Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w15 9/1 pp. 3-4
  • Mene ne Ke Faruwa da Mu Bayan Mutuwa?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Mene ne Ke Faruwa da Mu Bayan Mutuwa?
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2015
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Mene ne yanayin matattu?
  • Za a Ta da Matattu!
    Me Za Mu Koya Daga Littafi Mai Tsarki?
  • Mutuwa Ba Ƙarshe Ba Ce!
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2014
  • Bege na Gaskiya ga Ƙaunatattunka da Suka Mutu
    Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?
  • Begen Tashin Matattu Tabbacacce Ne!
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2000
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2015
w15 9/1 pp. 3-4

ABIN DA KE SHAFIN FARKO | ZAI YIWU A SAKE RAYUWA—BAYAN MUTUWA?

Mene ne Ke Faruwa da Mu Bayan Mutuwa?

Yara da manya suna tsaye kusa da akwatin gawa a makabarta

“Na ɗauka cewa idan mutum ya mutu yana iya zuwa wurare uku, wato sama ko gidan wuta ko kuma purgatori. Na san cewa ban cancanci zuwa sama ba kuma ban yi abubuwan da suka isa in shiga gidan wuta ba. Ban san ainihi abin da purgatori yake nufi ba. Ban taɓa ganin kalmar a cikin Littafi Mai Tsarki ba, kage ne kawai.”—In ji Lionel.

“An koya mini cewa dukan waɗanda suka mutu suna zuwa sama amma ban gamsu da hakan ba. Na ga kamar mutuwa ce karshen kome, wato babu wani bege ga matattu.” —In ji Fernando.

Ka taɓa yin irin wannan tambayar: ‘Mene ne ke faruwa da mutane sa’ad da suka mutu? Matattu suna shan azaba a wani wuri ne? Za mu sake ganinsu kuwa? Ta yaya za mu tabbata da hakan?’ Don Allah ka yi la’akari da abin da Littafi Mai Tsarki ya faɗa game da wannan batun. Bari mu fara bincika yadda Littafi Mai Tsarki ya kwatanta mutuwa. Bayan haka, sai mu tattauna begen da Littafi Mai Tsarki ya yi magana a kai.

Mene ne yanayin matattu?

ABIN DA LITTAFI MAI TSARKI YA CE: “Masu-rai sun san za su mutu: amma matattu ba su san kome ba, ba su kuwa da sauran lada; gama ba a kara tuna da su ba. Dukan abin da hannunka ya iske na yi, ka yi shi da karfinka; gama babu wani aiki, ko dabara, ko ilimi, ko hikima, cikin kabari inda za ka.”a—Mai-Wa’azi 9:5, 10.

Kabari wuri ne da ake saka mutane sa’ad da suka mutu, ba wuri ne na zahiri ba domin mutanen da suke wurin ba su san kome ba kuma ba sa aiki. Wane ra’ayi ne Ayuba mai aminci yake da shi game da Kabari? Ya yi asarar dukiyarsa da ’ya’yansa a rana ɗaya kuma Shaiɗan ya addabe shi da gyambuna. Ya roki Allah: “Da fa za ka yarda ka ɓoye ni cikin Lahira [‘Kabari,’ New World Translation].” (Ayuba 1:13-19; 2:7; 14:13) Hakika, Ayuba bai ɗauka cewa Kabari gidan wuta ba ne inda wahalar da yake sha za ta daɗa karuwa ba. Maimakon haka, ya san cewa wurin hutu ne.

Akwai wata hanya kuma da za mu iya koya game da yanayin matattu. Littafi Mai Tsarki yana ɗauke da labaran mutane takwas da suka tashi daga mutuwa da za mu iya yin bincike a kansu.—Ka duba akwatin nan “Tashin Matattu Takwas da Aka Ambata a Littafi Mai Tsarki.”

Babu ko ɗaya cikin mutane takwas da aka ambata da ya je sama ko kuma gidan wuta. Da a ce waɗanda aka tashe su sun je irin waɗannan wuraren, kana ganin da ba su ba mutane labari ba? Kuma da ba a rubuta hakan a cikin Littafi Mai Tsarki don mutane su karanta ba? Ba a rubuta kome game da hakan a cikin Littafi Mai Tsarki ba. Babu shakka, waɗannan mutane takwas ba su ce kome ba game da wannan batun. Me ya sa? Domin a lokacin da suka mutu ba su san kome ba, kamar sun yi barci ne mai zurfi. Hakika a wasu lokuta, Littafi Mai Tsarki yakan kwatanta mutuwa da barci. Alal misali, amintattun mutane kamar Dauda da Istafanus sun “yi barci,” wato sun mutu.—Ayyukan Manzanni 7:60; 13:36.

To, wane bege ne matattu suke da shi? Za su iya farka daga wannan barci kuwa?

a An yi amfani da kalmar nan “Kabari” a wuraren da kalmomin Ibranancin nan “Sheol” da kuma na Helenanci “Hades” suka bayyana. Wasu juyin Littafi Mai Tsarki sun yi amfani da kalmar nan “jahannama” amma Littafi Mai Tsarki bai koyar da cewa ana kone mutane a wuta ba.

TASHIN MATATTU TAKWAS DA AKA AMBATA A LITTAFI MAI TSARKIb

Yaron wata gwauruwa Annabi Iliya ya ta da yaron wata gwauruwa da ke Zarefat a arewacin Isra’ila.—1 Sarakuna 17:17-24.

Ɗan wata Ba-shunammiya Elisha magajin annabi Iliya ya ta da wani yaro a garin Shunem kuma ya mika shi ga iyayensa.—2 Sarakuna 4:32-37.

Wani mutum a makabarta An binne gawan wani da bai daɗe da mutuwa ba a inda aka binne annabi Elisha. Mutumin ya tashi sa’ad da gawarsa ta taɓa kasusuwan annabi Elisha.—2 Sarakuna 13:20, 21.

Ɗan wata gwauruwa a kauyen Nayin Yesu ya dakatar da wata jana’izar da ake yi a garin Nayin kuma ya ta da wannan matashin, ya mai da shi ga mahaifiyarsa da ke makoki.—Luka 7:11-15.

’Yar Yariyus Wani ma’aikacin majami’a mai suna Yariyus ya kira Yesu don ya warkar da ’yarsa da ke rashin lafiya. Yesu ya ta da ita jim kaɗan bayan ta rasu.—Luka 8:41, 42, 49-56.

Li’azaru, abokin Yesu Yesu ya ta da Li’azaru bayan kwanaki huɗu da mutuwa kuma mutane da yawa sun shaida wannan aukuwar.—Yohanna 11:38-44.

Wata mai suna Dokas Manzo Bitrus ya ta da wannan matar wadda aka san ta da ayyukan nagarta.—Ayyukan Manzanni 9:36-42.

Aftikos Manzo Bulus ya ta da wani matashi mai suna Aftikos da ya faɗo daga tagar wata bene.—Ayyukan Manzanni 20:7-12.

b Tashin matattu mafi muhimmanci shi ne na Yesu Kristi kuma ya bambanta da waɗannan takwas da muka tattauna. Abin da za a tattauna a talifi na gaba ke nan.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba