi ga Jehobah.
Daga baya, Jehobah Allah ya tabbatar wa Ibrahim cewa zuriyarsa za ta yi yawa kamar taurarin sama. Ibrahim ya yi imani da wannan alkawarin. Duk da haka, Saratu, ƙaunatacciyar matar Ibrahim, ba ta haihu ba. Sa’ad da Ibrahim ya kai ɗan shekara casa’in da tara kuma Saratu ta kai wajen shekara casa’in, Allah ya gaya wa Ibrahim cewa shi da Saratu za su haifi ɗa. Kamar yadda Allah ya faɗa, Saratu ta haifi Ishaku. Ibrahim yana da yara, amma Mai Ceto da aka yi alkawarinsa a Adnin zai zo ne ta hanyar Ishaku.
Shi kuwa Lutu da iyalinsa suna zaune a Saduma, amma Lutu mai aminci bai bi halin lalatattu mazauna birnin ba. Sa’ad da Jehobah ya yanke shawarar hukunta Saduma, ya aika mala’iku don su je su gaya wa Lutu halakar da ke tafe. Mala’ikun sun umurci Lutu da iyalinsa su gudu daga Saduma kuma kada su kalli baya. Bayan haka, Allah ya yi ruwan wuta da ƙibiritu a kan Saduma da kuma mugun birnin da ke kusa da ita, Gwamrata, kuma ya halaka dukan mazauna cikinsu. Lutu da ’ya’yansa biyu mata sun tsira. Amma matar Lutu ta kalli baya, wataƙila don marmarin abubuwan da ta bari. Ta rasa ranta domin wannan rashin biyayyar.
—An ɗauko daga Farawa 11:10–19:38.
◼ Me ya sa Ibrahim ya koma Ka’anan?
◼ Wane alkawari ne Jehobah ya yi da Ibrahim?
◼ Me ya sa Jehobah ya halaka Saduma da Gwamrata?
[Akwati a shafi na 7]
ALLAHN ALKAWURA
A zamanin da aka rubuta Littafi Mai Tsarki, alkawari yarjejeniya ce. Ta hanyar jerin alkawuran da Ya yi, da sannu-sannu Jehobah ya bayyana yadda manufarsa game da Mai Ceto da aka yi alkawarinsa a Adnin zai cika. Alkawarin da ya yi da Ibrahim ya nuna cewa Wanda aka yi alkawarinsa zai fito ne daga zuriyar Ibrahim. Alkawuran da aka yi daga baya za su ba da ƙarin haske wajen gane Wanda aka yi alkawarinsa.
[Taswira a shafi na 7]
Farawa ●
Fitowa
Levitikus
Littafin Lissafi
Kubawar Shari’a
Joshua
Alƙalawa
Ruth
1 Sama’ila
2 Sama’ila
1 Sarakuna
2 Sarakuna
1 Labarbaru
2 Labarbaru
Ezra
Nehemiya
Esther
Ayuba
Zabura
Misalai
Mai-Wa’azi
Waƙar Waƙoƙi
Ishaya
Irmiya
Makoki
Ezekiel
Daniyel
Hosiya
Joel
Amos
Obadiya
Yunana
Mikah
Nahum
Habakkuk
Zafaniya
Haggai
Zakariya
Malakai
Matta
Markus
Luka
Yohanna
Ayyukan Manzanni
Romawa
1 Korintiyawa
2 Korintiyawa
Galatiyawa
Afisawa
Filibiyawa
Kolosiyawa
1 Tasalonikawa
2 Tasalonikawa
1 Timotawus
2 Timotawus
Titus
Filimon
Ibraniyawa
Yaƙub
1 Bitrus
2 Bitrus
1 Yohanna
2 Yohanna
3 Yohanna
Wasiƙa ta Yahuda
Ru’ya ta Yohanna